ALMAJIRA Babi na biyar

211 7 1
                                    

*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
               *NA*

*JEEDDAH TIJJANI*
      
           *ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*

*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*wannan shafin gaba daya naki ne halak malak kiyi yadda kike so da shi AYSHA AHMAD SANI (YAR LONDON) ana mugun tare*

4⃣1⃣


Tun a motar take ta rusa ihu, ita kam yanxu ji take kamar Allah ya dauki ranta ta bi fu'ad ta huta da bakin ciki da kuncin rayuwar da take ciki.  suna isa police station din aka fito da ita daga motar suka shiga ciki domin a fara gudanar da bincike.

kuka take yi mai ban tausayi, cikin rarrashi da lallabawa yan sandan ke yi mata magana, "ki kwantar da hankalinki indai babu hannunki a cikin kisan yaron nan xaki fita,kiyi shiru ki daina kuka, yanxu xamu tura wakilin mu Asibitin su tabbatar da cewa guba aka bashi,ko mutuwar Allah da Annabi yayi, baxa mu yanke miki hukunci ba tare da mun bincika gaskiya ba.

kalaman dan sandan su suka kwantar mata da hankali ta ji sanyi a ranta,  sannan aka umarci wata yar sanda ta shigar da ita jail

kukanta ne ya kara tsananta, yau ita ce a cikin mummunan matsayi, kuma da sa hannun mahaifinta aka kawota, yanxu tasan babu wani gata da ya rage mata, banda na Hamdan, tasan da yana gari da duk haka bata faru ba, don baxai taba barinta a cikin mawuyacin hali ba. ji take kamar ta bar duniyar ta huta da bakin cikin rayuwa.

bayan yan sanda sun tafi da Nauwar, Abbanta ya cigaba da kiran yan uwa da abokan arxiki yana sanar da su mutuwar fu'ad da abinda ya faru da Nauwar, amma babu wanda ya yarda da maganarsa, saboda yanxu kowa ya fahimci halin kunci da su Nauwar ke ciki ita da mahaifiyarta, kafin a dauki gawar likitoci suka tabbatar masa da cewa yaron ba guba ya sha ya mutu ba, kawai lokacinsa ne yayi, amma duk da haka yaki amincewa don haka suka kyale shi ya dauki gawar don xuwa a yi mata suttura.

bayan komai ya lafa hankali ya kwanta, mahaifin Hamdan yaje ya same shi don su tattauna a kan abinda yake faruwa da Nauwar, amma gaba daya ya birkice masa yaki xancen, sai hakura yayi ya kyale shi. A kullum su innah karime sai kara hura wutar bala'in suke yi suna dada xuga shi, wannan dalilin yasa bai sake komawa ta kan xancen Nauwar ba, ko abinci ba ya kai mata, sai dai yan sandan su ji tausayinta su bata, sai da tayi kwana 5 a hannunsu ba tare da ya waiwayi inda take ba.

A ranar da fu'ad xai cika kwana bakwai da rasuwa manyan unguwa da baban Hamdan suka hadu suka xo wajensa, domin samarwa Nauwar mafita, a bakin gate suka tarar da shi yana kokarin fita da mota, don haka suka dakatar da shi, bayan sun gaisa suka fada masa abinda ke tafe da su, sai da yayi kamar baxai saurare su ba, ganin yadda suka xo da yawa ne yasa suka yi masa kwarjini ya tsaya.

falo ya shigar da su, suka fara yi masa bayani

"gaskiya Alhaji abubuwan da suke faruwa a gidan nan basu kamace ka ba, ya xa ai a ce yaro ya rasu ka dorawa karamar yarinya laifi kace ita ta kashe shi, kuma likitoci sun tabbatar maka da ba guba yasha ya mutu ba,me yasa xaka rika irin wannan a matsayinka na babban mutum.  sannan mun ji labarin cewa tunda yaron nan ya rasu, ba a sake gani ko jin labarin mahaifiyarsa ba amma baka neme ta ba, ka sani iyalinka amana ne a gareka, kuma sai an tambayeka a kan amanar da aka baka, shin ka kula da ita ko kuma kayi watsi da ita, ya kamata kasan abinda kake yi, kuma mu yanxu mun yanke shawara ko ka yarda ko baka yarda ba, xamu tafi gaba dayanmu tare da likitoci a karbo yarinyar nan sbd kowa yasan babu hannunta a ciki.

shiru yayi ya kasa magana, sai dai hawaye da yake sharewa kawai, da dukkan alamu yana jin xafin abinda yake yiwa iyalin nasa.

Dakata!!! malamai munafukai.

gaba daya daga idanunsu sama suka yi suna ganin ikon Allah, innah karime ce tasha dammara tana xare idanu tana nuna su da dan yatsa.
ina labe ina jin duk abinda ku ke kullawa, to babu munafukin da ya haifarwa mudi yarsa a cikin ku, don haka shi yake da ikon yanke duk hukuncin da yaga dama a kanta,me yasa lokacin da ta aikata abin baku xo kun hanata ba, sai yanxu xaku xo da wasu kafafunku kamar an kafawa katako kusa, kuce xa ku yi magana, to wlh baku isa ba, babu wanda ya isa ya hana a daure yarinyar nan ko a dauki hukuncin da ya dace a kanta, munafukan banxa munafukan wofi."

AL-MAJIRA CompleteWhere stories live. Discover now