GIRMAN KAI

172 4 1
                                    

*GIRMAN KAI...*
        ('''RAWANIN TSIYA''')

*Na*

*Aisha Alto*

*Wattpad-@AishaAlto019.*

     '''Sadaukarwa Ga My Sweetheart, My Aminiyar Ƙwarai, My Ƙawar Arziki, Ta Gaban Goshin Aisha Alto, My Jinin Jiki, My Sisi Of Life JANAF🥰'''

*Wannan page ɗin sadaukarwa ne a gareku, Fiddausi Sodangi, Mai Dambu, Jamila K/Mashi, Khadeeja Candy, Feenarh (MATAR SOJA), Maryam Obam, Hauwa A Usman Jidda, Miss Xerks, Binta Umar Abbale, Shalele, Aunty Halilos, Phateema Mrs Sardauna, ina ƙaunarku domin Allah marubutan mu, inai muku son so FISABILILLAHI*.

    *Bismillahir rahmanir rahim*.

'''page'''...F

Washegari sai ƙarfe 10:am. Sannan Ya fito daga part ɗinsa cikin haɗaɗɗen shirinsa na ƙananan kaya, baƙin wandon jeans ne da farar T-shirt a jikinsa, shigar ta karɓi jikinsa sosai ta fito da tsantsar kyaunsa da kwarjininsa, sai faman zuba ƙamshi yake, ya nufi part ɗin Abba, ta cikin babban falon gidan yabi, a hankali yake takawa kansa a duƙe hannayensa duk zube a cikin aljihun wandonsa, zaune a kan dining table ya hango Ummee da Ramlat suna magana ƙasa-ƙasa.

Har ya wucesu zai nufi hanyar part ɗin Abba, sai kuma yaga rashin dacewar hakan, a hankali ya juyo ya nufo inda suke, tun daga ɗan nesa dasu yake ƙare mata kallo, yau ma dai cikin banzar shigarta ta kullum take, sai dai ta yau ta ɗan fi muni, dan wani ƙaramin tree quotern jan wandon roba-roba ne a jikinta, wanda ya matse ta sosai ya ɗame mata cinyoyi, ya tsaya mata dai-dai iya gwiwa, sai wata ƴar ƙaramar rigar half ves fara, wacce iyakar k'irjinta kawai ta rufe, tun daga kan ɗan shafaffen cikinta zuwa cibiyarta duk a waje suke.

Wani daddaɗan sassanyan ƙamshin turare mai daɗi ta shaƙa, da sauri ta lumshe idanuwanta saboda wani sanyin daɗi da taji ya sauka a zuciyarta, jin daddaɗar muryarsa cikin sanyi yana gaida Ummee, yasa da sauri ta buɗe idanuwanta tana yatsina fuska haɗi da taɓe ɗan ƙaramin bakinta, a ɗage take watsa masa wani kallo, da ƙyar Ummee ta amsa tana wani ciccijewa da watsa masa harara, shiko ko a kwalarsa sai ma watsawa ƴar lelen tata wani wulaƙantaccen kallo da yay yana jan tsaki, da sauri ta duƙar da kanta dan kallon nasa sosai ya daki k'irjinta, juyawarsa kawai yay ya shiga part ɗin Abba, yana ayyana abubuwa da dama a cikin ransa da zuciyarsa.

Bai wani daɗe sosai da shiga ciki ba, suka fito tare da Abba wanda yake shirye cikin wata dakakkiyar bluen shadda wacce tai masa tsananin kyau, ta fito da haiba da dattakonsa, yana riƙe da hannun Saif, yayin da fuskokinsu ke ɗauke da matsananciyar fara'a, a haka riƙe da hannun juna suka ƙarasa gurin dining ɗin, Saif ya ja kujera da murmushi a fuskarsa yace “Zauna Abbana.” cike da jin daɗi ya zauna, sannan shima Saif ɗin yaja kujerar kusa da ta Abban ya zauna, a hankali Ramlat ta miƙe sai da ta watsawa Saif wani banzan kallo sannan ta ƙarasa kusa da Abba ta rungumesa ta baya cike da shagwaɓa tace “Barka da fitowa Abbana.”

Janyo hannunta yay yana murmushi, “Yauwa barka dai babyna, fatan dai kin tashi lafiya?” a ɗan yatsine tace “Lafiya amma ba lau ba Abba...” da sauri ya ja kujerarsa baya yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, ɗan dafe masa hannu Saif yay yana ƙaƙaro murmushin takaici, “Haba mana Abba ina kuma zaka, kai da ake jiranka a office zaka shiga meeting? Gashi lokaci ya kusa, kayi breakfast please tukunna, karka ɓata lokaci.” ya fad'a ya ɗauke kansa ya shiga bubbuɗe wamers ɗin dake kan tebur ɗin hankalinsa kwance, wani irin mugun kallo Ummee take bin Saif dashi, dan kwata-kwata ma ta rasa gane kan lamarin yaron, shi a komai dai sai ya nunawa mutum iyakarsa, tsuke fuska ta sake yi tana watsawa Abba wani irin kallo, “Alhaji baby na maka magana kuma kayi kamar zaka...” ɗaga mata hannu kawai yay, sannan ya janyo pilet ɗin da Saif ya zuba masa soyayyen dankali da kwai sai source ɗin hanta a gefe, ya fara ci yana kurɓar tea mai kauri da Saif ɗin ya haɗa masa, hankali kwance ba tare da damuwar komai ba, kwaɓe fuska Ramlat tai kamar za tai kuka, ta shiga buga ƙafafuwa a ƙasa, a hankali ya ɗago yana kallonta kafin ya taɓe baki kawai, ya ci gaba da cin abincinsa, juyawa tai zata wuce, da sauri Abba ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta, sake kwaɓe fuska tai ta taɓe baki alamar tana gab da rushewa da kuka, sai daya haɗiye dankalin dake bakinsa sannan cikin kwantar da murya mai cike da lallashi yace “Haba mana babyna, kiyi haƙuri mana ai ina sane dake, ki bari idan na dawo dama akwai maganar da nakeso muyi dake kinji, sai muyi a tsanake.” a sangarce ta ɗaga masa kai, kafin ta duƙa tai masa peck a kumatu, ta juya ta nufi ɗakinta bayan ta watsawa Saif wata muguwar harara, ɗan murmushi kawai ya saki ya miƙe daga kan dining ɗin yana goge bakinsa da tissue, kallonsa Abba yay, “Ba dai kana nufin har ka ƙoshi ba?”

Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi, “Eh Abba na ƙoshi, zan jiraka a waje sai ka fito.” yana faɗa ya juya cikin takunsa na izza da taƙama ya fice daga cikin falon, da wani wulaƙantaccen kallo Ummee ta bishi, kafin ta saki wani tsaki tana hararar hanyar da yabi, tsam Abba ya miƙe yana ƙara haɗa rai ya nufi ƙofar fita daga cikin falon shima, da sauri ta miƙe tabi bayansa har ya kai bakin ƙofa, ganin ta biyosa yasa ya dakata a ƙofar falon yana watsa mata wani irin kallo, ɗan tsuke fuska tai tana harararsa ƙasa-ƙasa, girgiza kai kawai yay yaja tsaki ya ƙarasa ficewa a falon yana mai jin tsananin takaici da baƙin cikin mugun halin matar tasa, tsaye ya samesa a jikin motarsa yana daddanna waya, ƙarasa kusa dashi yay ya kamo hannunsa yana dariya ya saka masa abu a tafin hannunsa, ya ƙara damƙe hannun yana kallonsa da murmushi akan fuskarsa, ɗagowa yay da sauri yana duban Abba da neman ƙarin bayani, janye hannunsa yay yana dariya yay masa alama daya buɗe hannun shima, da sauri ya buɗe tafin hannun nasa, key ɗin mota ya gani mai madannai a jiki kamar remote, da sauri ya ɗago kai yana kallon Abba, dariya yay kawai yana girgiza kansa, kafin ya ɗaga hannu ya nuna masa wata haɗaddiyar baƙar BUGATTI mai lulluɓe da baƙaƙen tinted sai faman sheƙi take tana ɗaukar ido daga ɗan nesa kaɗan da inda yake tsaye a cikin wata baranda da motoci suke a fake lulluɓe da tampul, wanda shi kwata-kwata bai ma lura da ita ba ko da ya fito.

Rasa abin cewa kawai Saif yay, sai kallon Abban kawai da yake yana sakin wani ƙayataccen murmushi, janyosa Abba yay jikinsa ya rungumesa yana shafa kansa, sai a lokacin ya samu bakin magana, a hankali ya ɗago yana kallonsa, kafin ya ƙara ƙanƙamesa cike da tsantsar murna da farin ciki yake faɗin “Nagode Abbana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya biya maka dukkan buƙatunka na alkhairi, ya baka abin da kake nema duniya da lahira, wallahi ban...” dakatar dashi Abba yay yana ɗaure fuska, “Dama ni bance kace man komai ba Son, addu'ar da kai min kaɗai ma ta isheni, na gode ƙwarai.” murmushi yay yana nufar inda motar take, bayan yaywa Abba alama daya jirasa, da sauri ya ƙarasa gurin motar ya danna madannin dake jikin keyn tai wata irin ƙara ta buɗe, yaja ƙofar ta buɗe ya shiga ciki ya zauna, yasa key ajiki ya kunnata ya bata wuta, sai da ta dan daɗe sannan yaja ta a hankali cike da ƙwarewa, ya nufi inda Abba yake a tsaye, ya fito ya buɗe masa ƙofar baya, “Bismillah Abbana shiga, yau ni zan kaika office a sabuwar mota.” ɗan dariya yay sannan ya rufe ƙofar daya buɗe ɗin ya buɗe ta gaba da kansa ya shiga ciki ya zauna, ganin haka yasa Saif ya zagaya da sauri ya shiga mazaunin direba yaja motar security suka buɗe musu ƙofar gate suka fice daga gidan, suka nufi cikin gari inda office ɗin Abba yake.

*Comments, share and vote*


          *Aisha Alto*✍🏻

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 10, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIRMAN KAIWhere stories live. Discover now