15

1.4K 77 0
                                    

ZUCIYAR MASOYI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 15

Washegari tun safe suna tare dady  suna tura sakwanni wa sauran branch din company dinsu dake sansa daban daban "Dady sai
  shagwaba Abdullah yakeyi hade da  ririta shi saboda namijin kokarin dayayi".Sai bayan sallar ishai sannan yashiga part din maminsa yayi dinner ya Mike hade da mata sallama mami takira yadan juyo yana karyar da kai ta tsareshi da idanuwanta ina zaka kuma yau kusan kwanaki masu yawa ban saka a idanuna ba balle muyi hira   Abdullah yayi murmushin mamina ina zuwa ba koina zani ba tace A,a sam banyarda ba dawo ka zauna yadawo kmr yadda tace  kallo daya ta masa tagane inda yake son zuwa, ta hadiye abinda taji ya tsaya mata a wuya.. sannan tasoma Yi masa hira tun yana gane kan zance nata har yazo bai Gabe abinda take cewa gashi sai yamike da niyyar barin falon sai dawo dashi  , uhmm yauwa Abdullah sai ta kuma dauko wani zance a haka dai yasoma tunanin yasan yauma dai maminsa tana son ta rusa masa burget dinsa daga karshe yagama  fuskantar mami batason  fitarsa ne ya Mike yayi  kwanciyarsa  akan three site din falon ya runtse idanunshi yana Jin yadda zuciyarsa ke  harbawa ""ya daura hannushi daya a dai dai saitin da zuciyarsa ke harbawa gabadaya ji yayi  hankalinsa bai gangar jikinsa tun yanajin mami sama har yazo bai jinta yanan kwance  kusan 30 minti  sannan yamike  zubur kmr an tsikare sa  ya bar falon mami na kallon kmr zatayi kuka addu'a kawai takeyi azuciyarta Allah yasa Abdullah ba gun yarinyar nan zashi ba  ...  ....

hankalinshi a tashe yake shi kadai yasan me yake ji a zuciyarsa yau dai komai za'ayi  sai  yaje yaga Aisha  muddin bai je yaganta ba  zuciyarsa na gaf da  bugawa "  ko wanka bai tsaya yi ba" har yace salis ya jirashi ya  fito suwuce ,Amman suna fitowa ya sallami salis shi kadai yake tuki ,cikin kamarar benz baka yayi Parking agefen titi , ya fito ya kulle motar sannan  yakarasa cikin lungun su Aisha goma batayi lokacin dan haka mlm abu yana nan a waje da kwarin gwiwa Abdullah yakarasa tare da sallama sannan har kasa ya risina yana gaishe da mlm abu...

Mlm abu yakashe radiyonsa  dayake ji ,cikin natsuwar yake kallon Abdullah din byn ya amsa gaisuwar sa ko kadan bbu damuwa ko bacin rai atare da yaron hakan ya kara sa mlm abu cikin wasi wasi yasoma tunanin anya  yasan halin da ake ciki  a game shi kuwa ?a fili mlm abu yayi gyara murya ya dubi Abdullah har yau yana da wata kima da daraja a idanunsa ,yace Abdullah ko? ALHAMDULILLAH daman kai muke Jira koda bakazo mu akwai bukatar muje ga mahaifinka "mudan jinkirta wa zuwanka ne domin ta inda aka hau tanan za'a sauka ya dan tsagaita sannan yace Abdullah mahaifiyarka tazo .....a frigice Abdullah ya dago ya kalli baban Jin sa ya tsaya dip ... yadaina ji komai nawani lokacin kmr an dura masa ruwa a kunne haka yake ji sannan ya girgiza kansa yana mai sauraron mlm abu.....hakan ya nuna wa mlm abu cewar bai san da zuwan nata ba mlm yacigaba  sun zo ranar lahadi ,kuma a yadda ta nuna bada saniyyyarta akazo nema maka aure ba ...Abdullah alahakikanin gaskiya  anci zarafinmu sosai dan bamu da komai wanda har hakan yasa na kudirce araina  nima duk ranar da ka sake zuwa kofar gidana da niyyar neman diyata  hukumace zata raba mu" Amman daga baya nayi tunanin kafin ayi haka afarayin hannun riga daga baya in yaso idan wani abu ya faru ko ma menene sai ayi ....

Mlm abu ya numfasa yayin da kirjin Abdullah yacigaba da bugawa kmr ana buga masa guduma "kamar yadda akace tsiya ce tasa muke haukan son hada ka da banzar diyarmu to a haka nakewa Allah godiya har nan ka Tako bazan  manta ba kozo neman ta.. dan haka duk haukan tsiyarmu da mukeyi sai da kazo sannan muka fara , saboda haka ni mlm abu nace kaje can ka nemi diyar masu arziki ka aura Amman ba dai  diyata Aisha ba...... ZUCIYAR Abdullah CE ta tsaya cak tadaina aiki  na wani lokaci sannan  dagabaya tacigaba da bugawa da sauri da sauri  sakamakon Jin maganar da mlm abu yace ,  duk wani kuzari da karfin jiki bbu shi atattare dashi  hankali atashe yake bin mlm abu da kallo kawai yake Yi " mlm  abu ya jijiga masa  kai alamar haka zance sa yake .... Sai yanzu   Abdullah  yasamu  yayi magana cikin sarkewar murya tare da dunkule hannuwanshi duka waje daya yace dan grman Allah baba kar kamin haka idan akai haka wlh komai zai iya faruwa dani ...

Mlm abu yayi murmushin takaici yace sai dai kayi hakuri , saboda mahaifiyarka ta Raina yadda Allah    ya ajiye mu cewa tayi zata bamu million goma domin in raba diyata da kai ...dan haka ko kai kadai karage mata  a duniya gara ta zauna jiran wani da na baka ita" saboda haka duk wani cin zarafi da cin mutunci da aka zo akayi mana har gida wannan munbarshi akan haihuwace ta tajawo mana haka .Amman halaka ta aure tsakanimu bbu shi har abada. in Allah yaso ni da kaina zan  zaba mata miji da yayi min kuma daidai da ita ...

Abdullah ya zubawa mlm abu idanunshi jikinsa har karkarwa yake tsabar tashin hankali dayake ciki musamman da ya karanci hakikanin gaskiyar mlm  abu yake fada masa ,yace to.....sai kuma yayi shiru yana juya kansa cikin sanyi jiki yace baba bari na koma gida gurin mami wallahi zata yarda idan naje zata amince in ....aure .. Aisha dan Allah kar kabawa kowa ita ni kadai ne mijinta ...

Mlm abu ya kalli Abdullah ya gane duk a rude yake da maganar.. ya dada fuskantar yadda yaron yake son Aisha Amman hakan da yayi shine kada zai sa su tsira da mutuncin su , yace Abdullah idan kaje ka samu mahaifiyarka da zamce ai asirin da ake fada munyi maka za'a sake kallo da har yanzu yana cinka , dan ma  banda mahaifiyarka ce Amman yadda aka zo har  gida aka keta mana haddi muka  dauki hakuri,kaima hakan ya kamata dole kayi hakuri da Aisha....

Abdullah ya hadeye wani dunkulalle abu dayake Jin sa a makogaronsa yana kallon mlm abu daya fara nade tabarma dayake kanta ,tare da daukar radiyonsa ,idonsa suka yi   jazir ya zube gwiwarsa a kasa yace na gode baba Amman dan ka taimake ni naga Aisha koda ganina da ita na karshe kennan ...

    Mlm abu ya masa duban tsab kmr wanda yake son ya karya masa maganarsa banda ma darajar sa data mahaifinsa ai da yanzuya kore shi  daga kofar gidansa ".yace wannan kana maganar wani al'amari ne da ya shude ya zama tarihi a game da fitowar diyata wajenka ina fatan idan ka koma zaka sanar da mahaifiyarka in Allah yaso gobe  suzo su karfi komai na aurenka in kuma basu zo ba yana kan hanya , sannan mlm  abu ya juya zai shiga gida.

Allah sarki Abdullah bawan Allah rasa yadda zaiyi yayi ya Mike a hankali tamkar ma baya cikin hankalin sa kmr ya manta dawa yake magana yace to baba idan kashiga kacewa Aisha ta taba cewa zatamin addu'a kuma nasan tayimin to yanzu ma dan Allah tayi min addu'a akan dukkan abinda zai faru a kaina a dalilin ta...sai  da mlm abu yagama ji hakan sannan ya shige gida maganar Abdullah ta tsaya masa arai , musamman yanayin sautin daya fadi hakan dashi .....

Abdullah ya zubawa kofar gidan ido mami ke kallon yafi karfin Aisha Amman shi tun daura idanunshi akanta da yanayinta yake ganin kmr zatafi karfinsa ,a duk zuwan da yake gurinta a hakan yake kallonta har gashi a yanzu yake tsaye a kofar gidan su ya dada gane da gaske Aisha tafi karfinsa ...

Ya jima yana kallon kofar gidan jitake kmr ya shiga har inda take ya daukota ya gudu da ita, kowacce kasa a daura musu aure in yaso idan ta tasamu ciki ko ta haihu sai  ya  dawo da ita su bawa iyayensu hakuri" a sannan bbu mai raba su , hannushi duka biyu ya soke cikin aljihun wandonsa ya zubawa kasa Ido tare da tura lip's dinshi  na kasa a baki ya dago Ido yana sake kallon  kofar gidan idanunshi sun jazir dasu sannan ahankali ya juya ya soma tafiya cikin sanyi jiki shi kansa bai san a wani irin yanayi yake ciki ba ...

Tun tara da yan mintina  ranar da mai gadi ya sanarwa alhj ishaq rashin ganin dawowar dan nasa gida hankalinsa yake a tashe har yanzu da gari yawaye  ya sanar da police haka nan securities dinsa sun bazu koina ,ko  mami basu sanarwa ba sai byn sallar asuba domin yasan ita bata wani hakuri akan ya'yanta don haka ya kyaleta ,sai da rana yadda mami ta dinga Yi kamar Abdullah  kadai ne danta .....

inda mami sukayi magana da alhj ishaq akan aure ,daman abunda dady  ya guda kennan ,to har zuwa karfe uku  na safiyar ranar bbu wani bayani akan Abdullah Allah sarki dady har kasa zama yayi sai karfi goma da mintina sannan  ya amsa wayar police da daya  daga cikin wayoyin Abdullah, cewa yazo  teaching hospital sir yahaya da gaggawa an tsinci Abdullah cikin wata benz baka mai dauke da number I. M sidi magaji yayi hatsari.. sai da dady yayi da gaske sannan mami ta hakura da binsu dan kusan tafi dady gigicewa  ..........

MMN SUDAIS CE

zuciyar masoyi Where stories live. Discover now