31

1.3K 87 1
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

    
       31

  A mota ya jefata ya rufe murfin motar be jira cewarta ba yaja motar a guje.....Hagen fitarsu bilkisu tayi Tana murmushin mugunta....ta juya abinta,

  Saida suka hau Kan titi sanan ya waigo ya Dan kalleta har yanzun kuka takeyi kamar wadda akaiwa mutuwa gashi ta dunkule waje daya Tana rawar sanyi alamar zazzabi ne ke damunta....

   Kada kansa kawai yakeyi minti minti Yana juyowa ya kalleta tausayinta ke ratsa sassan jikinsa,

  Be tsaya ko inaba sai asibitin su Ahmad,parking space yayi parking motarsa sanan ya Ciro wayarsa ya Kiran ahmda minti kadan sukai magana ya kashe....

  Kallonta yakeyi yadda ta juyar da kanta gefe Tana hawaye yakai minti biyu a haka sai da ya gaji yace "muje ko?"

  "Bana bukatar taimakon kowa sai na Allah da ka maidani kawai ai Allah Yana sane Dani tunda mantawa Kayi Dani"

  Kamo hannunta yayi ta kwace "Fatima dama abinda ya janyo Miki zazzabi kenan?abinda yasamun ke rashin lafiya kenan?kika rame kikai baki tamkar wadda tayi ciwon shekara daya?....dafe kansa yayi take tausayinta ya Kara ratsa zuciyarsa cikin sanyin murya ya cigaba da magana "kiyi hakuri banyi hakan da ganganba sai Dan wani uzuri,Kuma Allah ya rubuto hakan zai faru insha allahu bazan sake barinki ba kinji?na tuba bintu"...ya karashe maganar cike da lallashi.

  Sai yanzun ta juyo da dubanta gareshi idanuwanta na fidda hawaye...."karka sake yimun haka idan ka barni bansan yadda zata kasance da rayuwata ba Kaine jigon rayuwata,idan ka nisanceni Yaya zanyi inyi rayuwa Babu Rabin rayuwata a tare Dani?"kafesa tayi da ido har yanzun hawaye ke zuba a idanuwanta

  Hannunsa yasa ya shiga share Mata hawaye cikin sigar lallashi yake fadin "ya Isa bintu Nima na shiga halin da kika shiga kanki kikasani juriyace kawai da jarumta irin ta da namiji Amma kiris ya rage in zubar da hawayena"...ya kashe Mata ido daya

   Cike da shagwaba ta langabar da kanta a jikin seat Tana jifansa da wani irin mayen kallo da idanuwanta ko kiftawa batayi yayinda yaji wani shaukin soyayyarta na dibarsa ji yakeyi tamkar ya rungumeta ya lallasheta,ji yakeyi tamkar ya dawo da kwanaki ukun da sukayi ba a tare ba....dakyar ya saita kansa ya matso daf da fuskarta Yana jiyo sautin futar numfashinta Mai zafin gaske "bintu Anya zan iya rayuwa da wata mace bayanki kuwa?"

  Kada Masa idanuwanta tayi hade da murmushin karfin Hali "Dole zaka koyawa kanka rayuwa da wata mace bayan ni dikda naso ace nice kadai zan mallakeka"

  Hancinta ya ja cike da zolaya "matsoraciya keda kikace bakiso Mai martaba yasan da ke?cewa kikayi Kar infada Masa saboda kina tsoron Kar deejah ta zauneki ni bansan yadda zaayi ki koyi zama jaruma ba"

  Turo baki gaba tayi Tana Masa hararar wasa"nidai muje kaga ka kawoni a dubani ka cikani da surutu"

  "Malama kin fa warke dama ciwon soyayya ne Ashe dai haka akesona"

   Hannu tasa ta rufe idanuwanta Tana dariya,lokaci daya sukaji Ana kwankwasa glass din motar.....

  Da sauri yarima ya zuge glass din ya motar gaba daya,Ahmad ne tsaye sanye da labcutt wuyansa rataye da abin daukar numfashi irin na likitoci,hararar yarima ya shigayi "malam ka kirani tun daxun zaku shigo Kun kwashe kusan Awa daya bangankuba nagaji na harhado Mata magungunan zazzabi na biyoku dashi Dan nasan soyayya kukeyi....

  Tabe baki yarima yayi hade da dage kafadarsa sama sanan ya Mika Masa hannu ya karbi ledar "zamuyi maneji Amma na rigada na Bata maganin ciwonta dama ciwon nawa ne ko bintu"

Anyi Walk'iya.......Onde histórias criam vida. Descubra agora