5 & 6

3.1K 54 1
                                    

_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_



             _IN BETWEEN THE LOVE_
            ❤ _Lies another love_❤


            _✍🏿M Shakur_

                        5️⃣ & 6️⃣

_how to pay your subscription fee_
_*zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*for those da prefer su tura kati, you can also send MTN card na 300 ta WhatsApp number na 07012181461 saina loda nasaki a group din danake posting ATSAKANKANIN SOYAYYA_



_Free page_

Sallame salla Ammi tayi
sake kwalamata kira akaro na uku tayi. "Aneesa wai bazaki tashiba, idan kika bari nazo dakin nan sai jikinki yay tsami, kindaisan abubuwan dake gabanki yau ko" da kyar ta iya bude ido jin Ammi na masifa tana kiranta jiya taci aiki a shago bana wasaba saisa tagaji haka, dama duk jumma'a haka take uban aiki a shago dan masu zuwa party nazuwa placing order dayawa kuma duksaitayi, da kyar ta sauko daga gado har bata gani da kyau tana dafa bango tafito daga dakin tafito Ammi tabita da kallo tai tsakar gida bayi ta shiga dan lokacin har gari yasoma wayewa fitowa tayi tadauro alwala takoma daki tadau hijabi ta sanya, akusada Ammi ta tsaya ta kabbarta salla, data idar tai karatun Al qur'ani sanna ta sallame ta gaida Ammi ahankali, amsawa Ammi tayi tace "tashi kije kidaura ruwa a wuta" gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta zare hijabin jikinta tafito daga dakin tai kitchen wuta ta kunna ta daura pot din ruwan wanka dake cikeda ruwa tadau tsintsiya ta share tsakar gidan fess sanan ta shiga dakin dakin Ammi ta tattaro ta gyara sanan tawuce nata dakin ta gyaro shima tahada da falo ta gyara tafito da dattin ta kwashe, tadawo ta kunna turaren wuta sanan tafito tasauke ruwan daya soma shirin tausa daga wuta ta daura dumamen tuwo tahada ruwa ta shiga bayi, wanka tayi tana fitowa ta sauke tuwon dayayi tasa miya sanan tai dakinta, mai kawai tashafa tadau doguwan riganta na gida baki ta zura tafito lokacin wajen 8 nasafe ta zuba abincin ta dan tasan Ammi bata breakfast early tadawo ciki ta zauna kusada Ammi tafara cin tuwon dayay dadi miyan harda wake aciki, ahankali takeci harta cinye sanan ta kai kwanon kicin ta wanke hanun ta ta dauraye baki tadawo ta zauna kusa da Ammi, da hannu Ammi tanuna mata dakinta tace "daukomin purse dina" tashi tayi tai hanyar dakin Ammi tafito rikeda wata bakar purse ta zauna kusa da Ammi tamika mata karba tayi tabude purse din ta ciro kudaden dake ciki wanda suke na Aneesan na lallen datakeyi take tara mata dubu biyarne Ammi tamika mata tace "kije kisiyo kayan lallen, sanan kisiyo handglove banson yanda kike bata hanunki haka, kiyi sauri kidawo dan nasan anjima kadan yan lallen zasu fara zuwa yau asabar kina gida" karban kudin tayi tana kallon agogon bangon dakin ganin Takwas da rabine yanzu yasa tace "karfe tara kasuwan lallin ke budewa, Ammi ki faramin tsifan kafin lokacin" tai maganan tana zare hulan kanta tulin kitson kanta datai shuku na hannu yawani zubo har gadon baya, hulan data cire Ammi ta daura ta mayar mata tace "sokike kije kasuwa dakai daya da rabi, aga nan yay kato nan yay kadan, Tara zaki fita yanzu takwas darabi minti talatin yayma kitson nan kadan, yanzu jeki fara shiryawa ne, kafin kigama shirin lokaci yayi" kaman zatai kuka ta tashi tai hanyar dakinta, sip dinta tabude tadauko wani gogaggen atamparta riga da skirt dakeda dilli dillin ja, sai ta dauko jan hijabin ta dayakai mata har guiwa ta maida sip din tarufe tacire rigan jikinta ta shiga shiryawa, riga da skirt din yay mata kyau sosai gaban madubinta taje ta shafa hodanta tadau man baki tashafa a lips din sai abin yay kaman tasa pink lipstick, dawowa tayi tadau hijabin tasaka daya kwanta a fuskarta tadau karaman jakanta tafito, baki Ammi ta tabe tace "kasuwan aka cima kwalliya haka yan mata kodai nai siriki ne akasuwan"  akunyace tace "laaaaa Ammi" dariya tadanyi ta dauke kai cikeda kunya tadau kudin dake gefen Ammi tace "nifa hoda kawai na shafa Ammi" tura kudin tayi cikin jaka tayi har lokacin taki kallon Ammi tace "natafi Ammi" "adawo lpy, ki adduan fita daga gidafa, kuma adaga kafa kar aje ana yauki akasuwa hmmm"  Ammi tafada cikeda zolaya, murmushi sosai tayi tasa hijabi tace "to, Ammi idan yan lalle sunzo kice sujirani bazan dadeba" "shikenan, saikin dawo, kiyi addu'an fita daga gida" ficewa tayi daga dakin tai addu'a tafita daga gidan.





ATSAKANIN SOYAYYA (In Between the Love) Where stories live. Discover now