chapter 8

333 26 2
                                    

Bismillahirrahmani-rrahim

Tunda Nawal ta dawo daga asibiti Zain ke haba-haba da ita yanajin fargaba dayawa dabesan meye dalilin hakan ba saidai yana musu fatan alkhairi. Da har ya d'auki fushi da Nawal akan abinda ta b'oye mishi daga baya ya haqura sbd ya fuskanci in yana damuwa ta fishi shiga damuwar

Amma fa babu abinda takeyi da kanta koda gyran gado ne masu aiki biyu yace a samo amma har yanzun ko dayama ba'a samuba

************
Wani aiki ya kai Zain kogi state, ni ka'dai nake zaune agidan daurewa kawai nake sbd ban saba zama ni ka'dai ba ko agida. Amman tunda sati daya zaiyi babu damuwa

Misalin sha biyu na rana megadi ya sanar dani nayi baqo nace ya masa iso, koda ya shigo ba sai ancemin d'an uwan Zain bane saboda yadda suke kama abayansa wata yarinya ce da shekarunta basu wuce sha biyar ba bana ganin fuskarta sosai sbd mayafin riga da wandon dake jikinta ya rufe fiye da rabin fuskar ta

A qasa ta zauna inda ya zauna a kujera, ni nafara gaisheshi ya amsa da faraa yaqara da cewa mijinki yace in sanar dashi inna sameki lafiya yanata kiran wayarki......da sauri na tashi na dubo wayata missed calls ensa lodi aciki

Na danna kiransa"kina lafiya kuwa nace karka damu ina lafiya wayar na ajiye a nesa na manta ina gyangyadi shiyasa, ko ba'a fa'da ba yarinyar nan ni take kallo inajin haka ajikina

Anan Zain yamin bayanin me ya kawosu yace wannan shine Ahmad" he is my cousin brother, ammafa duk wadda aka samo kiyi haquri da ita sbd samun me aiki yafi samun aiki wahala a garinnan sai na dawo take good care of yourself and our baby kinji? Kiss yamin jin na kasa mayar masa yasashi dariyar mugunta yasan da su Ahmed a gurin nace bashi ka ɗauka nayi masa sallama ina dariyar nima cikeda sonsa da missing ɗinsa. Bayan munyi sallama dashi muka qara gaisawa da Ahmad

Daga nan ya waiwaiya yace mata buɗe fuskarki mana. Jikina ne yafara rawa ganin irin kyau da tsarin da Allah yayi wa wannan yarinyar ko ita akace tayi kanta iya abinda zatayi kenan

Komi nata yafita dukkan kuma abinda kukasan ana kira kyau to ta gama haɗashi she's a real definition of beauty nace a raina,sai kuma nan da nan naji na tsaneta sbd yarensu daya da mahaifiyar Zain gashi yana matuqar son duk abinda ya shafi mahaifiyar shi nan da nan launin fuskata ya canza, Ahmad ya fahimci hakan

Yayi saurin cewa matar aure ce dakike ganinta bansan sanda nayi ajiyar zuciya ba har ta fito fili

To amma me ya kawota nan kuma ma aikatau. Nazo neman mijina ne sai alokacin tayi magana hausarta bata fita sosai amma zaqin muryarta saida ya ratsani

Kuma banida masauki, kinajin turanci?eh tace nace to ina ganin zefi mana sauqi yin magana ko? Kai kawai ta gya'da alamun eh

Mun tattauna duk abinda ya kamata ta amince nima haka

Nace saura sharadi na guda daya "me kenan?" Koda wasa karki sake hanya ta ha'da ki da mijina dara-daran idanunta ta d'ago tana kallona kamar mejin tsoron abinda na fa'da

Kinji zancen danake? A sanyaye ta d'aga kai alamun to sai kawai hakan ya qular dani nace cewa nayi inkina son zama dani karki ta'ba bari ku ha'du da me gidan nan, da sauri wannan karon tace I'll do exactly as you said. Nace welcome to my house uhmm...
What's your name?

N.. ni...n......" Nanna Ahmad yayi saurin qarasa mata na fuskanci ya b'oye mata suna sai kawai na zaci sunan natane wani iri sbd Indians en nan harda me sunan aljannu

**********

Zan iya cewa banta'ba ganin yarinya hard worker irin Nanna ba babu qiwa babu son jiki uwa uba kuma ga tsafta akwana ukun nan saida gaba dayan gidan nan ta canza masa fasali da tsabar gyara

Cikin mamaki nake kallon ta inda ta kalleni tayi murmushi nace in tambayeki? ta rusuna tace tohm nace mace kamar ke meya kaiki auren wanda besan darajarki ba. Shiru tayi alamun tambayar ta mata yawa

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now