Epi~ 7+7 =(14)

614 69 2
                                    

*—••••«•»••@••«•»••••—*

            *RUBINA!!!♦️*
_[Rayuwata suke son ɗauka]_

   *—•«•Novel series•»•—*
              *{SEASON1}*

*Wattpad @Smart_Feenert*
              *Be ~ smart*

*_{🌼Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🥀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🥀*
*—••••«•»••@••«•»••••—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—••••«•»••@••«•»••••—*

    *Epi~ 7+7 =(14)*

     Da k'arfi ya kara bud'e idanuwanshi cikin wani matsanancin firgici domin abinda ya gani ya yi bala'in tsundumar da rayuwarshi cikin wani wahaltaccen yanayi mai had'e da wani gawurtaccen rud'u da fargabar abinda zai biyo baya a wajenshi.

Bai san lokacin da bakinshi ya furta, "Babbar bu...uban nan." Ba.

Cikin rawar murya ya ce "Rubin? da kan ka?" sai dai ganin ko kad'an bai ga alamun sun san da zuwanshi a wajen ba, ya saka shi hira sama ya dira a tsakiyar gadon da suke kwance da kokarin yaye zanen dake lullube a jikinsu.

Cike da wani d'an uban k'arfin hali, ya shiga b'anb'arar Rubin a saman jikinta cikin kwancewar brain, sai dai ko kad'an ya kasa d'aga ko da d'an yatsanshi a sama.

Yayinda cikin wata bak'ar wahala mai had'e da nishin gajiya, ya sauko k'asa a hanzarce ya tsaya daidai kan k'ofa fuskarshi ta yi jawur tamkar attaruhu, in da cikin 2seconds yanayin fatar jikinshi ta soma canza launi........

    ......Bari mu d'an waiwaya baya kad'an."

Lokacin da Ya Rubin ya bar gidan, direct gidan wani babban Abokinsa Ashir ya nufa da ke cikin unguwarsu, kasancewar shi ma abokin nasa tuzuru ne kamar shi, ya sa bai ji nauyin zama a wajenshi ba, tare da kawar da damuwar komai da ke cin zuciyarshi, inda ko kad'an ya kasa nuna wannan damuwar ga abokin na shi kamar yanda ya kasa sanar da shi sirrin da ke cikin zuciyarshi, dik da yana cikin matsanancin tashin hankalin da ba ya da ranar tsayawa, domin a tunaninshi wannan sirri ne na gidansu wanda ba kowa yake da hurumin jin shi ba.

Sai dai ko kad'an tunanin zuwa masallaci a d'aura mashi aure da ita bai shigo zuciyarshi ba, domin shed'an ya riga ya dak'ile wannan hanyar a cikin zuciyar shi.

Sai misalin karfe 10:30pm ya baro gidan, sai dai ya bar motarshi a wajen Abokin nashi da sunan gobe zai zo ya dauka ba tare da ya sanar da shi dalilin da ya sa ya bar motar a wajen shi ba.

    Tin kan ya ida isowa get din gidansu ya kira Baba mai-gadi a waya, ya zo ya wangale mashi get ya shiga.

kai tsaye ta kofar baya ya nufa wadda za ta sada shi da babban palour, kuma ya yi katuwar sa'a domin bai same kowa a palour'n ba wanda hakan ya kara mashi kwarin gwiwar ci gaba da tafiyarshi a hankali har ya kai ga hawa saman benen babu wanda ya samu ganin shi.

     A hanzarce ya nufe part din Rubina, yayinda yana mirda handle d'in kofar ta bude, ya shiga salun-alun, ya ja kofar da kyau yanda ba wanda zai ji karar ta, ya rufe da key sannan ya sonce key din daga jikin kofar ya saka a aljilhun wandonsa sannan ya d'an rage gajiya a saman 3seater da ke cikin palour'n ya ga yanda hali zai yi....

  A Lokacin da ta fito aguje daga cikin bedroom, har wani b'arawon bacci ya d'an fara satarshi, sai dai ihun da ya ji tana yi ne ya tayar da shi

Yayinda ita ma a wannan lokacin da ta shiga wannan yanayin ko kad'an hankalinta bai kai gareshi ba dan ko kad'an ba ta san da kwai mutum a wajen ba.

Cikin hanzari ya mik'e tsaye ya nufe wajen da key din fitilar d'akin yake ya kashe, a daidai lokacin da take juyowa wajen lalaben wayarta ne kuma ya cafke ta...

           *—•~~~~~~•—*

Cikin d'an k'ank'anen lokaci halittar da ke jikin Papa ta rikida izuwa wata mummunar halitta marar kyan gani.

Inda fatar jikinshi ta koma danyen haki sharkaf (Kalar ganye), hannayenshi suka koma kamar kafafuwan karnuka, yayinda a kaifar faratanshi kuma tayi zago-zago tamkar ta birai, fuskarshi dik ta wani yakuce kamar ta tsofaffi mutane 'yan shekara200, idanuwanshi suka koma jawur kamar babu kwayar baki a cikinsu.

Nan take wata k'atuwar riga red color, wadda ke had'e da hullarta, ta fado a saman jikinshi, ta soma sarrafa kanta a jikinshi, yayinda wajen d'aurewa, ta daure da kanta, wajen saka aninai, ta saka da kanta, komai dai ita ke yi kamar yanda ake saka ma sarki alkyabba.

     Sai da komai ya kammala a wajenshi, sannan ya d'aga hannayenshi biyu a sama ya sake wani dan uban ihu, sai da gidan ya wani girgiza da k'arfi tamkar za ya zube k'asa, inda daga bisani kuma, gadon da suke kwance har izuwa wardrobe da mirror da sauran tarkacen kayan dake cikin bedroom d'in dik suka mik'e tsaya tsamgam tamkar abin da aka saka hannu aka d'auka.

  A dai-dai wannan lokacin hankalin Ya Rubin ya dawo daidai, bayan ya gama jin kanshi dumus, wanda kuma ko kad'an bai san abinda ke faruwa a wajensu ba.

A rikice ya shiga duba halin da Rubina ke ciki ganin ta daina motsi, yayinda hankalinshi bai ida kai wa mak'ura wajen tashi ba, sai da ya ga bedsheet din dik ya b'ace da jini.

Cikin firgici ya shiga nanata kalmar "Innalillahi wa'inna Ilaihim raju'un!." Yana kiran sunanta da k'arfin tare da jijjiga gabad'ai ilahirin jikinta.

Yunk'urawa ya yi zai sauka kan gadon, da sauri ya ji kanshi ya tab'o silin.

A razane ya dawo baya ya zauna cikin wani matsanancin tashin hankali, ganin silin na shirin had'ewa da su, inda a hankali ya ji gadon ya soma juyawa da su cikin wata ajujuwa, inda cikin al'ajabi ya d'ora idanuwanshi k'asan gadon, ya ga gabad'ai k'asa ya zurma sosai ya koma kamar rame.

Kafin ya kai ga maida hankalinshi a saman gadon, ya ji Papa ya kece da wata mugunyar dariya mai dauke da alamun takaici, sai da Ya Rubin ya kai ga dwade kunnayensa biyu da hannayesa tare da ambaton sunayen Ubangiji da dik addu'ar da ta fad'o mashi a baki.

Nan da nan ya ga wannan gadon ya fara fecewa da sauri yana juyawa tamkar fankar da aka soma k'ara gudunta, inda kafin wani d'an lokaci tuni juyawar ta soma rinjayar k'arfin halin da yake takama yana da.

Addu'ar da yake yi ma ya ji ya kasa, da kyar ya ji ya soma karanta Ayatul-Kursiyun, da guda-guda cikin dahe kunnayenshi tare da runtse idanuwanshi gam tamkar chewing-gum.

   Wani uban ihu ya ji Papa ya saka sai da ko ina ya sheda, sannan ya ji gadon ya sauko kasa twii da su tamkar abinda aka jefo.

    A hanzarce ya yi karfin halin saukowa k'asa tare da lalabo boxer dinsa ya saka, sannan ya ja bargo ya lullub'e mata jiki, sai dai d'ago kanshi da zai yi ya kalle halin da mahaifin nashi yake ciki kad'ai ke da wuya ya ci karo da wani wazgegen mashi mai bala'in tsinin tsiya, da sai basbasniya yake da wuta (alamun kaifi) ya na kokarin tunkaro wajen da yake.

      Nan take ya ji ya kafe waje guda ko motsin kirki ya kasa yi, cikin mugun sadak'arwa ya runtse idanuwanshi sosai bakinshi ya soma motsi da kalmar shahada.....
Dan Allah kuyi manage da wannan, wlhy yau sai a hankali wutar nepar, Editing a kwai wahala sosai.
Follow me on wattpad and vote.

RUBINA!!!♦️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora