💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)Page 72
......Ahankali me gidansa ya d'ago yana dubansa fuskarsa d'auke da murmushi, sannan yace " ya kaja ka tsaya kana mamaki,ka k'araso mana ka zauna ....
jiki a sanyaye fu'ad ya k'araso yasamu guri kusa da me gidansa ya zauna har lokacin idanunsa na kanta , sannan zuciyarsa na cike da matsanancin mamakin abinda ya kawota "to me take nufi dashi...?
"Ana so dole ko kuwa dazata zo gurin me gidansa?
"Shifa baya son kayan nacin nan, haka mead ta dinga yi masa naci har daga karshe tasamu nasarar mallakarsa yanzu kuma ga sajida.Itama tun daya shigo parlour'n idanunta ke kansa tana kare masa kallo tsab ko kifta idanunta batayi,domin sosai kayan dake sanye jikinsa suka masa maseefar kyau ,bayan bayyanar da sumar kirjinsa da sukayi a filli saboda bai rufe maballin rigar har sama ba ,azuciyarta tace "baby kayi masefar kyau tana kada masa kwayar idanunta, wani irin sabon shaukin soyayyarsa ce ke sake taso mata tare da huda kowa wani sashi na gangar jikinta, adduarta daya Allah yasa zuwanta yayi mata amfani yazamo silar yin aurensu..
tsawon minti goma da zamansa, batare da me gidansa ya sake cewa dashi komai ba illa coffee dayaketa kur'ba kad'an kad'an yana karewa yanayinsu kallo had'e da nazarinsu ,sannan ya ajiye cup din akan D'an karamin table din dake ajiye agefensa kana ya numfasa, tare da kiran sunansa "fu'ad kasan kowacece wannan yarinyar dake zaune?
Take Gaban fu'ad yabada wani irin rasssss yashiga duka uku uku sannan yace "sir na santa kawar matatace....
"Ok meye tsakaninka daita saboda tazo min da wata magana..?
"Babu komai atsakanina daita face gaisuwa..Jin haka yasa gabanta faduwa itama take kuma zuciyarta tashiga rawa "babu komai tsakanina daita face gaisuwa ta sake maimaita abinda ya fada tana kuresa da idanunta, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu.
Naunayen ajiyar zuciya me gidansa yaja ya sauke sannan yace sajida ko ?
Da sauri Ta d'aga masa kai . "Dan bamu guri ki shiga dakin can kijiramu.ta mike tsam zuciyarta na wani irin dokawa, jikinta na rawa tana jin kar ta kurma ihu ta shiga dakin daya nuna mata wanda ke facing dinta.
"Fu'ad wannan yarinyar tazo min da zance tana sonka da aure, a yadda tabani labari tace sama da shekara goma ta d'auka tana dawainiya da soyayyarka tun kafin ka aure me'ad, giftawar me'ad tsakani, yasa ta dane nata soyayyar, Amman a dan tsakankanin wannan lokacin take jin bazata iya hakura dakai ba ,kodan matsalar dake faruwa agidanka ,tayi alkwarin zama da kai da amana tare da kulawa da nasreen,inda har tace zata ajiye aikinta ta zauna zaman aure da kulawar gidanka,Dan haka me zaka iya cewa yanzu akan wannan lamarin?
Wani irin naunayen ajiyar zuciya da numfashi ya sauke atare, yana duban me gidansa sannan ya bud'e bakinsa da kyar tmkr me koyon mgn "sir duk naji bayaninka, sai dai Dan Allah kabata hakuri saboda banida niyyar k'ara aure ahalin yanzu, ta gidana ma ban gama daita ba balle nayi tunanin kara aure, auren ma da aminiyar matata wace Allah kad'ai ne yasan tsakaninsu ,bana jin iya aurenta ,domin kuwa aurenta shine babban abun kunyar da zan aikata arayuwa yakarasa fadar hk yana me sukuyar da kanshi kasa....
"Babu zance kunya, abinda yakamata kayi kenan... domin musguna matarka bisa ga mummunar halaiyarta, auren sajida kad'ai zai sa tashiga hankalinta ..duk wace zaka aura bazai ta'ba mata ciwo ba kmr auren sajida, bugu da kari yarinyar na sonka da alamun zata maka biyayya tunda har aikinta tace zata ajiye ta kular maka da yarinka abinda matarka ta gida ta gazayi maka kenan .
"ni dai amatsayina ina baka umarnin da shawarar ka aureta kawai kasamu ingancin rayuwa nmj ne kai kana damar kara aure fiyye da daya ,karka sanyawa zuciyarka damuwa feel free kayi abinda yadace...

YOU ARE READING
'YANCINKI
Romance'YANCINKI ALL TALK ABOUT ROMOTIC, TRUE LOVE ,DIS RESPECTING THE PARENT, BREACH OF TRUST ,UN ACCEPTING WHAT'S ORDAINED BY GOD.