Page 4

117 16 0
                                    



Page 4
***********************************

"Sailuba ce zaune a dan tsakar gidan nasu data share shi tsab ko ina yayi kal dashi.
dalhatu ya fito daga cikin dakinsa dauke da rigarsa ta jar shadda a hannu sai faman washe baki yakeyi yana murna kai kace kyautar wasu kudi ya samu.
Tabe baki tayi kawai ta dauke kanta zuwa gefe guda..
Dalhatu na zura rigar tasa a jikinsa ya kallota yana cewa..
Yadai sailuba ko kina da sakone a kasuwar?kinsan fa yau take laraba yau zamuje cin kasuwar tsauri!
Sailuba ta kalleshi cike da takaici..
Kafin tace..
Ni bani da wani sako,kawai kayi lafiyarka..
Dalhatu yayi dariya..
Ki saki ranki yarinya,kinsan dai ba kumbura ba ko fashewa zakiyi umma da abba bazasu taba barin ki ki shiga kasuwar tsauri ba...
Sailuba ta kallo sa tana jin wani irin takaici a cikin zuciyarta..duk budurwar dake garinsu tana zuwa cin kasuwa,suyi siyayyar su ta yan mata abunsu.
Ita ko Wacce irin rayuwa ce wannan takeyi ? ace wai tun tana yar shekara goma sha biyu bata taba saka kafa ta fita daga cikins gidan su ba idan har ba ya zamo tilas bane(rashin lfy)
Wai sbd kawai tana auren wani DAN SARKI  can wanda bata taba ganin sa,bata san ya yake ba,bata san halin sa ba,bata san ko ya san da ita ba ma, kasancewar aurensu da iyayen su suka daura tun basu san ciwon kansu baa
Tsaki taja mai ciwo..kafin nan tace,
Na sani yaya dalhatu nasan da cewa ni matar aure ce!da iyayenmu suke yiwa kulle!
Dalhatu yadan tausaya wa kanwar tasa dan shi kam bai ga amfanin wannan auren da akayiwa sailuba ba.yadan washe baki yace, ki kwantar da hankalinki ke da ma naji ance a  watan nan zaki tare a MASARAUTAR SHIMLA....
Yadan duka kasa cike da zolaya yana cewa..
ALLAH yaja zamanin ki gimbiya SAILUBA ranki ya dade matar yarima!
Wata muguwar harara ta watsa masa kafin ta mike ta shige cikin daki tana fashewa da kuka mai tsuma rai..
Kuka sosai tasha kamar kullum,dan ma umma bata gidan nasu ta shiga gidan makotane tasan da sai taci mutumcinta kullum take irin wannan kukan haka umman ke rufeta  da fada.
Tsaki taja tana mikewa tsaye..
Inaa bazai taba yiwuwa ba dolene taje kasuwar nan itama taji dadin rayuwar ta,kamar yarda tasan shima wannan dan sarkin yana can yana wolewar sa...

"SULAIMANU ya kalli magajiya a tsananin mamaki cike da gamsuwa da bayanin da ta gama yi masa..
Ta jinjina kai tana cewa..
Ai yanzu dai, sai ka yarda da wannan zancen tunda gashi yarinyar nan da kanta ta fada maka wanda yayi sanadiyyar yi mata fyaden.
Umma uwani a wannan lkcn ta gama cika fam dan kuwa ta gano inda maganar magajiya take Zuwa,wato dai dan ta Zaidu take son hadawa da mahaifin sa..shi yasa take kokarin daura masa wannan kazamin kazafin.
Kallon baiwarta tayi da idanuwanta da suka soma kankancewa..sbd tsatsanin bakin ciki.
Kasa kasa tayi mgnr...tace
Salame maza kije sashen yarima zaidu kiyi min kiransa,salame ta mike cikin hanzarinta ta fice daga cikin falon dan aiwatar da umurnin uwar dakin nata.

Waye YARIMA Zaidu?
Yarima zaidu Da ne ga sarki sulaimanu da gimbiya fauziya,saurayi ne kyakkyawa mai ji da kansa,yarima zaidu dogo ne mai jikin karfafan maza,ba fari bane sannan kuma ba zaka kira sa da baki ba sai dai ace masa ruwan tarwada(chocolate) fuskarsa na dauke da idanuwa kanana da dogon hanci da kuma lebe mai dan fadi, ba karamin kama yake da mahaifiyarsa ba dan komai nata ya dauko.
Yarima zaidu na da farin jini sosai ga mutanen masarautar shimla,dan kuwa yana da fara'a sosai da kula jama'a,sam bashi da wani ji dakai bare kuma kasaita,mutum ne da bashi da hayaniya ko kadan.
A halin yanzu ma yana can filin wasan doki  ne yana kilisa da bawansa JAMILU wanda sam bazaka taba cewa bawa ne da uban gidan sa ba dan kuwa ba karamin sakewa yakeyi da jamilu ba ya dauke sa tamkar abokin sa kuma amininsa tunda a tare suka taso,duk wani sirri na yarima Zaidu toh jamilu ya sanshi.
Tunda ga nesa na hango salame ta taho kamar zata tashi sama,sauri kawai take bugawa har tana hadawa da gudu gudu dan tafi kowa sanin halin da uwar dakin ta take ciki.
Lkcn data karaso wajen da suke jamilu ne yayi saurin saukowa daga kan nasa dokin ya tare ta da saurinsa.
Umma salame naji ya kira ta dashi..kafin cike da mamakin ganin ta yace,
Lafiya kika zo har nan da fatan dai babu wata matsalar ?
Salame bata ko kalle shi ba ta juya zuwa ga zaidu dake kokarin saukowa daga kan nasa dokin,kafin ta karasa kusa dashi ta dan duka kasa tana fadin.
Allah ya kara maka yawan rai gimbiya uwani wato mahaifiyarka ce take neman ka cikin gaggawa a sashen mai martaba.
Zaidu ya lumshe ido yana sakin murmushinsa irin na kullum yace,toh salame kije gamu nan karasowa yanzun nan.
Ta gyada kai ta juya ta fice tana kallon jamilu daya bi ta da kallo dan kuwa baiji abunda ta fada wa yariman ba ko kadan.
Zaidu be  ya kalli jamilu a takaice yace ,kira bayi su mayar da dawakan nan zamu wuce sashen mai martaba ne yanzu,jamilu yace toh zanka ya dade cikin saurin sa ya shiga kiran bayin dake tsaye kusa dasu.

Tafiya sukeyi cike da nutsuwa,duk inda suka wuce bayi ne suke zamewa kasa suna kwasar gaisuwar daga wajen yarima zaidu dan albarka ,shi kuwa fuskar nan kamar gonar auduga sai zuba murmushi yakeyi yana amsar gaisuwar tasu cike da sakewa babu wani girman kai a tattare dashi,

Wani sashe dake can kusa da sashen na sarki suka zo wucewa,jamilu ya kalli zaidu da murya kasa kasa yace dashi,yallabai dazu nake jin wani lbr a wajen bayi wai yarima Tafida ya sake barin masarautar nan yayi wata fitar sirrin kamar yarda ya saba.
Ko ina yake zuwa Allah masanin gaibu.
Zaidu  ya daga kafada bai ce komai ba har suka iso sashen na mai martaba,jamilu ya samu waje ya tsaya kusa da fadawan dake wajen,shi kuwa zaidu sallama ne yayi masa iso ya shige ciki cike da mamakin kiran da ummansa ke masa a cikin sashen na sarki.

A zazzaune ya tarar dasu gaba daya sun saka mai martaba a tsakiya ,ya samu waje a gefen umman tasa ya zauna cike da ladabi ya gaisar da mahaifin nasa,mai martaba ya amsa masa muryar sa na cike da bacin rai da kuma fusata.yace,
Amma zaidu ka bani kunya !
Ban taba tsanmanin zaka aikawa wannan barnar ba kana matsayin Da na.
Zaidu cike da mamakin furucin mahaifin nasa yace,
Allah ya karawa mai mai martaba tsawon rai,kayi min afuwa duk da bansan menene laifin da ake tuhuma ta da aikatawa ba,yana fadar haka ya dukar da kai kasa.
Mai martaba ya kalle sa da idon basira yace, dazun ne wani lbr yake yazo min wai kayi wa wata yarinyar baiwa fyade!
Ni na rasa wannan jaraba indai har auren nan kuke so abune mai sauki a wajena sai nayi muku na huta da wannan abun kunyar da kuke son jajibo min!
Magajiya dake jin dadin fadan da mai martaba keyi wa zaidu. ta gyara zamanta tana sauke lumfashi ganin tayi kokarin wajen rufawa dan ta tilo asiri,da yanzu shi ne mai martaba zaya hukunta..
Zaidu  ya dafe kirji cike da tsantsar mamaki da fargaba yace,wlh bani da masaniya akan wannan sharrin da akeyi min,magajiya tayi saurin cewa sharri kace fa?yarinyar da a gaban kowa tace kai ne kayi mata!
Zaidu  gaba daya ya rikice ya shiga neman afuwar mahaifinsa hade da kokarin fahimtar dashi kazafi ne akayi masa bashi da masaniyar abunda ake tuhumar sa dashi.
Mai martaba ya kallesu duka yace ku tashi ku tafi gaba daya ransa ya bace sosai..umma uwani ta mike da sauri ta kamo hannun danta sukayi waje,magajiya ta kalli mai martaba rai a bace ganin bai dauki wani mataki akan alamarin  ba.zatayi mgn ya daga mata hannu kawai ya mike ya shige uwar dakinsa.

Jakadiya ce dake daga waje  ta fado ciki da sallama,magajiya dake ta cika tana batsewa ta kalleta tana fadin,kin duba sashin nasa?
Jakadiya ta gyada kai naje ranki ya dade amma bayin dake aiki a ciki sunce yau kwana biyu kenan yarima tafida baya nan,magajiya ta mike da sauri cikin tashin hankali tace,shifa barde(bawan sa) yana ina?jakadiya tace, na aika wani bawa yayi min kiran sa dan ance baya gari ya fita  kai sakon mai martaba wajen waziri.
Magajiya gaba daya ranta ya sake baci,ta mike a fusace ta fice daga sashen.
Tana koma wa nata sashen ta yi kiran baiwar ta wato hansai.
Kina jina hansai?talatu tace ina jinki uwar dakina.magajiya ta nesa tace,so nake ki saka wani bawa amintaccen mu ya fita neman yarima.ko a ina yake ace dashi ina masa neman gaggawa. Hansai ta jinjina kai tace an gama ranki ya dade

Ku biyo niiiiiii

Gimbiya sailuba Where stories live. Discover now