'DAN'DANO

15 2 0
                                    

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFAI UKU DA KUKE SO, WADANDA SUKE TAFIYA CIKE Da BAN SHA'AWA DA BURGEWA! AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL!!*

*DANDANO DAGA* _*KISHI NE!*_
Tare da alk'alamin MAMAN HANEEP

*KISHI NE*

Cikin tsantsar b'acin rai da d'acin da ke yawo cikin zuciyarta harta ke jinsa saman harshenta, ta yi kukan kura ta shak'o wuyan Amina kanwarta wacce suke uba d'aya.
Cikin huci ta shiga firta" Meye laifin y'ay'a Dan Allah ya yosu a matsayin 'ya'yan mijinki? Me sukai miki zaki azabtar dasu? kin zauna da uwarsu ne? Mai uwarsu tayi miki balle kice ramuwar gayya kikai a kansu Amina?.

Cikin sanyin jiki ta saki wuyan Amina wacce keya kakarin aman don muguwar shakar data a hannun maryam ba karama bace.
A hankali ta ja baya tareda firta" Nina ja muku Affan ku yafe ni, ku ya feni Dan girman Allah da ban kasance mai taurin kai da kinjin maganar iyayeba da duk hakan bata faru ba, da wanne ido zan kalli Yaya Fatima in munhadu a aljanna? Ban rike amanar data bani ba.

Tana kaiwa nan ta wawuri wuka tayi kan Amina a sakamakon kallon bayan ummu khulsum da tayi Wanda shatar dutsen guga ya fito d"odar a bayan yarinya, fatar gun duk ta kwashe sai tsallara ihu yarinyar take alamun rad'adin kunar ke ratsata,
Ganin tayi kan Amina da wuka yasa Adam yin hanzarin dakatar da ita, amma ina kan ya kai ga riketa har mai afkuwa ta afku....

Meke damun matan wannan zamanin? Shin kishi haukane?

*DUNIYA BIYU!*
Tare da alk'alamin _*JEEDDERH LAWALS*_

Jikinta rawa yake, ba kuma rawa ta kadawa ba, rawa ta karkarwa kamar wadda ke cikin matsanancin hali na zazzabi. Wannan wace irin masifa ce? Bata taba ganin tashin hankali irin wanda take gani a gabanta a yanzu ba.

Fauza jijjiga take kamar wadda ake kadawa mazari ko za ta hau bori. Gashin kanta da ya sha karin izgar doki yayi buzu-buzu, dankwalin kanta ta kama shi ta daure a kugu.

"na rantse da Allahn da Ya halicce ni, yau sai na kawo karshen duk wani bakinciki da kike tusa min a cikin raina. Ina dalili? Ke kadai tsurarki, kin shige min hanci da kanainaye. Uban me zaki ci da Baqeer? Me ye hadin kifi da kaska?!". Take fada cikin masifa da balbalin tashin hankali. Fuskarta tayi jawur gabadayanta musamman hancinta da take ta hurawa cikin tsiya.

Mutanen unguwa da suka taru ana kokarin raba wannan tashin hankali, suka yi kanta a sukwane lokacin da ta wawuri wane faskaren itace tayi kanta tana gunjin ihu. Wasu suka samu suka janyeta da kyar, ta bugi kyauren gidan da dama jogana shi ake yi. Ya tafi ya fadi can gefe guda.

"Ahhhh!!!".
Ta kara sakin wani ihun cikin tsananin bacin rai.

Hannu ta mikawa Hannabiyya, babu musu ta zura hannu cikin jaka ta ciro wata kwalba, ta mika mata cikin rawar hannu. Ita kanta ta tsorata da Fauza din. Bata taba ganinta cikin wannan hali ba.

Duk wata dauriya ta kau daga kan Ameenatu. Kuka take riris, tun karfinta. Wannan tashin hankali yafi karfin tunaninta.

Fauza ta tsaya a gabanta shelakai, dan siririn kugunta rike cikin hannunta. "Me kike takama da shi ne a duniya? Fari? Kyau? Nasaba? Ko kuwa kudi? Kin san cewa duk na fiki wadannan. Wace tsiya ya gani a jikinki? Wace tsiya gareku? Da har zai ki ni ya zabeki? To yau sai na kawar da wannan banzan kyawun naki da yake fuzgarshi, sai mu ga idan zai iya aurenki a haka. Banza diyar masu sai da gwanjo...!!".

Kafin mutane su ankare, tayi kanta gadan-gadan da kwalbar nan da babu tantama ruwan batiri ne a ciki.

Ameenatu ta kwala ihu tana sakin salati cikin kidima, kafafunta da tun daga lokacin da taga Fauzar suka fara rawa, suka gaza daukarta. Ta tafi gabadayanta ta zube a kasa...!

*RAYYANA!*
Tare da alk'alamin _Sanah Zakariyya

RAYYANA

A firgice Rayyana ta d'aga ido ta kalle shi ta ce "Bukhari kana sanin abin da kake fad'a kuwa? A cikin hankalinka kake sosai ko ka sha wani abun?"

  Ya tako gabanta da kwalbar a hannunsa ya d'aga mata daidai hancinta ya ce "Ras nake Rayyana! Ki yarda ko kada ki yarda, amma dole ne ki binne min wannan kwalbar kamar yadda nace, in ba haka ba kuwa wallahi sai na kashe ki dan baki isa ki shiga tsakanina da cikar burina ba" Ya lalubo hannunta ya saka mata kwalbar ya dam'ke.

  Ta runtse idanunta wadanda suke zubar da hawaye tana kokarin fisge hannunta cikin shessheka ta ce "Wallahi baka isa ba Bukhari! Na kuma rantsewa da Allah burinka ba zai cika ba, koda ka kashe ni haqqina ba zai barka ba binka zai yi ta yi duk inda ka sa qafa.
Na san kana SO na ba zaka iya kashe ni ba"

  "Bari na nuna miki tabbacin zan iya ko ba zan iya ba"

Ya zaro wata sharbebiyar wuqa daga bayansa ya nufi wuyanta.
Tana ja da baya har saida ta dangana da bango jajayen idanunta wanda suka cika da tsora sai kad'awa suke.

"Na san ko a lahira za ki bada labarin son da nake yiwa cikar burina ya wuce wani banzan sonki da na ajiye a banzar zuciyata"

Ya d'aga wuqar ya da6a mata.

Wadannan littafai zaku same su ne a group dinmu na whatsapp, inda za'a fara su ranar 10/01/2020.

Farawa ce wadda babu tsayawa har sai an saukesu da yardar Allah.

Don haka me kuke jira?
Wadanda suke bukata su garzaya su biya kudinsu a,
0152514395 Hassana Zakari Usman gtbank

Masu sayen daya zasu sameshi a naira 200, biyu kuma, 300.

Wadannan littafai babu na yarwa, don haka kada ku bari a baku labari. Sai kun zo!

Domin neman karin bayani, sai a nemi daya daga cikin wadannan lambobi

09039063492
09030312094
07066310865

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 22, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HA'DAKAR FikhraWhere stories live. Discover now