page 16

1.4K 126 26
                                    

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writer's)*

    *SA'A TAFI MANYAN KAYA*g

*BILLY GALADANCHI*

        16
Seda yae nisa sosai sannan yae parking ya soma mayarda numfarfashi sama sama cikin tsananin b'acin rai da bak'in ciki, idan sa sunyi ja sosai, kansa ya sauke akan sitiyarin motar yana mejin wani azababben rad'ad'i a zuciyar sa, yafi 2 hours a wurin kafin ya baiwa kanshi hak'uri ya juya akalar motar sa zuwa cikin gari!!!!!

    Mamakin take irin yanda yake sharara uban gudu akan titin sekace besan ciwon kan saba, kishingid'a tae asaman kujerar motar tana me lumshe idanta, wayarta ta janyo ta shiga laluben number Nasira, bugu biyu ta d'auka

"Siirah?" Shine abinda tace bayan an d'aga wayar, daga d'aya b'angaren ta ansata

"Yadai meye labari?" Shafar giran idanta tae

"Meke damun yaa shammaz ne wai? Ya kamata daddy ya masa magana akan yanda yake tuk'i gaskia sekace bayason kanshi" Murmushi Nasira tae

"Da akwai abinda yake damun sa dai, amma yaa shamm aishi sam baya gudu da mota, idan zamuyi tafiya har bamaso yace ze kaimu, sabida yanda yake lallab'a mota" jinjina kai tayi

"Kinsan har yanzu idan na kirasa baya d'agawa sam" Nsawa Naseerah tae

"Mamita dakin sharesa wlhy, dan yanzu haka fa yaa shaam yayi auren bazata" zabura tayi daga kishingid'an datayi

"Karki gayamun haka Siirah, aure sekace tatsuniyan yara?" B'ata fuska tayi

"Haba mana mamita da gaske wlhy, labarin me tsayine sosai, idan kin samu dama kizo gida" wani yawu ta had'iya kan tace

"Ina kan hanya ma, bari dana shigo zanbi ta gidan ku.

*******
     Diyyah bayan fitarsa anan ta durk'ushe tana gunsheshen kuka tabbas tana cikin musiba, gabaki d'aya abubuwa sun sauya mata arayuwa, batada nutsuwar zuciya akan 'yarta, dama mahaifin 'yar tasani shammaz taimakonta yae amma dukda haka shine silar komai, bazata iya yafe masa ba har abada, ga wannan k'addararren auren da aka k'ak'aba mata.

*washe gari*

     Bashida zab'in daya wuce cika umarnin mommyn sa, wannan ne ya bashi damar sake shirya ya nufi gidan nasu diyya cikeda fargabar abinda yau kuma ze tarar, yarasa abin yi so yake ya rarrashi zuciyar sa ya soma rarrashin ta yana matuk'ar so yaga ta sakko koba komai ita d'in macece kuma me rauni sosai!
    Yauma kamar kullum murtuk tashigo da fuskar nan babu wata walwala, zama kurun tae ta had'e rai batako da niyyan gayar dashi

"Sannu da Gida Nadiya yaya jikin naki" kallon sa tae kamar ta shak'e masa wuya ya mutu takeji, tsabar takaicin dayake bata tagagara furta wata kalma

"Ya komai ina fatan kina lafiya" ya k'ara furta mata cikin murya me taushin gaske, tsaki me tsayi taja masa kantace

"Idanda bana lafiya dabanzo nan ka ganni ba ai, bak'in ciki dakakeso ya kasheni kuma inshaa Allah sesai kai bak'in ciki ya kashe ka badai niba mugu kawai" mamakin kalamanta yake har ranshi

"Ni yanzu Nadiyya ya zanso mtuwar ki kina matayin matana, bana fata Allah karya nunamun, dama nazone zancen tariyar ki" kan tae magana se ganin mommy sukai

"Sabida kana hatsabibin d'an iska da jegon zata tare maka? Kai mata uwar me shashashan banza, ina me gargad'inka akan takurawa yarinyar nan wlhy kamaji na gaya maka ka sakarmun yarinya inba haka ba wlhy sena saka an b'atar dakai, mugu kawai fasik'i" wasu zafafan yawu masu d'aci ya had'iya, lokaci d'aya ya zube k'asa domin gayar da ita

"Barka da gamma mommy" hararasa tae

"Jeka ka nemi uwarka, kome akayi kai d'in nan d'an zina ne, halastaccen jini baya aikata aikin karnukan daka  aikata, inshaa Allahu seka gani akan jinin ka, fyad'e dai dole se an musu" runtse idanshi yae daga duk'en dayake wannan wace irin musiba ce yake cikin ta shi Manure?

"Ke kuma shige muje, in k'ara ganin wannan d'an kwararon yazo kin fito, auren yaci ubansa, badai ina numfashi ba zaki je gidan sa" haka taja hannun 'yarta shi kuwa yafi 30mns kafin yabar gidan cikin tsananin b'acin rai, gidansu ya nufa kai tsaye baze juri wannan mugun zafin ba mara kan gado amma baze iya gayawa mommyn sa ba, besan yaya zata d'auki abunba yasan mata..yana fitowa daga mota mamita yaci karo da ita, ta tabare fuskar nan wane zatayi kuwa

"Yaya Manure" ta furta cikin tsananin tausayin kanta dashi kanshi labarin shi abun tausayi, ko kad'an bataji wai batason saba dan kuwa ya zauna ya gayawa ahalin gidansu komai daya faru na gaskiyar al'amarin, dan haka Naseerah komai ta sanarwa Mamita, zaman kuka tayishi jiyan kuma ta nuna k'aunarta ga jinjirar sosai
Murmishi ya sakar mata cikeda son nuna ba komai dake damunsa

"Yaa Manure kaga yanda kai bak'i wai?, se inta kiranka baka d'agawa sam"

"Banida number ki shisa" ya furta a k'ok'arin sa na barin gun, bin bayan sa tae

"Yaya Manure naga babynka fine girl mashaa Allah" tsayawa yae chak yana kallonta amma beyi magana ba

"Nacewa mommy ta barmun jinjirar amma sam tak'i saurarona, nida babu inda nake zuwa base nake renon ta ba" kawar da kanshi yae daga duban ta yanzu kam

"Yaya zaki ce haka, ai kema kinsan baze yiyu ba, yarinya a hannun kakarta zata zauna" yana gama fad'ar hakan ya kama gabansa, shan gaban nasa tae cikeda hanzari

"Zan gayawa mommyna zan dawo nan gidan da zama, ina dama bataso nake zama acen tace mutane zasuce ni 'yar macece bazasu ganni da daraja ba in dawo nan gidan base yanzu na dawo renon taba, Allah yaya Manure inasan jinjirar har raina" cikin k'osawa yace

"Damuwarki" kanya wuce kurun bayan ya rab'e ta gefen ta ya wuce, idan da sabo ta saba sosai da halayyar sa ta dizgi, ita dai tana sansa,kuma duk rashin sakewar sa inshaa Allah seya aureta.

*********
   *Bayan kwanaki biyar*

Kamar yanda yae alk'ari yabi ragamar sarki zuwa gidansu a k'auyen dasuke wurin mahaifin sa na asali wato Baba ard'o me wake, sunyi rashin sa'a yana gona haka duka zauna jiransa bayan da aka aika akirasa....

Mutuwar tsaye Baba Ard'o yae ganin me martaba sarki me daraja, ya jima sosai suna musayar kallo sarki ma shi yake kallo kan daga bisani ya juya da gudun fanfalak'i zuwa jejin batare daya tsaya sun koda gaisa da sarki bane, cikin dakakkiyar murya sarki yace da fadawansa

"A kawomun shi yanzu yanzu" haka suka dafa masa shammaz gabaki d'aya shida daddynssa kansu ya k'ulle, sarki ma a sarari se Nanata kalmar Malam Ard'o yakeyi yana jinjina kansa...

   Mom Nu'aiym.

SA'A TAFI MANYAN KAYAWhere stories live. Discover now