35

3.6K 336 34
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers Association*_

*35*
*Unedited*

   Ya fisgi motar sa a 360, bai zarce ko'ina sai GT bank, Rough parking yayi ya fito, Fuskar sa a d'aure tamkar wanda aka aikowa da sak'on mutuwa,  Ya shiga bankin, Manager bank d'in ya buk'aci gani, ba b'ata lokaci aka sada shi dashi.

    Cike da girmamawa ya tarbe sa, Ya nuna masa seat ya zauna, Suraj ya zauna, yana cije lips na k'asa, Suka gaisa, Ya zayyane masa abunda ke faruwa,  Manager ya jinjina kai yace "Abu ne mai sauk'i, zamu duba suna da time d'in da aka cire, su Cashiers d'in bara su kasa rik'e face na waye and akwai cameras", Suraj yace " Do your possible best", "OK Sir"

     Ya samu Cashiers ya tambaye su a wurin wa aka yi withdrawing 500m yau, Chioma tace "Am the one Sir", " Waye yazo?", "A lady with niqab", " Muga record ", Ta d'auko littafin ta basa, Ya shiga dubawa Aisha Lawal ya gani, 9:30 na safe,

    Ya koma yayi wa Suraj bayani, " Lady with niqab kuma Aisha Lawal", Ya furta, Manager yace "Yes Sir", " Toh wacece?, ko namiji ne yayi shirin mata dan ya b'atar da kama?", "It can be", Cewar Manager, " Thank You Manager, idan akwai buk'atar wani bayani zan dawo", Ya fad'a yana mik'ewa, "OK Sir",

    Ya shiga mota, ya zauna tare da d'aura kansa kan sitiyari yana nazari, " Waye zai yi wannan aiki?, Wallahi I won't spare him", Ya fad'a cikin karaji.

     "Kai ban fita da cheque ba, na tuna da na fito wanka ina sauri ban d'auka ba", Ya tabbatar wa kansa, " Fatima has something to do with it", Wata zuciyar tace "Why will she do so, tayi yaya da kud'in wanda basu kaisu bama, ta nuna bata so, maybe wata ta shigo gidan, i have to find out", Yaja kan motar sa zuwa gida.

      Yasmeen na zuwa gida da kud'in, K'atuwar akwati ta samu, ta zuba duka kud'in da kulle da padlock, ta d'aura can saman drawer, ta d'aura wasu akwatuna a kai, babu wanda zai d'auka akwai kud'i a ciki.

     " Ya Allah ka shigewa Fetta gaba, Allah ya daidaita su da Suraj, kasa musu soyayyar juna, Allah ya d'aura mishi zazzafar k'aunar ta", Ta furta tana sauke ajiyar zuciya, Ta fice zuwa kitchen taba ciki hakk'in sa.

    Securities na bakin gate, Ya tambaya "Wata ta fita da niqab?", Habu yace " Eh Ranka ya dad'e", "K'arfe nawa", " Da safe wuraren tara", "Ta dawo?", " Eh", "K'arfe nawa", " Goma ta wuce"

       Ya k'arasa ciki kamar zai tashi sama, "Fatima", Ya furta yana squeezing hannun shi,

       Tana zaune falo ya shigo, Ta tsorata da ganin yanayin sa, Ta dake tace " Sannu da Zuwa", "Yawwa", Ya amsa ba tare da ya nuna mata wani abu ba, " Waya zo wurin ki d'azu?", "Ba kowa", " Kin tabbata?", Ta d'aga kai sama, Ya wuce d'aki ba tare da ya sake cewa komai ba.

    Jikinta yayi sanyi "Ya Allah ga baiwar ka, bani da nufin sharri a kansa, Allah kayi mun jagora"

    D'akin ya shiga bincike, duka drawers, da akwatunan ta sai da ya duba, bai ga wata alama na ita bace.

    Wayarta dake jikin chaji ya d'auka, bata saka mata password ba, Yaji dad'in hakan, Ya fara bincike WhatsApp da text messages bai ga komai ba, Har zai ajiye wayar, ya shiga contact, d'aya bayan d'aya yake bin numbers d'in, Idonsa ya kai kan sunan Alhaji Tambari,

      "Alhaji Tambari", Ya furta, " Meye alak'arta dashi?, ko sun shirya cuta ta ita dashi?", Ya shiga girgiza kansa yana fad'in "Noo", Yayin da zuciyarsa ke k'ara tabbatar masa " Had'in baki ne ita da Alhaji Tambari"

FETTA (COMPLETED)✅Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon