Black Monday

1.2K 120 3
                                    

BAHAUSHIYA𖣘︎

 

   😭𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢💔

𝙆𝙖𝙘𝙤𝙠𝙖𝙣 𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙎𝙖𝙙𝙖𝙪𝙠𝙖𝙧𝙬𝙖 𝙘𝙚!
𝙕𝙖𝙞𝙣𝙖𝙗 𝘼𝙗𝙙𝙪𝙡𝙡𝙖𝙝𝙞 𝙒𝙖𝙯𝙞𝙧𝙞! 𝙈𝙖𝙢𝙖𝙣𝙖🥰
𝙈𝙖𝙝𝙖𝙞𝙛𝙞𝙮𝙖𝙩𝙖 𝙩𝙖 𝙠𝙖𝙞𝙣𝙖! 𝙄𝙣𝙖 𝙩𝙨𝙖𝙮𝙚 𝙣𝙚 𝙨𝙖𝙗𝙞𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙧𝙛𝙞𝙣 𝘼𝙙𝙙𝙪'𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙧𝙖𝙣𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙠𝙞𝙠𝙖 𝙝𝙖𝙞𝙛𝙚  𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙧 𝙕𝙪𝙬𝙖 𝙔𝙖𝙪😘🥰😍, 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖 𝙜𝙖𝙛𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙢𝙞𝙠𝙞 𝙙𝙖 𝙍𝙖𝙝𝙖𝙢𝙖!🥰😍

Black Monday.

  Babi-takwas

       Shiru yayi yana nazarin can ya tattara ya watsar sannan yayi wucewar shi inda angwaye suke, yana isa gurin cikin fara'a Dr Aahil wanda ya sha manyan kaya, irin na Dr Bature, ya mika mishi hannu suka gaisa.

                 Wasu tawagane suka zo wucewa, kan Dr Bature a sunkuye ji yayi ana busa algaita lafiya Moddibo Usman Abubakar! Lafiya toron Giwa dan Abubakar. Na gaida Uban Abubakar.

     Koda ya d'ago sun wuce, murmushi yayi sannan ya kalli Dr Aahil cikin raha yace.
"Gaskiya ina son culture dinku na Hausawa, kamar yadda akaiwa wancan mutumin ya burgeni."

    Cikin jin dadi Dr Aahil ya bude baki zai magana akayi shelar an daura Auren Dr Aahil Aliyu Maitama tare da A'isha Ahmad Sodangi...

      Kura mishi Ido Dr yayi cikin tausayin Husnah. Ganin yadda A.A ke murna dama haka Musulmai sukewa junar su, Amma me yasa?! selfish.

    Tabbas son zuciya ya sanya Dr Aahil ya cutar da innocent lady, da bata ji ba, bata gani ba yayi destroy rayuwarta into hell.

    Ganin yadda kowa ke taya shi murna shima ya mik'a mishi hannu daga nan suka dunguma zuwa liyyafa wanda aka shirya a Center hall.

    Gurin yayi kyau, duk abinda ake yi, Dr Bature yana kallon su har suka gama.

     Ranar bai koma gida ba sai ƙarfe biyar yana shiga gidan ya tadda ita, kauda kai yayi cikin sauri ya nufi step yana hada bibiyu.
        Dan haɗu yarinyar ta haɗu, matsalar shi baya yinta ne baki d'aya.
         Kallon Daniel tayi, kamar zata yi kuka tace.
"Kana ganin ya share ni?!"

         "Mr Arrogant! Ne fa, Devanah ga Joel da yake sonki me yasa ba zaki amince ba".

    Murmushi tayi tana kallon Joel, akwai mabanbanta halayyar da ya raba Dr Bature da Joel, Dr mutum ne me kamun kai, ko taba ba yasha, balle wine.

     And secondly Dr baya niman mata amma shi yanayi. Sun isheka."

    Mik'ewa tayi tabi bayan shi, tana zuwa yaji kofar a rufe, tsaki tayi ta cigaba da bugawa.
  
Kuma shima yasan da haka, zata iya shigo mishi, that's why ya rufe kofar.
         Sai da ya shirya tsaf sannan ya zo ya bude sanin cewa zata ya rungume shi.
   Shi yasa sai ya rungume kofar yayi Banga banga.

        "Excuse Mr Arrogant!"
    Murmushi yayi, sannan yace.
"Ok Miss Funny zan shirya tukun"
  Ya rufe kofar, abin shi kwanciyarshi yayi cikin jin dadi ya manta da ita.

   Tabbas yasan Devanah tana masifar son shi, amma Allah ya gani baya sonta, baki daya a rayuwarsa. Bawai bata yi bane, tayi iya wuya shine dai bata mishi ba. Kuma da Babanta da Mommah cikin su daya.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now