Epis.. 0+1 =(1)

2.1K 185 12
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

           *RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

    *—•«•Novel series•»•—*
                *{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
               *Be ~ Smart*

*_{Yahoo- smartfeenert@yahoo.com}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS ✍🏻 ASSOCIATION🤝*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://ww.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

      *_Godiya ta tabbata ga Allah [S W A] mai kowa mai komai  da ya bani ikon kammala wancen buk lafiya kuma ya sake bani dama ta sake rubuta wani cikin ikon shi_*
             *Tsira da aminci su kara tabbata a gurin fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammad (S. A. W) Ameen_*

       *JAN HANKALI*
_Wannan littafin ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba dik wanda wannan lbrin ya zo daidai da rayuwarsa ya yi hakuri._
          _Sannan ban yarda ta kowacce tsiga a canza mani taken labari ba, yin hakan laifi ne babba, ina fatan za a kiyaye? Allah ya sa haka Ameen,_

     *—••••«•»••@••«•»••••—*

           *Epi ~ 0+1 =1*

  Wata matashiyar budurwa ce wadda kimanin shekarunta ba za su haurawa Goma sha tara da 'yan watanni ba, ke tsaye a gefen gado cikin shigarta ta mai shirin shiga wanka.

            A hankali ta cira k'afarta ta soma nufar hanyar da za ta sada ta da bathroom, sai dai kafin ta kai kan k'ofar, wani zankad'ed'in kira ya shigo wayarta wanda hakan ya katse kuzarin da take d'auke da shi, ta yi tsaki a hankali ta juyo baya ta nufe wajen mirror wanda a saman shi ne wayar take.

Sai dai wani rashin sa'a kafin ta kawo kan wayar ta tsinke, ta saka hannu ta ɗauka a d'an raunane, ta soma duba sunan wanda ke kiran nata, sai dai ganin Unknow number ya saka ta tab'e d'an k'aramin bakinta ta soma harmar canza akalar tafiyarta wajen abin da take da niyyar aiwatarwa cikin wurgar da wayar a saman lafiyayyen gadonta na alfarma.

Kai tsaye ta samu damar isa cikin bathroom, inda ta na shiga ta haɗa ruwan wankan a cikin baho, sannan ta zage towel ɗin da ke ɗaure a k'irjinta, ta faɗa cikin ruwan ɓatt ta zauna cikin gincirar da kanta a wani gefe da ke kan bahon wankan, ta na mai jin daɗin zamanta cikin ruwan.

       Sai da ta kusan shahe 10mins kafin ta miƙe zaune tare da miƙa hannunta a wani gefe da niyyar ɗauko sabulun wanka.

         Sai dai wani rashin sa'ar da ta sake yi, shi ne; ko kan sabulun hannunta bai kai ga tab'awa ba, Ƙill ta ga an ɗauke wutar nepa da wani matsiyacin k'arfi sai da hantar cikinta ta kad'a.

Nan take duhu ya fara bayyana a cikin bathroom ɗin wanda ta kasa gane asalin kalarta a cikin shi.

A mugun tsorace ta yunƙura da k'arfi za ta tashi tsaye, sai jin ta yi kamar wasu ƙatta majiya k'arfi, sun saka hannayensu a saman kafaɗunta sun daddanne ta wanda ko motsin kirki ta kasa yi.

           Ba ta ankara ba ta ga bathroom ɗin gabaɗai ya turmuƙe da wani mugun bak'in hayaki mai kafurin yajin tsiya, tamkar wajen da aka buga barkonon tsohuwa (ciyagas)

             Nan da nan wani mahaukacin haske jawur tamkar na wutar murhu ya soma bayyana a can nesa da ita, inda daga bisani kuma ya gauraye gabaɗai ilahirin girman bathroom ɗin, har da k'yar take iya janyo numfashinta.

            A rud'e ta soma jin sautin amon wata dak'ik'iyar dariya Kaɗan-kaɗan tamkar ta jarirai, inda kafin ta ida tabbatar da hakan, tuni dariyar ta haifafa ta koma ta tsofaffin mutane barkatai wad'anda ba za ta iya k'ayyade adadin su ba.

          A wahalce ta neme bakin yin ihu ta rasa, sannan dik yanda ta so ta kulle idanuwanta ta yi amma ta kasa.

Inda Jin wani taku ne a bayanta yasa da ƙarfi ta walkaɗar da kanta wajen, sai cin karo ta yi da wata ƴar karamar kwarya cike da jini ana ƙoƙarin dungura mata ita a baki.

            Nan take cikin mugun fita a cikin kogon hayyaci, ta samu nasarar cira hannayenta sama ta daddahe kunnayenta biyu sannan ta samu damar buga wani firgitaccen ihu sai da ko ina ya amsa, inda a take kamar anyi walkiya an janye, ta ga komai ya tsaya cakk cikin dan ƙanƙanen lokaci komai ya dawo daidai, wutar nepar ma ta kawo.

              A rud'e ta fito daga cikin bahon wankan ta ja towel ɗin da ke rataye a muhallinsa da ƙarfi, ta bangaza kofar bathroom ɗin ya buɗe tamkar za ya b'alle, ta nufe tsakar bedroom wanda sai a sannan ta ankara da babu komai sanye a jikinta,  ta walwale towel d'in a hanzarce, ta ɗaura ma jikinta, sannan ta baro part d'inta a guje ta sauko k'asan downstairs, ta nufe hanyar isa main palour inda take tunanin samun mutanen gidan.

           Cikin wata matsananciyar wahala ta samu nasarar isowa tsakar main palour da wani d'an uban gudu, ta na faɗin "Wayyo Mammie za su kashe, sun biyo ni da wuk'ak'e suna neman illatar da rayuwata

              Wani haɗaɗɗen saurayi ne tsaye a gefe wanda shekarunsa ba za su haurawa 27 ba, riƙe yake da kofin tea a hanunsa tare da laptop bag riƙe a ɗayan hannun, wanda alamu suka nuna a uzurce ya ke da barin gadin.

          Cikin tashin hankali ya ajiye cup da laptop bag a saman center table ya tinkaro wajen da take a rud'e, ya rik'o hannunta a hankali cikin son saisaita natsuwarta, ya ke cewa "lafiya Rubina? me ya ke damunki ne?"

          A firgice ta ce "Yaya Rubin mutuwa zanyi! wlhy rayuwata suke son ɗauka!."

            "Oh my god" A maimakon "Innadillahi" ya sake cewa "Rubina kwantar da hankalinki, ki natsu kin ji? Ki gaya man su waye ke son d'aukar rayuwar........." tsayar da zancen ya yi a daidai lokacin da maganar Mammie ke dukan cikin kussayen kunnayen su, wadda ke k'ok'arin fitowa daga cikin kitchen, yayinda yanayin ta kad'ai za ka kalla ka tabbatar da tashin hankalin da ke shimfid'e a fuskarta, ta ce "Me ya ke faruwa ne Rubin?" ta na mai janyo Rubina a jikinta ta rungume ta k'amm a jikinta cikin bubbugar bayanta a hankali.

Inda ita kuma ke matuk'ar lahe a jikin Mammie tana fitar da sautin wani shagwab'ab'b'en kukanta mai kama da na ƙananan yara irin wad'anda ba su gama sakin nono ba.

         Wani zazzafan numfashi Mammie ke saukewa cikin hamdala ga ubangiji ta d'ago fuskar Rubina a sanyaye, ta ce "Me ya ke faruwa ne Daughter?"

Cikin shasshek'ar kuka ta shiga gaya ma su abinda ta gani a cikin bathroom ɗin, Papa dake himmar saukowa k'asa daga saman matattakalen bene, wanda ya gama jin komai a kunnen shi.

Ya ce  "Ki daina tayar da hankalinki a kan wannan Rubina, wannan ba komai ba ne face Horror film d'in da kike yawan kallo, shi ne ke maki gizo, dan haka ki rage kallon horo film kin ji?."

             Cikin matsanancin kuka ta yo wajen Papa ta tsaya tamkar za ta shige jikin shi, ta rik'o hannun shi a hankali, ta ce "Papa seriously is not logging, it's true, I'll see......"

Da hanzari ya katse ta da cewa "Calm down dear, yanzu ki je ki shirya ki fito mu yi break kin ji? daga nan sai mu san abin yi."

             "Amma Papa...." za ta sake yin wata maganar ya sake dakatar da ita, a susuce ta koma dakinta domin shiryawar.

           Yayin da ta b'angaren Rubin kuma ba tare da b'ata lokaci ba, ya dubi agogon da ke tsintsiyar hannunshi ya ga lokaci na ta tafiya yana neman k'ure ma shi, ya dauki laptop bag ɗinshi ya yi sallama da iyayenshi ya kama hanyar shi ta fita main palour'n.

              Mammie da Papa kuma suka halarce wajen dinning table suka zauna zaman jiran lokacin da ta gama shiriritar ta, ta fito sannan su yi breakfast....
Follow me on wattpad and vote.

RUBINA!!!♦️Where stories live. Discover now