Ina masoyana suke ku firfito ku marmatso kuji...
Amma kafin nan bari mu kammala karatuCikin falourn sarah ta zauna tana mai jin kanta na juyawa, sarah tai serving dinta drinks, zainab a ranta kuwa sam ba wadannan ne a gabanta ba,
Wata takarda ta zaro ta miqa mata, zainab ta karba tana son ganin mene cikin takardar dan zuciyarta na fada mata sakon faruq ne, tai hanzari budewa sanann ta soma karantawa cikin ranta
"Assalamu alaikum warahmatullah zainab dina
By the time da zakiyi receiving wanan papern im already gone, so far, yes zainab, amma banaso kiyi tunanin hakan na nupin wae karshen soyayyarmu ne yazo, ko kadan wannan ne ma mafarin soyayyarmu, inda hali ki jirani zainab ina nan zan dawo, in shaa Allah zan kiraki, i will definitely call"
Zainab ta sake karanta takardar cikin rashin fahimta, sae ta dago ta kalli sarah, ina faruq yaje? Meyasa bemin sallama ba? Ya akayi ya bar wannan takardar a hannunki?
Sarah ta kalli zainab cikin tsanaki tace " faruq yaje gurin malamin ku (levelcoordinator) right,
Zainab ta gyada kai yes
"B.u.k sunyi withdrawing dinshi from the department, accusing him of examination malpractice" zee ta miqe
"Sarah are u drunk, are u okay? Kinsan me kike fada man kuwa, faruq dinne yayi exam malpractice? How comes?" Sarah tayi sighing "zauna kiji, zee ta zauna kwakwalwarta na kokarin fassara mata abinda sarah ke fada ko zata yarda amma ina,
"Nidae shi ne kawae abinda na sani gameda wanan if you need more info u can contact your levelcord" zee tayi baya ta jingina kanta a jikin kujerar tana jin juwa, sarah ta dakko wayarta ta miqa mata, zee ta amsa tana maida idanunta kan pictures din,
Ta dan mirje idanuwanta ganin wani almara a cikin wayar, "what the heck" ta fada on top of her voice,
Ta kalli sarah idanunta tap da hawaye, meye haka sarah?" Sarah bata samu courage na kallan idanunta ba ta dan sunkui da kai, hakane zainab wanann shi ne babban dalilin dayasa faruq ya tapi beyi miki ko sallama ba, saboda ya kare mutuncinki ne, saboda yana qaunarki fiyeda yanda yake qaunar kanshi,
Hawayen suka gangaro daga idanunta ta saka hannu ta rufe bakinta tana mai cigaba da kuka zuciyarta na pounding, ta dade tana wannan kuka me qaramin sauti, ta jima tana shatatar hawaye, dan kanta ta lallashi kanta bawae dan kukan ya isheta ba sae dan tana buqatar komawa kebantaccen guri tayishi son rantaA maimakon ta koma gida sai ta wuce school, ko sau daya ka kalleta sai kasan tayi kuka, idanunta sunyi luhu luhu, still tana tafiyar hawaye na zuba time to time, saedae ta saka bayan hannunta ta sharce, direct office din levelcord ta wuce amma se bata sameshi ba, ta fito ta koma bin titin, duk inda ta waiga cikin school din sae ya tuna mata da faruq, hakan kan kara ingiza kukan nata, can bayan school ta samu kasan wata bishiya, gurin tsit yake dan kamar daji ne saedae wucewar motoci kawae zaka na ji,
Ta tsugunna kasan wata bishiya ta sunkuyar da kanta cikin raunin zuciya hawayenta ke diga kan tafin hannunta, What a mysterious life, ko a mafarki jiya i yanxu bazata ce faruq ze tapi ya barta ba cikin kankanin lokaci haka, ta ciro wayarta tana sliding pictures din, me hakan ke nupi, meyasa sarah zatace sune dalilin tapiyar faruq?,Bata samu amsarta ba se kurawa pictures din ido da tayi, shot hudu ne kuma sun dauku tarr koyaya imdae kasan zainab zakasan ita da faruq ne cikin hotunan a wani yanayi... Zee tana tuna sanda abin ya faru, lokacin da aka gama hidimar bikinsu zakiyya, taje gidanshi ta taddashi cikin mawuyacin hali, har tayi kokarin taimaka mishi
Bari mu dan koma baya kadan
From episode 34:"Ta karasa bakin gadon da sauri ta zauna tana kallanshi, idanunshi a lumshe suke ya budesu a hankali yana kallanta,
Ya kara haske akan wanda tasanshi, labbanshi sun bushe fuskarshi ta rame, idanunshi sunyi ciki kamar wanda yayi jinya ta watanni,
Muryarshi ce ta ja hankalinta
Ta dan kara tauri da karfi yace "taimakamin na zauna, batayi wani tunani ba ta riko kafadarshi kusan gabadayanshi a kirjinta yake, (first shot) ta taimaka mishi ya zauna sannan itama ta zauna gefenshi, (another shot) tari ne ya rikeshi, wanda har saida idonshi ya fidda ruwa sannan ya sauka
Itama taji nata idon ya kawo ruwa amma ta hadiye kukanta, kai kana kallan faruq zakasan yana jin jiki,
Da muryar tashi da ta sake rashin dadi yace "nerh nerh ya gida? Ya hiddima?" Ta gyada mishi kai kurun
Mene ya sameka? Kuma bazaka iya kirana ba, kaje asibiti ne?"
Ya lumshe ido tarin ya sake yi sannan yace "mura ce kawai sai ciwon kai, na kira wannan doctorn na momy yazo ya dubani har ya bani magunguna kuma masu aikina na kulawa dani ba wani abin damuwa"
A kufule ta dubeshi "har ni zaka cema babu wani abin damuwa"
Yayi shiru yana kallanta a kasalance bece komai ba, sannan yace ki jirani a falour zan shiga bandaki
Tace to, ya miqe dakyar kamar iska zata kadeshi ya fadi, jallabiya ce jikinshi, sai lokacin ta lura ramar ma har jikinshi ne,
Ganin yana tangadi kamar dan maye, yasa ta zuba mishi ido cikin tausayawa, kasa yayi luuuu
Saukinta a tsaye take ta tafi da sauri ta riko kugunshi (3rd shot)
Dukansu sai suka zube a kasa, gyalen nata ma ya riga yayi nashi guri, (last shot) numfashinshi takeji gaba dayaa fuskarta da kirjinta shine yayi saurin tashi a kanta sannan itama ta miqe"......Karashen maganarsu da sarah ta soma tariyowa "zee tace "amma meyasa hotunan suka zama dalilin tafiyarshi, in ze tapi ma kuma meze hanashi yimin sallama" sarah tace "nidae i dont know much abinda yace min shi ne "sarah ki fadawa nana zainab dina, ko zan bada rai na fansa bazan bari a taba mutuncinta ba, haka kuma makircinsu baze sakani rabuwa da soyayyarta ba"
Wani tinani ne yazo kanta "kenan su ya halisa sunyi amfani da wannan pictures sukayi manupulating faruq har ya tapi ya barni, meyasa soyayyarmu ta tsaya musu a rai har haka, nikam mene nayi musu a rayuwa da basa son tarayyata da faruq"
Kwanakin zainaab biyu tana zazzabi harda amai da matsanacin ciwon kai, sam taqi zuwa ganin likita, tana dai shan magunguna kuma tana ayyukanta na gida amma sam bata zuwa school, kuma koyaushe tana daki, dayake anty bata wani damu ba itama tana ta hidimar lil saghir yasa bata lura ba,
Tana kwance a daki wayarta tayi ringing, tasa hannu da ciro ta a chargi dan tun ranar da sukai magana da sarah tai watsi da wayarta dama babu chargi se ta mutu, se dazu ta tuna ta saka ta a chargin,
Sallama tai da wata irin murya mai kauri alamun bata da lpia, anty hawwer ta amsa tana tmbyar lpia zainab, ina kika shiga inata neman wayarki tun jiya, zainab ta lumshe ido
A hankali hawaye mai zapi ya biyo kuncinta ta hadiyi yawu mai daci, Anty haww.... Bata qarasa ida furta sunan antyn ba kukan ya kwace mata, bata cire wayar a kunnenta ba kuma bata fasa kukan ba,
Anty hawwer kuma bata ce mata komai ba, kuka take tana ajiyar zuciya da shan majina duk lokaci guda,
Sai kuma ta soma mata bayani cikin kukan "faruq ya tapi ya barni, sun sakashi tapiya bada son ranshi ba Anty, sai kuma ta soma warware mata abinda ke faruwa tun daga last call dinsu dayace mata zeje gurin levelcord, her anniversary suprise, yadda sukai da sarah kashegarin ranar, har zuwa yadda takeji yanxu,
Anty zuciya ta zapi takemin, nagaji nagaji Anty, Ammi ta tapi, Abbah ma ya tapi yanxu kuma faruq ne, shima ya tapi Anty nasan kuma baze dawo ba,Anty ta katse ta "wane yacemiki baze dawo ba, inace cikin takardar har cewa yayi ze kiraki ya akayi kika kwallafa ranki kan faruq har haka, yanxu ki tashi kiyi wanka zan kira zeena tazo ta rakaki asibiti, banason wannan zaman dayan da kike, kina nupin bazaki karbi kaddara bane ke kam a rayuwa, kina kokarin butulcewa ubangiji, haba mana zee"
Ta share hawayen ta gabadaya rayuwar babu dadi "maza ki tashi kinji" ta gyada kai tohm ta sake goge hawaye "kuma banason wannan kukan kinyi kuka kuma ya isa haka, kina da abubuwan yi da hawayenki, zee tace to bawae dan hawayen sun dena zuba ba
Yadda anty tace hakan tayi ta tashi ta nemi ruwan dumi cikin heater ta gasa jikinta tun daga kai zuwa tafin kafarta ta saki shower, sanan ta cuda jikin nata kadan dan babu wani kwari,
Tana fitowa taga kiran zeena ta dauka jiki a sanyaye "gani nan tafe kinji sannu" tace to, mintunan da basu gaza 15 ba zeena tayi sallama a falour, Anty siyama dake fitowa a kitchen ta amsa mata suka gaisa sannan tace zee din tana daki, zeena ta wuce dakin ta tadda ta zaune karshen gado ta rungume jikinta, zeena ta karasa ta dafata, zee ta daga ido ta dubeta tana mai kokarin kada hawayenta su zubo, zeena batace mata komai ba ta miqe ta dau hijab ta saka suka fice a gidan, bayan sunma anty sallamaMabiya kuma masoya Al_hubb
Wannan dama ce tazo da dumbin masoya zasu nunamin kauna, yau ina neman alfarma a gurinku karku watsamin kasa a ido, zanji dadi idan kuka karfafamin guiwa 🙏🏻
Please ku biyoni a shafi na na instagram @Ayshabnaseer
Karku karanta ku wuce inma searching zeyi wuya ga link nanhttps://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3
Pls surprise me, inaso ku bani mamaki na tashi na tadda followers bila adadin, yadda ban gajiyawa gurin typing dan following dai nasan kuma bazaku dauke kai ba,
Show me love😥
Surprise me
Nima se na cigaba da baku mamaki wajen typing❤
I will love to see my true fans💝

ESTÁS LEYENDO
AL_HUBB💞 (THE LOVE)💔
Romance"To love is to suffer... To avoid suffering one must not love.... But then one suffers from not loving... Therefore to love is to suffer...not to love is to suffer... To suffer is to suffer.." "To be happy is to love.... To be happy, then, is to suf...