🌹🌹DEEDAT 🌹🌹
wattpad
Rashmarrka
Writing by ( maman khady)
Page 1
Tafe take tana tsale 2 tana wakarta da tasaba kuma a cikin wakar baiti daya ta iya aciki " karka manta dani kobabu raina dan Allah kadinga tunawa dani " shikadai take maimaitawa a daidai lokacin da ta karaso gida da mugun gudu tashiga gidan tadauki buta tashiga bandaki dan fitsari takeji yamatseta innah wuro natsakar gida zaune tana soya man shanu batace mata kalaba dan tasaba da halin SA IMAH fitowa tayi ta wakarta tashiga daki tajawo kwanon fira innah wuro ta kwalla mata kira amasawa tayi daga cikin dakin innah wuro tace kizo kidebo mana ruwa Wanda muke dashi yakusa karewa tunda tunsafe kika fita gantalinki baki dawoba sai yanzu dan nasan yunwace takoro ki da bazan gankiba sai dare SA IMAH ta amsa da to bari ingama bata dadeba tafito tanacewa inah tulun yake innah wuro tanuna mata inda yake dauka tayi ta nacewa sai nadawo innah wuro tace dan Allah SA IMAH karkije kizauna wasa da ruwa kinga rana tayi da yanzu karfe 1 SA IMAH to amsa da to tayi gaba tana wakarta tanafita wata yarinya ta hango dauke da tulu ta debo ruwa SA IMAH gurinta ta nufa tanacewa wana kama yarinyar tace dan ALLAH kiyi hakuri innah ta kejirana zata Dora mana abinci SA IMAH tace zan yafe maki amma kikai ruwanan gidan mu yarinyar dasauri ta amsa da to dan tasan idan batakai ruwanba ba itaba har iyayenta sai SA IMAH ta adabe su da fitinarta
****
Motoci kusan guda shidda ne suka jero da mahaukacen gudu kamar zasu tashi sama jiniya ke tashi dagaji kai kasan babban mutum ne aciki duk Wanda yaga haka gefe yake komawa dan tsaratar da rayuwarsa wani daga gefe yace waye wanan wani dattijo yace kai bakaga number motar ba Wanda yayi maganar yace a a ni ban luraba dattijon yace DEEDAT kenan Wanda yayi maganar yace wane DEEDAT tsohon yace amma kai bakone agari nan yace eh banfi sati da zuwa ba tsohon yace gaske dai dan duk fadin garinan babu Wanda baisan iskancin yaronan ba dan gidan Alhaji Hashim ne mutumin yace ah kace dan gidan karunane duk Nigeria waye baisan Alhj Hashim ba yace oh kodai shine dansa guda day tilo da ake cewa yadade bai haihuba sadaga baya aka haifeshi tsohon yace eh shine mutumin yace banaji ance soja neba tsohon yace eh sojane amma bayada mutunci ko kadan mutumin yace amma naji ance yana zuwa unguwar talakawa yana taimaka musu tsohon yace indai barin kudine baisan ciwon suba yanada kyauta amma karka shiga gonarsa dan yanzu zai daukeka da bindiga ko yasa atakaka da mota mutumin yace Allah ya kyauta ya amsa masa da amin
Kwance yake abayan motar ya lumshe idanunsa kamar mai bacci amma ba bacci yakeyiba sanye yake da wando sojoji sai farar riga dayasa ba karamin kyau kayana sukayi masa ba Horn driver yayi dakarfi saida mai gadi ya firgita dagudu yakaraso gurin get din dan yasan yana kara 1 mint zaikarbi hukunci gurin yaran oga DEEDAT dan basuda mutunci yanzu zasu iya takaka da shegun takalmin su ko su zaneka yana bude masu get dagudu motocin suka shiga sai hannu mai gadi yake dagamusu jin tsayawar mota yasashi bude idanunsa wow below eyes nagani bakaramin kyau yakara masaba fitowa yayi daga motar gaskiya kyakyawa ne nakarshe gashi doga farine tas kamar ba dan Nigeria ba shiga babban falon gidan yayi sallama yayi ciki2 idan bakusa dashi kakeba bazakajiba wata dattijuwa ce zaune dagani kasan mahaifiyar sace tana sanye da wata tsadadiyar atamfa kusa da ita yazauna yanacewa wash Ammah nagaji murmushi tayi yashafa gashin kansa da yake sheki tace my son sannu da kokari yace Ammah papa baidawoba tace eh badawoba
****
Sai dab da magariba SA IMAH tadawo gida koda tadawo baffanta yadawo dugudu ta isa gurin shi tanacewa lah baffa hakadawo daga birni yace yar baffa nadawo innah wuro akan haushinta da takeji batace mata kalaba
Washe gari ranar juma a duk musulmi yana kwaliya juma a haka SA IMAH taci kwaliyarta tafito daga daki zataje yawonta innah wuro ta cemata karki dade tace to inah tanafita ta hadu da wani yaro an aikoshi gurin baffanta tareshi tayi tace kai inah zaka yqbata amasa dacewa gwaggo ce ta aikoni gurin baffa idan zaije birni yasiyomata fitilar hannu karbar kudin tayi tace kawo nakaimasa ba yanda ya iya yamika mata kudin yajuya yatafi kai tsaye kasuwar garin ta nufa bata dawoba saida dare yayi ta nufi hanyar gida tana isa kofar gidan tajiwo murayar gwaggo bala I aranta tace zakiga makirci tafara kuka munafurci tashiga gidan

YOU ARE READING
DEEDAT
ChickLitLabarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam...