💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*16.
Daki na koma nayi dakin yah meenah na sameta tashin ta kenan,tana mik'a da salati.
Murmushi nayi mata ina hayewa gadon nace,"Morning my dear."
Hararata tayi kafin ta sauka daga gadon tana cewa,
"Mai kukan banza kawai,wallahi saboda kuka wataran sai kin makance rab'o kawai."
Dariya nayi don yadda ta dage sai hararata take tana fad'a,
"Kinyi dariya mana ni kinga shigata wanka,kinsandai yau muke fara attending lectures ko."Kwanciya nayi ina jan bargo tare da cewa,
"Wallahi yah meenah ko bature bazai nuna maki biting time ba,kiga fa kwata 2 eight muda keda lectures ten thirty."Ta na daga cikin barth room din tagama wankeshi tana hada ruwan wanka tace,
"Kanki akeji don wallahi bazan ringa let ba,dana gama inhar baki tashiba saidai kisaman can,don na lura nawarki is too much wlh."Dariya nayi nashige bargo don sanyi akeyi kwanan kamar kamarme.
Dandanan bacci yayi gaba dani don dama idon sai lumshewa yake saboda tsabar baccin dake cina.**********
Areef ne da jahid suna wajen exercise dinsu,don wajene keb'entacce wanda aka k'awatashi da abubuwan more rayuwa,babuce babu awajen Abbune yafito zaiwuce ya hangi k'ofar wajen abude,yafasa shiga ya cewa driver yasaka mashi jikarshi baya yana dawowa.
Shiga yayi ya samesu duk sunyi gumi,jahid na kan machine din gudu Areef na gefe yana kan na keke......hira suke jefi jefi saida yagama kallesu sannan yayi gyaran murya,duk juyowa sukai suka kallo wajen...........da sauri areef ya sauko daga inda yake ya iso inda Abbun yake,ya dan rugumeshi yana cewa.
"Good morning Abbu."D'agoshi yayi yace,
"Morning."
Jahid ma yazo ya rungumeshi ya gaidashi,don wannan salon tun suna yara sukeyinshi kuma Abbun ne ya koyar dasu hakan,don yanajin dadin jin yaransa ga jiki,Allah kadai yasan irin son da yake masu.Duk suna zaune kasa shi yana tsaye,
"Ya kamata dai kamar yanzu kunfara zuwa office,ai kun huta haka nan ko."Areef ya langab'ar dakai zaiyyi shagwabar da ya saba,Abbu yace.
"Karkace komi,sarkin son jiki kaikuwa wata macen ma tafika jarumta,don haka banason korafi idan na dawo am talking about that issue OK."Duk suka ce yes Abbu tare suka fito suka rakoshi har mota,Areef ya bude mashi baya yashiga sannan yarufe,daga mashi hannu sukai har yafita...........
Komawa sukai suka cigaba d aikinsu,Jahid yace."Don Allah bakaji kunya ba."
Kallon haushi yayi mashi yace,
"Kunya! For what."Jinjina kai yayi yaci gaba da abunda yake,saida yadauki lokaci sannan yace,
"Ka wulakanta bukatarsa jiya sannan yanxu ko kunyar had'a ido dashi bakayi,meyasa akullum baka damuwa da damuwar wani sai taka,wallahi Areef ur Always selfishness gay ka gyara wannan ba rayuwa bane."Ran Areef yayi masifar b'aci ko kallon da yake ma jahid kad'ai zai tabbatar maka da hakan,cikin muryarsa data zama so deef yace,
"Duk Akan wannan yarinyar kake gaya mun magana yadda ranka yaso ko jahid,to bari kaji wani abu wallahi kalma guda da kake fadan marar dadi akan wannan vellege girl din karajin tsanarta nake cikin zuciyata,don haka ba zance ka daina ba plss continue."

YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Romancelove story labari kan tsantsagoron soyayya sa hakuri,juriya da cin amana karku bari labari