NUNA SO GABAN KISHIYA❣️
wattpad:UMMIEN2018
whatsapp number:09076427357*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment and to educate and enlight our readers)_*page 11
Cikin murmishi takaraso tayi hugging na ummie cike da farin cikin ganinta... ummie ma tayi kewar yar uwarta haka sukayi ta murna kayansu kaman wanda sukayi shekaru basu hadu bayan a lokacin aurensu ma anisa taje ta...
tare suka shiga kitchen sukayi dinner abinsu inda suke ta hirar yaushe gamo... bayan anyi dinner sun dan taba hira goggo ta wuce turakar mai gidanta inda ta shaida masa duk abubuwan dasuka faru...
shima baiji dadi ba yayi ta fada sosai ba kadan ba... haka dai suka jajanta abin...asuba tagari goggo amina...!
bangarensu su ummie na daki suka wuce bayan fiddousi kuma tana parlo tazauna tana karatunta sbd jarabawar dazasu fara ta waec...
saida sukayi wanka suka shirya cikin sleeping dress nasu bayan sun kashe haske waya sukabi lafiyar gado suka dulmiya hirar rayuwa inda anisa ke tambayar ummie zuwanta na lafiya ne kuwa...?
Nan ummie tabata labarin duk abinda yafaru tundaga farko aurenta da ameer da abinda suka shuka mata har kawo yau dinnan datake bata labari...
takarasa maganar cikin kukan tausayin kanta...
hmmm ummie kenan kin manta mai na ta6a fada maki a baya ne...?
ummie har daukan hannu kikayi kika mare ni akan na fada maki gsky amma gashi yanxu kin ga abinda nake fada maki da idanunki na tabbata yanxu kin fuskanci da wacce kike tare kou...?
Haka ne anii amma wlhy ban taba tunanin cewa a rayuwa mimi zata aykata haka a gareni ba ballanta ya ameer da shakuwarmu ta wuce misali...
Ni dama tun lokacin da aka daura aurenki da ameer danaga kalan kallon da mimi ke maki nasa ba a banza ba... amma dana maki magana akan hakan kika rufe ido kikace sam mimi bazata maki haka ba...
karshenta ma da maganar ta tsawaita a tsakaninmu kika sauke man yatsunki biyar bisa fuska ta sbd na fada maki gsky......
nidama tun baya dakika taba fadaman kina son ameer nace banga alamun sonki cikin kwayar idanunsa ba amma kika musani wai kin tabbatar wata rana zaisoki... gashi kuwa kinga yasoki din ay... anisa takara she maganarta fuska a hade...
yanxu dai duk ba wannan ba anii dan allah mubar maganar abinda yawuce abaya tsakaninmu...ni yanxu kawai daukar fansa nake so nayi akan ita mimi kamin takoma kan uban gayyar kibani shawara mai yakamata nayi tunda naga kece mai kauna ta tsakani da alllah ba wacce nake tunani ba...!
murmushi anisa take kana tace kawo kunnenki kiji...……...kinji abinda na fada maki ay...?
gumi duk yajika ma ummie jiki tsabagen tsoro tace anii dan allah ki rufa mana asiri wlhy nikam tsoro nakeji bazan iya ba...!
wlhy zaki iya indai daukar fansa ne wato duk kin manta kalar azabar dasuka gana maki kou ummie...?
haka zaki barsu suci bulus akan abinda suka maki...? gaskiya idan kikayi hakan kin rako mata duniya wlhy baki cika cikakkiyar mace datasan inda yake mata ciwo ba...
da kalar maganganunnan har anii tayi nasarar tunzura ummie zuwa ga halaka ta amince da abunda takawo mata...
haka suka kwanta bacci cike da tunani kala kala a zuciyoyinsu...
washe gari haka suka tashi cikin annashuwa kamar babu abinda yafaru...
toh rayuwar gashu'a tama ummie dadi dukdama garin ba wani babban gari bane amma kam akoi su da dadin zama mutanen garin...
bangarensu mimi ma anata cin duniya da tsinke bata da wani matsala a yanxu sai tunanin yar uwarta tana mmkin kanta har yanxu wai itace tayiwa ummie irin wannan cin kashi?
gaskiya ashekarun baya idan akace zata aykata hakan ga ummie dole zata karyata hakan take sbd zata iya barmata ameer dinma amma gashi tayi abinda take dana sani...
ta tabbatar yau da ummie ya ameer ke so toh wlhy ko tantama batayi bazata bari a cutar da itaba……
bangaren ameer kam yama manta da wata ummie shikam balle kuma ta fado masa a rai har yayi tunanin ya aykata abinda ba shine ba...
bayan wata biyar
maryama ta haifo da kyakkyawar yarta waccw taci sunan ummi suna kiranta mami...
kuma alokaci cikin mimi wata bakwai ne...
yau da lafiya gobe babu lfy sbd cikinta yayi wani irin girma na ban mmk...
dole tadawo karkashin iyayenta domin su kula da ita kullum maganarta akan yaushe yar uwarta zata daw tanaimi yafiyarta...?
amma ummie kam fir taki dawowa tace ba yanxu taga dama ba...!
bugu da kari ga aniisa dake zugata irin sosai da sosai dinnan.....yanxu kuma baby ma nada karamin ciki na wata uku...
Yau mimi ta tashi da wani ciwon ciki mai tsanani wanda yatada hankalin iyayensu... tafice hayyacinta sosai ba kadan ba...
ameer hankalinsa idan yayi dubu ya tashi kamar yayi ta kwanzama ihu... sunje asibiti anyi duk gwaje gwajen daya kamata amma kuma ina anrasa takamaimai abinda ke damunta sbd na'ura na nuna masu qalao take...
sai kuka take tana kiran ummi gwani ban tausayi an kira goggo akan ta turo ummie tazo amma tace ita sam bata san zance ba...
Daddy ma dakansa yakira ummie amma dashike akoi irinsu aniisa atare da ita ta badawa idonta toka tace ita sam batasan zancen ba...
wanda hakan baima kowa dadi ba ko kadan har goggo amina lallashinta tayi amma ummie tace allah yakashe ta ita bazata je ba...
hakan ne ya fusata abba yakira yarufeta da fada shin ita wace kalar zuciya ce da ita da baxata iya mance abinda yafaru ba ta yafewa yar uwarta gashinan sai naiman ta takeyi...!
Kawai sai ta fashe da kuka sosai kamar wacce aka zarewa rai...shuru abba yayi yana sauraranta domin jin ba'asin kukan nata...
goggo dasu anisa ma kukan fatyma dasukaji ne yashigo dasu inda suka tarar tafara magana……
Shikenan domin ni marayniyace sai a takuramin ace sainazo naganta sbd bata da lfy...? don anga iyayena basa raye shine ake son a takura min...?
duk abinda ya ameeer da ita mimin suka min kou fada ba'a masu ba ballantana adauki mataki akansu shine ni yanxu akan naki zuwa naga jikin mimi kowa zaice sai nazo naganta sbd ita nata iyayen suna raye...?
kuka takeyi sosai sbd hankalinta yatashi da taji yanda ake cewa mimi na naimanta amma saboda taurin kai yamata katutu bazataje ba...
ita tariga da ta yafewa mimi amma kuma anisa ce ke kara tunzura abin...
vote
comment
share
follow@ummien2018

YOU ARE READING
NUNA SO GABAN KISHIYA!
Actionakan yanayin zamantakewar ma'aurata wanda littafin zaija ra ayinku ne akan yanda wasu mazan ke nuna fifiko tsakanin matansu