orphanage home 2005

26 2 3
                                    

Cikin kaya grey white aka shirya ta, yarinya ce wacce bata wuce shekaru bakwai da haihuwa ba. Kamannin ta ya fi kama da na larabawa, kyakkyawa ce sosai, mai karancin magana.
Doguwar riga da wando, zubin Pakistan wears ta fito tare da mayafin su. Idanunta basa dauke da ko tozali bare fustar ta a sa mata hoda amma a haka ta fito tayi kyau abinta.
Kasancewar ta mai gashin gaban goshi, yasa duk yanda aka boye shi da dan kwali baya ɓoyuwa, don haka doguwar jelar gashin ta kawai ake boyewa cikin ribon bayan ribon.
Kafarta dauke take da Safa saitin kalar kayanta tare da tambarin sunan "zeezee na" haka zalika sneakers din dake kafarta. Jakar goyon ta ce kawai baka tare da kalar grey white na cartoon character din Elsa ta frozen.
Cikin natsuwa ta juyo ta kalli wacce take shirya ta mai suna hafsi tace
' Aunty hafsi? Mai ke faru ne? Naji sai tafi ake da murna ko mun samu baƙi ne?
'eh Zainab ga duk kan alamu, sai dai kar ki manta da abinda nake fada miki kullum babu ruwan ki da magana da wani baƙon da baki sani ba, bayan kun fito daga karatu zaki je ganin likitan ki.
Gyaɗa kai tayi alamun ta gane sannan ta sa kai zata fita. Amma sai ta tsayar da ita sannan ta miko mata wayar da ke kara kusa da ita.
'za ayi miki magana. Ko bata fada mata komai ba ta san muryar wanda ta saba ji ne, sai dai ta kasa gane alaƙar su dashi shin mahaifin ta ne ko kuma wani da yake taimaka mata kawai? Tana ka ra wayar a kunnan ta ta ji Muryar shi yace
'zeezee nah? Bata ce komai ba ta cigaba da sauraron sa.
'da fatan kina nan lafiya kuma hafsi tana kula min da ke sosai? Nan ma bata ce komai ba.
'haba zeezee nah ba dai fishi kike yi dani ba?
'yaushe zaka zo muje gida? Abinda ta iya cewa kenan kafin ta mikawa hafsi wayar ta kama hanya ta fita.
Kallo daya zaka yi mata ka gane cewar duk gatan da take ciki bai ɗebe mata kewa daga kuncin dake ranta ba. Yarinya ce dake da matukar bukatar soyayyar iyayen ta, ba ta mai aiki ba.
Haka ta fita ta samu wuri daya kusa da class din su ta zauna tana kallon yadda sauran yaran ke ta tsalle da murna. Kamar yadda suka zata ziyara aka kawo musu a matsayin su na marayu, wadanda suka rasa gatan iyaye, wanda suke zaune a gida na musamman tare da 'yan uwan da basu da haɗi na jini sai ƙaddara mai muni da ta haɗa su tare. Wasu tsinto su ake akan bola, wasu a kofar gida, wasu a gaban gate din kasuwa, wasu akan layi, wasu kuma a gaban gate din gidan masu kuɗi. Wasu har a cikin kwata, an yasar dasu an bar su saboda ba'a san su. Haka ta fahimta. A kullum tunanin ta shine ita a wanne hali aka samo ta? Waye wanda yake kiranta, kuma yake gatanta ta haka?
  Hawaye ne suka ciko a cikin idanuwan ta, tunanin ta kullum shine ina mahaifiyar ta? Shin bata son ta ne ta kawo ta nan? Ta kan ji kishi mai tsanani idan ta kalli wasu masu zuwa kawo musu ziyara tare da yaran su, mai yasa tasu ƙaddarar ta zamo daban? mai yasa na su iyayen suka kasa zama irin wanda suke kawo musu ziyara da tallafi? Mai yasa aka zabi a barsu a killataccen wuri tamkar dabbobi daji ko na zoo wanda ake mararin ganin su ba wai don tafiya da su ba? Mai yasa ita kulawar ta ta bambanta ta zama tamkar na sarauniya akan sauran yaran da take gani acikin gidan? Wacece ita kuma menene asalin tarihi ta?.... Katse tambayoyin da take yiwa kanta aka yi ta hanyar yi mata magana
'sannu? Tana dago ido ta ga wani yaron matashi wanda bai fi shekaru sha biyar ko sha shidda ba, ya tsira mata ido.
Juyawa ta yi ta kalli gefe da gefen ta don ta tabbatar da ita yake.
Murmushi yayi kana yace
'eh dake nake naga kowa yana ta murna amma ke kin zauna ke kadai kuma kamar kuka kike yi? Sannan wancen zuwan ma idan ban manta ba na ganki, kin zauna ke kadai a bayan wancan bishiyar. Ya nuna mata wata ƙatuwar bishiyar mangwaro dake jikin dakin su.
' haka ne? Ya ce still yana dan murmushi.
Sake binsa tayi da ido kamar wanda ta ga sabon halitta ko kuma yake magana da  wani sabon yare.
'Don Allah ki dena kuka, abinda nazo na fada miki kenan, sannan Allah yana tare da ku, kuma al'umma gaba daya suna tare da ku kuma sun zamu iyayen ku, kin ji...? Ya dan kai dubansa zuwa kasa inda ya cikaro da tambarin da ke jikin takalmin kafarta wato zeezee nah. Don haka yace kin ji ....zeezee nah? Sai dai maganar ta zo a matsayin tambaya ne sama da zaman ta a matsayin lallashi.
Kan shi sai da ya ɗan ɗaure alokacin domin sai da ya sa ke kare mata kallo da kyau domin ya tabbatar da zargin sa akan ta.
Tabbas! wannan yarinyar ba mara gata ko marainiya bace tana da cikakken gata, a zahiri ma daga gidan kuɗi ta fito ko sarauta. Bai kammala nazarinsa ba hafsi ta zo da sauri ta kama mata hannu tana cewa
'mai kike yi anan bana ce kar kiyi magana da kowa ba, zo muje cikin class kafin malamin ku ya shigo.
  Haka ya bi bayan su da kallo, inda ta kama hannun ta suka wuce, kafin su kai ga shigewa cikin ajin yarinyar ta juyo ta sake kallon sa, sannan suka shige.
'Abba mai kake yi anan? Ka zo mu tafi ya ji muryar mama sa tana magana, sake kallon kofar da suka shiga yayi sannan ya zo ya shiga cikin motar suka bar farfajiyar gidan.
Sai dai ya tafi da tunanin ta, ba yau kadai, ba tun shekarar da ta gabata da ya ganta yake ganin ta kusan kullum a mafarkinsa.
Yau kuma da yaga fuskar ta da kyau, yasan ba zai dena ganin ta har sai ya sake ganin ta idan sun sake dawowa. Don haka zai ajiye wannan image din na fuskar ta har zuwa wata dawowar.
Lumshe idanuwa yayi sannan yaje fa kansa a jikin kujerar motar da yake zaune ta gaba, yayi kamar yana son yin barci, sai dai take fuskarta ta dawo mishi. Kyakkyawa, mai manyan idanuwa, pink lips, oval face, black brow, pencil nose. Ta yaya zan iya mantawa da ita yanzu? Mai yake damuna? Mai nake tunani game da ita? Mai ya sa nake tunanin ta har haka? Ya jefa wa kansa tambayoyi marasa adadi, sai dai a halin gaskiya shi kansa bai sani ba, bai son mai yasa take farautar sa a mafarki ba, bai san mai yasa gabansa yake faduwa ba idan ya ganta ko kuma yanzu da yake tuna kamannin ta, ya kasa gane farin ciki yake ji ko akasin haka. Zuciyar sa na fama da different emotions akan yarinya daya.
'Abbba!!! Da sauri ya bude ido ya kalli daddyn sa dake gefansa yana tuƙi.
'naam daddy. Yace cikin sanyi.
' mai kake tunani ne? Ina ta magana shiru?
'ba komai na dan rufe ido ne kadan da yake yau mun tashi da wuri saboda shirye-shiryen zuwa nan so akwai barci a idona, yace tare da ajiyar zuciya.
Daddyn sa kallon sa ya sake yi cikin tsanaki kana yace 'ka tabbata?
'yes, mai kake cewa? Abba ya tambaya
'Tambayar ka yayi ko kana bukatar mu tsaya a pharmacy? Inji maman sa wacce take bayan mota.
' no still ina da ragowar magani na, mu wuce gida kawai.
'To, haka daddyn sa yace sai dai hankalinsa bai kwanta ba, gani yake kamar ɗan sa yana da wata damuwa da yake boyewa. Wanda hakan babbar illa ce ga lafiyarsa.
Suna isa gida, ya wuce dakinsa inda ya ɗan watsa ruwa ya canza kaya zuwa riga mara hannu da wando three quarter na shan iska duk ka Ash colour.
Cikin locker dinsa ya bude inda ya dauko sketching book din sa, tun daga shafi na daya har zuwa na goma duk hoton mace ce wanda babu fuska, ko dai a zaune ta juya fuska ko kuma a tsaye tana kallon ruwa ko taurari.
Idonsa akan guda daya ya tsaya wanda take zaune a kasan bishiyar mangwaro ta juya baya, wani daga bayan ta yana kallonta.
Cikin murmushi wanda ya bayyanar da dimple din dake gefan kumatun sa na dama. Ya dauko alkalamin sa ya rubuta "zeetah" babu shakka yasan sunan ta Zainab. Amma wacece ita? Mai take yi a cikin gidan nan tare da shiga ta alfarma? Abinda yake son sani kenan yanzu.
Cikin kwarewa ya fara wani sabon zanan a sabon shafi, cikin ransa yana fadin a yau na samo fuskar ki da kuma sunan ki zeetah.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 02, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSINTACCIYAR MACE Where stories live. Discover now