GIRMAN KAI

192 9 4
                                    

*GIRMAN KAI...*
        ('''RAWANIN TSIYA''')

*Na*

*Aisha Alto*

*Wattpad-@AishaAlto019.*

     '''Sadaukarwa Ga My Sweetheart, My Aminiyar Ƙwarai, My Ƙawar Arziki, Ta Gaban Goshin Aisha Alto, My Jinin Jiki, My Sisi Of Life JANAF🥰'''

    *Bismillahir rahmanir rahim*.

'''page'''...E


     Cak ya tsaya kafin a hankali ya juyo ya dawo da baya, kusa da kafafun Abba ya zauna yana faɗin “Gani Abba...”

  Kallonsa Abba yay kafin ya cira hannu ya dafa kansa yana yace “Kayi haƙuri da halayyar Ramlart da Uwarta Saif, wata rana sai labari kaji.” ya faɗa cikin tsantsar damuwa, kan Saif na ƙasa, a hankali ya ɗago bayan ya saki wani kayataccen murmushi mai ƙarawa fuskarsa kyau yace “Haba mana Abbana, yau nake a gidan nan? ai nasan halin kowa wallahi, kar hakan ya dameka, babu komai fatan mu dai Allah yasa su gane gaskiya su daina Abin da Su keyi.” Gyaɗa kai Abba yayi kafin “Haka ne Saif akoda yaushe natsuwarka da kaifin hankalinka na burgeni, karka damu indai ina numfashi babu wanda ya isa ya wulaƙantaka a gidan nan, ita kanta Baby da uwar tata zanyi maganinsu yau ɗin nan.” Jinjina kai Saif yayi sannan ya miƙe, “A'a Abba, don Allah ka ƙyalesu, ita Ramlat yarinta ce ke damunta, ita kuma Umme ban san dalilinta na min haka ba, amma koma mene ne Abba ka rabu dasu wata rana bama zasu ganni ba, balle har suyi min hakan.”

Bai jira cewar Abba ba ya juya zai fice yana faɗin “Abba zan fita, ina son zanje na duba Abdallah.” Gyara zama Abba yay, “Ok Son, amma fa karka manta yau ka dawo ko hutawa baka yi ba.” ɗan dariya yayi, “Ba daɗewa zanyi ba Abba, yanzu zan dawo insha Allahu, akwai maganar da zamuyi dashi ne.” 

“To shikenan sai ka dawo, Allah yayi maka albarka.” da Amin ya amsa sannan ya fice daga falon, yana wulla key din motar dake hannunsa yana caɓewa  ya fita harabar gidan ya shiga motarsa 4matic ya fice daga gidan da gudu sosai wanda kallo daya za kai masa ka fahimci ransa a matuƙar ɓace yake.

 

Baby tana shiga ɗakinta ta fada kan gado tana rafza uban kuka, a zahirin gaskiya ta tsani wannan Saif ɗin, saboda yadda yake shigan mata hanci da ƙudundune, komai na gidan ya gama mallakewa, ya mallake dukiyar Abban ta, ya mallake shi kanshi Abban, Ayyah kuwa kamar Ubanta haka ta ɗaukesa, dan jin maganarsa take sosai, ya zama tamkar wani annoba, duk hukuncin daya zartar ko Ayyah bata isa ta tsallakeshi ba balle Abba, ta rasa wannan iko da fin ƙarfin, bayan kuma Umme ta faɗa mata daga gidan marayu aka ɗaukosa amma kalli yadda yake iko da takama kamar dukiyar tundama chan ta ubansa ce.

Sai faman kuka take tana buga ƙafa akan gado kamar  ranta zai fita, shigowar Umme bai sa ta tsagaita ba, sai ma miƙewa da tayi akan gadon tana tsalle, tana faɗin “Wallahi sai na nuna masa bai isa ba, wannan karon zan nuna masa iyakarsa, dukiyar Ubana ce bata ubansa ba, saboda haka bai isa ya hanani yin yadda naga dama da dukiyar Abbana ba.” sai faɗe take tana tsalle-tsallen kukan tsabar sangarta kamar mahaukaciya.

Ƙura mata ido Umme tayi kafin ta fara ƙoƙarin hawa gadon tana faɗin “Stop Baby, stop please karki illata min kanki.” Ummee ta fad'a tana ƙoƙarin riƙota, saurin jada baya tayi tana faɗin “Don"t Touch me Umme, ai kina kallon duk abin da ya faru, wani yunƙurin kika yi na dakatar da wannan banzan ey?” ta fad'a cikin tsawa, idanunta duk sunyi jawur hawaye na zubar mata.

Sororo Umme tayi tana bin Baby da kallo da alamu ranta ya ɓaci da maganar da ta faɗa mata, cikin azama ta sauka daga kan gadon tana faɗin “Lalle Baby na yarda baki da hankali ko kaɗan.” ta faɗa tana jifan ta da wani irin kallo.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 09, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIRMAN KAIWhere stories live. Discover now