💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always 💔_✍🏿M Shakur_
2️⃣
Bude kofan dakinsu da gudu tayi ta shiga tasaka sakata da sauri Lubabatu dake kwance tana danne dannen awaya tace "kekuma dawa zaki shigowa mutane daki da gudu haka?" hannu Zeenah tasa abaki alamun tai shiru kar Mummy tajisu hakan yasa Lubabatu tai shiru tana kallonta, ihun auta dukansu sukaji ta kwalama Mummy su kira tana kuka sosai atare dukansu suka fashe da dariya Lubabatu ta taso daga kan gadon da sauri tazo wajen da Zeenah ke tsaye tana dariya tace "me kika mata makira eh?" wani irin murmushi Zeenah tayi kafin tace "wanan Black Cameroon pepper dinan na container na juyemata duka a abincin aiko taci shine take kukan nan gobema takara zama bayan tasan hanyan kitchen asa nakai mata abinci saina samata wanda yafi wanan" takara kwashewa dawani dariyan, shiru Lubabatu tayi tana kallonta cikin jin haushi tace "haba Zeenah ai duka kuma yay yawa kema kinsan koni bana iyacin Black pepper nan fadanshi yay yawa balle ita dabama tason yaji ko kadan inda tata ta za'abi da karma ai girki da attarugu just tomato and onion, inama laifin 1 spoon koshi ya isa yakoya mata lesson kika juye duka kinsan awa nawa zatayi tanajin yajin kuwa?" maganan Luba yasa Zeenah itama duk taji wani irin badadi zatayi magana sukaji muryan Mummy tana ihu tace "wlh, wlh kashekine kawai bazanyi ba yau Zeenatu inna kama ki, muje Auta" takama hannun Autan dake kuka sosai tabude dakinta suka shiga ciki dakine hadadden gaske komi tsaf yana kamshin turaren wuta, zaunar da ita tayi akan gado tace "zauna ina zuwa bari na kawo miki gishiri da ruwa yajin zai tafi stop crying" gyadama Mummy kai tayi tana hura baki tana kuka Mummy tajuya tafita da sauri daga dakin tai kitchen dinsu taje ta dauko salt da ruwa a fridge tahado mata da yogurt tadawo, gishiri da ruwa tabata da sauri ta karba tasha sosai tana kuka idanunta sunyi ja kaman wacce akama shegen duka, karban goran ruwan Mummy tayi ganin tana neman shanye duka ta ijiye tace "ya isa kekuma zaki fasa cikinki da ruwane? Karbi yogurt dinan kisha yajin zai tafi duka I promise" karban yogurt din tayi tana sauke ajiyan zuciyan kuka ta shiga sha itakuma Mummy ta juya ta ijiye ruwan kan side drawer gadon sanan tadawo ta zauna gefenta akan gadon, ahankali Rahima ta janye Yogurt din daga bakinta ta ijiye tawani matso jikin Mummy tadaura fuskarta kan kafadan Mummy tai lamo jikinta nadan bari, cikin wani irin murya na mugun shagwaba tace "Mummy kibani abun please, yau baki baniba at all, am feeling hungry" daga kanta Mummy tayi da sauri daga kan kafadarta tana kallon yanda tayi kaman mara lapiya tace "kindai san babanku na garin nan ko, kuma kinsan baya bacci batare daya ganku dukaba, ki rufamin asiri kibari yay tafiya yacemin kwana uku zaiyi, gobe ko jibi zai tafi kibari inya tafi saina baki kinji" fashewa da kuka tayi sosai tana makema Mummy kafada tana goge hawaye da bayan hannunta, dan tsaki Mummy tayi cikeda gajiya da shegen rigiman banzan Rahima tace "ohh My God, Ke wlh kincika matsala Auta, nace kibari babanki yatafi ko kin wagemin baki kina kuka" kara kara karfin kukan nata tayi tana kallon Mummy tana ihu da sauri Mummy tace "to naji yishiru, yishiru lemme think, ki bari nai tunani to" shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya tana kallon Mummy nata, hannu Mummy ta daura kan goshi tana tunani, kafin chan tabude ido ta kalleta murmushi ta sakinmata tace "shikenan to naji zan baki but saida daddare, kinga anama kiran sallan la'asar yanzu any moment from now babanku zai shigo, kibari idan zamu kwanta saina baki, yanzu tashi jeki cire towel dinan kisaka kaya babanku yahanaki zama da towel haka" dan turo baki tayi ta tashi tafita daga dakin tana tafiya ahankali Mummy tabita da kallo harta bace mata, dakinta tawuce ta tsallake barin shinkafan datayi tahau kan gado abinta, jakan makarantan ta tabude taciro wayarta Samsung mai kyau ta bude data tana dube duben message, fita tayi ta shiga game tafara bugawa, shima fita tayi ta jefar da wayan kan gado babu abinda kemata dadi, littafan ta taciro na school ta shiga dubawa suma babu wanda ke mata dadi hakan yasa ta watsar dasu akasa ta kifa kanta kan gadon tana nishi sama sama kaman mai asma tana bubbuga kafafun ta akan gado kanta nawani irin sarawa sai lashe bakinta take tana bubbude wa kaman wacce kejin kishi, bude kofanta da akayi yasa tabude idanuwanta dasuka kankance Lubabatu ce ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta babu alamun wasa kan fuskarta tace "Malama kitashi kije ankira sallan la'asar nasan ma kona azahar bakiyiba kiwuce kije kiyi, kin daisan Abba yace mudinga kiranki idan zamuyi salla ko to kitashi" harara tawani irin watsa mata kafin takara gyara kwanciya kan gadon kifa kanta kan gadon tace "Malama kitashin mini agaban kofan daki tunda ba dakinki bane" daga bakin kofan Lubabatu tace "okay bazakiyi sallan bako bari nahadaki da Mummy" tsaki Auta tayi tace "anan dukanku kukafi auki gulmammun babbunan banza kawai" "Mummy, Mummyyy" Lubabatu ta kwalama Maman su kira, fitowa Mummy tayi ta tsaya daga bakin kofanta tana kallon Lubabatun, cikin tsananin jin haushi Mummy tace "wai menene matsalan ku da yarinyar nan eh, Zeenatu tasamata yaji a abinci kekuma mai kika biyota yanzu kimata, kasheta zakiyi?" cikin jin haushi Lubabatu tace "Mummy nifa ko dakin ta banma shigaba fa, kiranta nayi tazo muyi sallan la'asar" cikin fushi Mummy tace "to bazatayi ba kubarta inta gama hutawa zatayi Allahu Gafurur Raheem, wuce kibace daganan wurin munafukan yara sun tasa yar kanwarsu agaba wlh Allah zai saka mata" kallon dakin Luba tayi auta tamata gwalo tana kyalkyacewa da dariyan iskanci da sauri Lubabatu tawuce tana kunkuni tace "kiyita lalata ta yarinya bata salla kona asuba da kyar takeyi" da sauri Mummy tace "dani kike magana ciki ciki?" dakinsu ta shiga batare datace komiba, komawa dakinta Mummy tayi ta shiga bayi alwala ta dauro sanan tai sallan la'asar tafito dakin Autan ta leka ganin ta lumshe ido yasa tadauka bacci take tawuce dakinsu, ahankali tabude dakin dawani irin gudu Zeenatu tai bayinsu ta garkame kofan kwafa Mummy tayi tace "ai wlh saina rama mata, ba yanzu zamu haduba Zeenah" ta kalli Siddiqa dake kan dadduma tana kallonta tace "harya tafi Sadiq din?" gyadamata kai tayi, tabe baki tayi tace "shine bakizo kin fadamin ba, anyway kutashi dukanku kuje ku daura abincin dare, Luba tashi kije dakin auta ki sharo min shinkafan data zubar akasa kifito da komi waje" wani kallo Siddiqa tama maman nasu kafin ahankali tace "Mummy yanzu fisabilillahi ya zaki saka taje ta sharo abincin da kanwarta ta zubar ba dole su dingajin haushin autaba in aka kuma tabata kidinga masifa, ita autan batada hannu ne, bata iya aiki bane? Mummy gaskiya abinda kikeyi baida kyau wlh kina nuna sonk......." yowa kanta da Mummy tayi yasa tai shiru Mummy ta nunata da yatsa tace "ina baki girman ki amatsayin ki na yayansu baki kama kanki ko, wlh duk randa kika karamin magana haka I will not mind muna gaban kanninki ne saina kikkifa miki mari wlh, kitashi kiwuce kitchen kuhada dinner babanku yakusan dawowa" tashi Siddiqa tayi cikin bakin ciki sosai ta zare hijabin jikinta tafice daga dakin kaman zata tashi sama fuu, itama Luba tashi tayi Mummy tabita da harara tace "kindaiji aikin danasaki kiwuce ki dauko tsintsiya kije ki kwashe abincin daya bare inkin gama saiki wuce kitchen kuyi girkin" sanan ta kalli bayin tace "wlh Zeenah inna dawo dakin nan nasame ki abayi baki wuce kitchen kun daura abinci ba saina kakkaryaki dako ubanki inya dawo bazai ganeki ba" tana maganan tawuce tafita daga dakin.
Agaban dakin Autan ta tsaya tana kallon yanda Lubabatu ke tattare shinkafan Auta kuma na wasa da wayanta tana shishila kafa ko lura ma da Mummy batayiba. "Auta na" jin muryan Mummy yasa da sauri ta dago kanta, murmushi tayi ta sauko daga gadon da sauri tana gyara daurin towel din jikinta ashagwabe tace "Mummy na nazo yanzu?" Tsaki Lubabatu dake shara tayi ta cigaba da aikinta, ahankali Mummy tace "a'a anjima, me zakici yanzu dan bakici komiba, su dafa miki Indomie ne?" yatsine fuska tayi tareda girgiza kai dan batada apatite ahankali tace "a'a, banajin yunwa yanzu Mummy" murmushi Mummy tamata tace "to kwanta kicigaba da hutawa abinki" gyadama Mummy kai tayi tana murmushi tai kwanciyan ta tana hararan Lubabatu da gefen ido tana murguda mata baki, kallon Luba Mummy tayi tace "dau sharan kifita me kuma kikeyi?" daukan pakan tayi tafita daga dakin Mummy tarufo kofan tawuce tai dakinta.

YOU ARE READING
CHASING THE HEART CRAVINGS (BIN ABINDA ZUCIYA KESO)
RomanceA girl that do drugs and a Soja that fight drugs, kakakara kaka.