MATAR DATTIJO page 9

1.7K 86 1
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Zahra musa*

9

kwanan shi biyu bai xo gidan mu ba saboda kunya sai dai mu yi magana da shi ta waya, amma duk abubuwan da nake bukata yana aiko yaron shi ya kawo min, a wasu lokutan ma innah ke dakatar da shi saboda hidimar tayi yawa.

A lokacin da aka yi mana hutun makaranta yaxo gidan mu, a soro ya tsaya ya aiko yaro ya kira ni, saboda har yanxu yana jin nauyin hada ido da innah saboda tonon asirin da nayi masa.

cikin nutsuwa yaron ya shigo tare da sallama, gaba daya muka amsa masa mayar da hankalin mu muka yi gare shi,  muna sauraron abinda xai fada mana, a ladabce yake mana magana.

wani dattijo ne yace yana sallama da Niimatullah, inna ce ta dauki mayafi ta fita, yana ganinta ya xube a kasa yana gaidata, cikin sakin fuska take masa magana. me yasa ka tsaya a nan Alhaji? ka shigo ciki Niimatullah din tana nan. sunkuyar da kansa yayi, nan ma ya isa innah ai ba dadewa xan yi ba,  takura masa ta shiga yi, a'a Alhaji baxa a yi haka ba, kwala min kira tayi da sauri naxo wajen, kallon shi nayi ba tare da na gaida shi ba, innah ce ta dube ni karbi kayan da ke hannunsa mana, cikin ladabi na karbi kayan.

biyo ni yayi a baya har muka shiga daki, ajiye kayan nayi a gabansa xan fita, cikin marairacewa ya kira sunana, Niimatullah ina xuwa? a hankali na juyo na bashi amsa wajen innata xan koma, cikin rarrashi yake min magana haba babyna ina xaki tafi ki bar marayanki wanda bai san komai ba sai soyayyar ki domin na ganki fa naxo gidan nan.

turo baki nayi ni baxan dawo ba, salon naxo ka rika dankoni kamar wata yar tsana, cikin sigar tsokana ya bani amsa ai yar tsanar ce, mikewa yayi yana shirin kamo ni da gudu na fita wajen innah ina haki, ina xuwa na xube a kasa ina kuka, ni Allah innah na gaji da halin mutumin nan Kullum ba shi da aiki sai son ya kamoni, ni wlh na gaji innah.

shiru tayi tana kallona ta kasa bani amsa sai jinjina kai kawai take yi, da yaji shiru ba nida niyyar dawowa ne yasa ya fito yaxo wajen mu,  ajiye ledar kayan yayi a gaban innah godiya ta shiga yi masa bisa ga dawainiyar da yake yi mana, cike da girmamawa yake wa innah magana ai wajibina ne na kula da ku.

ni kuwa sai hararasa nake yi a raina ina cewa dube shi sai kace mutumin arxiki, kansa a sunkuye yake wa innah magana.

innata dan Allah idan babu damuwa ina neman wata alfarma a wajen ku, hankalinta ta bashi sannan tace, ina saurarenka Alhaji ai babu abinda xaka nema bamu yi maka ba indai muna da hali, yaji dadin abinda innah ta fada masa don haka ya saki ransa ya fara yi mata bayani.

dama so nake ku bani aron Niimatullah xa tayi min rakiya Abuja, na nemi matata ta raka ni to abubuwa sun mata yawa, ni kuma bana so nayi tafiya ni kadai, gabana ne ya fadi nan da nan na fara kuka.

ni wlh baxan bishi ba innah tabdi,  duka ta kai min, me yasa kike haka ne Niimatullah ansa da ke ne da xaki sa mana baki, Alhaji dai mijinki ne tunda ya bukaci ya tafi da ke ba mu da ikon hana shi, ke ma kuma dole kiyi biyayya ga mijinki. kallon shi rayi, bari na yiwa malam magana nasan shi ma baxai hana ba.

tashi tayi ta shiga dakin baba ta sanar da shi yadda suka yi da mijina, gaba daya suka taho inda muke, fada suka rika yi min sosai, dukan su bada damar na bi shi, ina kuka suka dakko kayana kala uku suka xuba min a leda, cikin kulawa yake wa su innah magana a mayar da kayan nata xan siya mata wasu a hanya.

kuka nake kamar raina xai fiti ta bakina, har bakin mota su innah suka rako ni ina ta xabga ihu. bayan mun tafi suka koma cikin gida innah ce ta dubi baba.

malam ni fa ina fargabar tafiyar yarinyar nan kada taje ta samu rabo saboda alamu sun nuna wannan mutumin yana da bukata da yawa, kada ciki ya fito kafin aje ko'ina, ajiyar xuciya baba yayi nima dai haka nake tunani hankalina xai fi kwanciya idan aka yi bikin nan ko menene ma yayi a dakin matarsa, amma ni baxan ji dadi ya rika xuwa yana daukar mana yarinya ba yana yawo da ita a gari kawai don an daura musu aure.

Har muka kusa xuwa inda xamu je na kasa yin shiru ashe ba wani Abuja da xan raka shi karya ya shararawa su innah.

A yi hakuri da wannan wlh ba nida lafiya yanxu ma karfin hali nayi na baku wannnan don kada ku ji shiru

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now