💕 ❤ 💕
💕 💕
💕 💕
💕
*KAICON SO...!*
💕
💕 💕
💕 💕
💕 ❤ 💕
ŇѦ*ɧAFىAT ɧAFŊAŊ*
watpadd @ Xclusive__hafnancy*ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:ɧaųwa •ى• ʑAɾƖA (MAMAŊ ŲىWAŊ)*
*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚✍*
_•Assalamu alaykum honey bunches😜masu bibiyar wannan littafin ina mika gaisuwata aduk inda kuke,amincin Allah ya tabbata agareku,inaso ne na danyi gyara akan page *1* ,awani wuri zakuga ana referring *SU'AD* to *JALEELAH* ,toh sauya sunan Su'ad din nayi xuwa Jaleelah don haka mistake ne bbu Su'ad acikin wannan lbrn daga farko har karshensa,it's *JALEELAH!JALEELAH!!!JALEELAAAH!!!*°_✍
*
*🅿2*
_*WACECE ASMA'U SANI?*_
*'ASMA'U SANI'* wacce ake k'ira da *'ASMA'* haiffafiyar k'auyen Bodinga ne dake agarin Sokoto.Asma 'yace ga Malam Sani dattijon kirki wanda yasan darajar dan'adam.Matan auransa biyu,Haj.Falmata itace uwargida,'ya'yanta uku kuma duk maza,sai amarya Furera wacce ita kuma 'yarta kwara daya ce tak wato Asma,'ya tilo guda awajen amarya Furera da kuma Mal.Sani.Kasancewarta 'ya mace tilo awajen iyayenta ya sanya Asma take samun kulawa akowani b'angare don hatta kishiyar uwarta na masifar qaunarta da yayunta maza,dake akwai zaman lafiya da kuma fahimtar juna atsakani wanda tun asali Mal.Sani ne ya gina yadda yakeson gidan nasa ta kasance.
Mal.Sani ba wani karfi ne garesa ba amma akwai d'an rufin asiri na Allah,shi dai manomin kayan masarufi ne yana siyarwa akasuwar k'auyensu kuma ba laifi Allah ya d'an tallafa masa.
Mal.Sani yana da wani kani mai suna *'Gambo'* wanda yara ke k'ira da 'Baffa Gambo',bayan haihuwar Mal.Sani,'yan biyu mata ne masu biye dashi,toh bayan sunarsu sai kuma duk suka koma,toh da uwar ta haifi d'a namiji shine ake ce masa Gambo amma asalin sunansa Muhammadu.bayan haihuwarsa ko b'atan wata uwar bata sake ba,sai ya zamana su biyu ne kawai awajen iyayensu,wato da Mal.Sani da Gambo.
Shi dai Malam Gambo mutum ne mai fafatukar neman ganin ya cigaba arayuwa wanda hakan ce tasa ya shiga gari ah inda ya soma neman abin yi,hayar taxi ya soma yi yana d'an tara kudad'e har yaxo ya siyi taxi din kansa,komai na tafiyar masa daidai yadda ya kamata don har takai ta kawo yana tallafawa dan'uwansa da iyalensa acan k'auye.
Bayan komai yayi masa daidai sai yayi aurensa da wata mai siyar da zogale ah tasharsu mai suna Bilki,kuma ba laifi suna son junansu,bayan aure amarya ta tare ah d'an madaidaicin gidan daya gina ah U/sabon birni,ba wani babban gida bane,dakuna uku ne kacal sai kicin da bayi,da d'an filin tsakar gida.
Shekara daya,biyu,uku har hudu shiru,Bilki zata haihu amma shiru kake ji kamar mutuwar sarki.Tun abin baya damunsu suna tawakkali har yaxo ya soma damunsu musamman Bilki wacce tafi tada hankalinta akan rashin ganin gudan jininta aduniya,kuma tsoronta daya kar Mal.Gambo ya qaro aure don hakan zai zamo tamkar cin fuska ne agareta.sai kuma akaci sa'a Mal.Gambo bamai ra'ayin ijje mace fiye da daya bane agidansa don acewarsa baya son tashin hankali duk da cewar yana sha'awar iyalen dan'uwansa na yadda suke zaune qalau amma hakan besa yaji sha'awar shi ya ijje matar aure fiye da daya anasa gidan ba musamman idan yayi duba da yadda matan abokinsa Mal.Awwal basa zaman lafiya kullum cikin rigima suke,toh sai yaji duk baya sha'awar qaro auran.
Haka dai ya haqura ya fawwalawa mai duka komai,ya cigaba da lallashin matarsa,suka kuma cigaba da kai kukansu ga Allah kan ya azurtasu da 'ya'ya na kansu masu albarqa,
