GABA DA GABANTA 25-26

922 35 0
                                    

*GABA DA GABANTA*

              *NA*

*PRETTY SALMA*

*WATTPAD@PRETTYSALMA173*


'''DAGA MARUBUCIYAR '''
*ILLAR KULLE*
*A'I BALA'I*
*RASHINJIN MAGANAR IYAYE*
*DIJEN KAUYE*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_25-26_*






Kai tsaye gida yakoma,yatarar da nabila zaune kan kujera tahada tagumi,ganinsa datayi yashigi yasa tatashi tsaye tarike kugu,shiko yasamu guri bisa kujera yazauna.
"To munafikin Allah,annamimi,wallahi kai wutarka daban take ko acikin ayan jahannama"

Kallonta yayi yana gyada kai yace,"yanzu ni nabila ni kikecema dan wuta,koda bakisanniba ai bakyqmin fatan hqkanba,balle ina matsayin mijinki"

"Naje nafada,ai ba karyanayiba,ni banda kaddara da tsautsayi bansan miyasa na aurekaba,kuma wannan tsohuwar kilakin dakake kokarin kawomin amatsayin kishiya,bance kada tazoba,tashigo,inajiranta,nida ita dakai shege kafasa,munafikai kawai daku"

"Duk abinda zakice kice,aurede nida bintu kamar anyi angama,cikin wannan satin zatashigo gidanan amatsayin matata,idan kinayima Allah,kuma idan harkin isa kihana faruwan hakan,muzuba mugani"

"Hakq kqce ko"hakade kace?,to wallahi zako kaga abinda zai faru"fuhhhh tashige daki.
Shiko gyada kafada yayi irin ko ajikina dinnnan.

******************

Iyayen kabir sunsamu iyayen bintu antsaida magana akan ranar jumq'a za'a daura aure,sunbada sadaki da duk abinda yakamata abayar sana sukatafi.

Cikin jin dadi bintu takira kb tanasar dashi,shima cike da murna yace Allah yakaimu lokacin suka amsa da amin.
Bintu nagama waya da kb taajiye wayar kenan saiga kira daga sabuwar number,da kamar bazata dagaba,wata zuciyar tace tadaga,dagawa tayi,amma batayi maganaba,jitayi anata zaginta,zagi nacin mutunci,koda baasanarmataba tasan wacece,wadda bayawuce matar kabir,batace da ita kalaba kawai takashe wayar sana tasaka number a black list,batakai da ajiye wayarba saiga kiran guy yashigo,nan tadaga,tqnadagawa yace tasamesa akofar gida kawai shima yqkashe wayar.
Tashi tayi tadauki mayafinta tafita izuwa waje,tsaye tagansa abakin motarsa yaharde hannuwa,karasowa tayi taname sallama,wanda ko arzikin amsa sallamar tata baiyiba kawai yahauta da cewa.
"Ashe dama ke mayaudariyace,macuciya,azzaluma bansaniba"

Cike da mamaki bintu ke kalllonsa tace"bangane inda kalamannan naka suka dosabafa"

"Eh,dama taya zaki gane,bayan kedin dakikiyace,jahila"

"Ya'isa haka,ya isheka,kabar ganin nayi shiru,hakqn bayanuni dacewa inatsoronka,banga dalilin dazakazo kanacin zarafinaba,akan mi?"

"Eh,dama ai dole kifadi hakan,nan mukqyi dake cewa,zan aureki,kikanunamin ke aure bayagabanki,amma sai yanzu naji labarin wannan juma'ar zaa dauramaki aure"

"Hahaha,wallahi harkabani dariya,kai ina kataba ganin dan iska ya auri dan iska,ai bazai taba yiwuwaba,kai kodama ya yiwu,to zaman nasu takaitaccene,domin kuwa kar tasan karce,kuma dakakecewa kaji labarin wai zanyi aure,to kafidda batun wai ma,bawai bane,dagaskene,zanyi aure ranar Friday dinnan mai zuwa,so daganan sai nace saduwar alkairi,Allah yayafemana baki daya"tajuya zatatafi kenan taji yayi jaking nata,tsayawq tayi tajiyo tana harararsa.

"Wallahi bintu baki isaba,inada rai babu wanda ya isa ya aureki,sede ki mutu bakiyi aurenba,muddin bani kika auraba"

"To dan girman Allah idan ka isa kahana"

"Zan nunamaki tabbas nidin kuwa na isa,ke bari kiji,koda andaura aurannan kafarki bazata taba taka gidan wani da sunan aureba,sainasa ankasheki,kowama yarasa"

"Kai haba,dagaske?,to inajira,kasa akasheni din,idan ka isa,kokuma nace idan raina ahannunka yake,banza dakai shashasha"kawai tashigewarta gida tabarsa anan.

Tana isa dakintq takira  ramla tazayyanemata duk abinda guy yayi ikirarin abinda zaimata,ramla tace kada tasake tasakama ranta damuwa,babu qbinda ya isa yamata wanda Allah baimataba,ahaka sukayi sallama.

Hidima takankama,amarya sai shiri akeyi anagyara kai,ga kunshi da kitson attach anshq,kawayen amarya sai kodata sukeyi,ranar alhamis yau kenan zaaje ayi jere,bintu tacanza duk kayan dakintas sabbi gal,kb yabata kudi isassu tasayi komi,yan dubai tasiya,ga set din kujeru royal suma,sabbin cuttins,kai komima sabo  ta canza,inda kuma su ramla zasuje ayo jere ayau din.
Mota kb yaturo akakwashi kaya sai karama akadauki mutane,ciki ko hadda amarya akaje gida,lokacin nabila nazaune tanacin taliya da manja,abinka gamai karamin ciki,sai gani tayi anashigowa da kaya ana ajewa,har akagama shigowa da komi,ramla tadubi wadda ke zaune tace.
"Ga dukkan alamu kece matar gidannan,don haka kinunamana dakin amarya zamusa kaya aciki"

Ko kallon inda ramla take nabila batayiba illa cigaba dacin abincinta datakeyi.

"Baiwar Allah dakefa ake magana"ramla takara fada.

Nabila batayi maganaba sai daga bakin kofar wani bedroom sukajiyo anafadin"shi wanda yabaku izinin zuwa da kayan bai fadamaku inda zaku ajiyesubane,zakuzo kudami mutane dawata maganar banza" surry kenan tafada haka.

Juyawa ramla tayi inda taga mai maganqr tsaye,dan murmushi tayi sana tace"uhmmm,amma ko bantambayaba,nasan kece kawar matar gidannan surry kike kowa,to bari kiji,idan ina magana da mutum baasanyomin baki,sai idan da wanda nake maganane zaisamin baki,kikiyaye,don gudun bacin raina"
"Kekuma nadawo gareki,canake kece matar gidan,kuma kece wadda kika gaza har mijinki yayi sha'awar karo aure,so kitashi ki gwadamana daki mushiga muyi abinda yakawomu"

Duk wannan maganganun da akeyi bintu bata wajen,tanacan waje itada wasu kawayen nata suna surutu.

Mikewa nabila tayi tazari tisue tagoge hannunta sana tadubi ramla cike da takaici,wanda takeji dama wuka nakusa da ita,dasai takashe yarinyarnan har lahira,amma tadaure tace.
"Ahayye nanaye,wane darene jemage bai ganiba,ai sede daran mutuwarsa,ayide mugani idan tusa zata hura wuta,dakike maganar gazawata,alhamdulillahi,ninasan mijina bagazawa yayi daniba,babu tabangaran danaragesa,balle kibude wani banzan kazamin bakinkican kifadamin wai nagaza,keee ba saaryinabace,kibari ita wadda aka auro din,tazo mugoga bura daya da ita,amma bake karereba,matsiyata dakuba"

Tassssss kakejin anwanke nabila da maruka har biyu,gefe da gefe,aiko marin yashigi nabila ba karya,dafe kumci tayi alamun taji azaba.
"Idan kin isa ke cikakkiyar yar barikice,kikara mai maita abinda kikace,kiga yadda zanmaki,ni ba kanwar lasabace,samun bintu kikayi,kuma ita takyaleki,amma ni baayimin akwashe lafiya"

Tahowa surry tayi tatsaya tare dafadin"lalala,kikamareta"?

"Eh anmara,koda abinda kema zakiyine?"

"Dan Allah idan kin isa kikara marinta kigani"

Ai kafin surry tarufe baki ramla takara daga hannu takara shararama nabila maruka lafiyayyu"

Still surey tace"idan kin cika ke yar halakce kikara marinta mugani"

Ji kake,fass fau fess,takara wanketa da mari,kafin ramla taajiye hannunta,surry tadaga nata tawanke ramla da mari itama,cikin mamaki ramla take kallon surry.
"Kika mqreni"?

"Anmara"

Daga bayansu sukakara jiyo wani sautin mari mai rai da lafiya,wanada bakowabace akamara face surry,bintuce tawanketa da mari sana tadaura dacewa"gobema kisake gigin marinta kigani,wallahi sede uwarki tasa bada gindi ga maza suci takara haiho wata mai kama dake,amma bade keba,shegiya karamar karuwa dake,kallin ramla tayi tace,miye zaki biyema karnuka,haba ba ajinki bane,kuzo muje ga dakincan wanda ke kallonmu"

GABA DA GABANTAWhere stories live. Discover now