Part 1

71 5 0
                                    

☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘

       *SAKAYYAR MU CE!*



--------✍🏻 story writing

     📖🖊
       by
  *Sumayya salihu*
         *👑 Queen Sumy ce*




🌈KAINUWA WRITERS ✍🏻 ASSOCIATOIN

{υnιтed ωe ѕтαndα αnd ѕυcceede; oυr αмвιтιon ιѕ тo enтerтαιn & мoтιvαтe тнe мιnd oғ reαderѕ}
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation



*page* 1⃣ to 2⃣


🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊HAPPY SALLAH ! HAPPY SALLAH !! HAPPY SALLAH !!! TO MY FANS😍

WANNAN GORON SALLAH NE GABADAYA MASOYA NA !!!
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊

*بسم الله الر حمن الر حيم*

*Da sunan Allah subuhanahu wa ta'ala da ya bani ikon rubuta wannan littafi, kuma shi ne na farko, ban yi wannan littafin ba dan in ci zarafin wata ko wani wannan kagen labari ne mai cike da tausayi ban mamaki da kuma nadama da tsantsan mugunta uwa uba soyayya akwai ilimantarwa a ciki da kuma nishadantarwa, ina rokon Allah Ya kare hannuna da tunanina da alkalamina da rubuta shashan abin da ba shi da amfani, Allah kuskuren da ke ciki Allah yafe muna, abu wanda yake da amfani ka bamu ikon aiki da shi ameen ya rabbil alamin👏🏻*

*ALL MY FANS*

Godiya gare ku masoya da fatan za ku bani hadin kai sosai sosai idan nayi posting kuke comment ta yanda zan ji dadin yi muku typing mai yawa domin jin dadinku,



*Dedicated*
aunty muhibba ina kaunarki irin sosai nan allah ya barmu tare my little mom

📖readers......ku biyo ni dan jin yadda shirin yake.........📱


💠💠💠💠💠💠

*FUSKARSA* baƙa ce  wulik, sanye yake da  riga da wando na suit komai nasa baƙi ne, idanuwansa jajir tamkar gaushi haƙoransa duk sun fito waje.

       Da gudu yake binta a cikin wani jeji me mahaukacin duhu, ko tafin hannunka ba ka gani, se faman ihu take amma ina ba wanda zai taimake ta.

tana cikin gudu ne ta yi arba da wani katon rami me mugun zurfi a gabanta, da sauri ta juyo dan tagani ko yana nan, juyowar da za ta yi ne ta ga ya ɗaga wuƙa yana neman caka mata ita.

       Wata irin ƙara ta yi lokaci guda ta afka ramin.

GA ALLAH MUKA DOGARA KUMA GA ALLAH ZA MU KOMA!

  shi ta faɗa, ta yi wani irin firgigit ta farka da baccin da take, zumbur ta tashi zaune se waige²  take, dan tayi matuƙar razana da wannan mafarkin da tayi, kallon inda  ta kwanta  ta yi a ƙasa ne, kan ƙasa a tsakar gidansu,

gidan ya yi haske, hasken farin wata daren goma sha biyar ne garin ya ɗau sanyi kasancewar lokacin sanyi ne.

     tunani take yi wai me yasa ta kwanta anan?, wannan tambayar  ce tayiwa kanta, lokaci guda ta mike tsaye, lokacin ne ta tuna da dukan da inna jummai ta yi mata ɗazu da magriba ta dubi jikinta se taga duk ya farfashe hannunta ne ta ji yana mata zogi, tayi saurin duban ɗayan hannun gani ta yi duk hannun ya yi jini har jinin ya fara bushewa.

"innalillahi wa'inna ilaihir rajiun"wannan kalmar ce ta faɗa, gami da xubo kwallar da ta cika mata ido ta sa hannu ta goge hawayen.

          shin wai suma na yi ko kuma bacci ne nayi?, ta tambayi kanta amma ba amsa. Sauri ta yi ta shiga madafarsu ta dauko  ɗan buhun da take kwanciya, ta shinfiɗa a ƙasa cikin farin watan, dakin inna jummai ta duba ta ga alamun ta rufe shi, ga shi kuma ɗan tsumman zanin da take rufa yana cikin ɗakin.

  haka ta kwanta kan buhun ga shi tana jin sanyi duk ta duƙunƙune  guri ɗaya,ta nemi bacci a idonta ta rasa, tufka da warwara take yi tana cikin tunanin ne ta tuna da bata siyo man da za'a soya ƙosai ba gobe nan da nan hankalin ta ya yi mugun tashi, jikinta har rawa yake da sauri ta tashi zaune tana faɗin.

  "na shiga uku na lalace se na ci duka a gun inna wayyo Allah na shiga uku ya zan yi da rayuwata?"

wani irin kuka ya kwace mata yau ya zan yi? ga shi kuma dare ya yi bare in je in siyo mata.

Tsaye ta miƙe ta yi saurin nufar ƙofar inna jummai da niyyar ta tambaye ta ko an siyo man.

Har za ta ta6a ƙofar kuma se ta tsaya kamar me tunani,
ina tambaye ta ko in bari har goben idan Allah ya kai mu,budewar ƙofar  ne ya dakatar  mata da tunani ta.

guri ɗaya ta maƙe tana kallon inna jummai, sautin muryarta ne taji tana cewa cikin masifa.

  "kee! shegiya uban me kikeyi anan ƙofar ɗakin ? mayya cinyeni zakiyi ko? mai baƙin hali wacce batayi gadon halin kwarai ba munafuka zo  nan" inna jummai ta jawo ta da ƙarfi cikin tsawa da masifa se ji kake tass ta wanka mata mari a fuska tare dayi mata dungu a baya d'iiimm!.

ba ta san lokacin da ta yi wata Ƙara ba "wayyo inna kiyi hakuri ki tausaya min wlh ba zan ƙara ba dan Allah"

"yi min shiru" tasa hannu ta toshe mata baki,tana cewa "munafuka so kike ki tona min asiri a maƙota su ji ina dukan ki ko eyyee".

     BASMA ta girgiza kai alamar a'a.

inna jummai ta ce " maza ki wuce can zaure ki kwanta yau a can zaki kwana dn ubanki kuma ki jira wani dukan shashashar yarinya kawai."

  Basma sai hawaye ke fita a idon ta ga shi duk jikinta zogi   yake mata ko ina na jikinta ciwo yake ga sanyi tana ji sosai.

A hankali take tafiya cikin sanyin jiki....


ku ci gaba da biyoni...

whatspp no.
08104986525

plx commet and share

    *TAKU CE 👑 QUEEN SUMY*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 07, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAKAYYAR MU CE!Where stories live. Discover now