DUBAI

4.5K 48 0
                                    

✈️ *DUBAI*✈️

*PAID BOOK*

*HAƘƘIN MALLAKAR*
              👇🏻
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*(UMMUH HAIRAN)*


*_6/7/2020_*


_Sorry Ladies naga qorafinku akan cewa nayi muku mgn biyu am mutane kesaka mgn biyu nayi kyauta an zageni har wasu na cewa wai amm.... Kudai share kawai nasan garin masoyi baya nisa akwai wadanda in yafi dubu nace buks dina zasuyi subscribe so daku nake.

_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_

_Account number_
             👇🏻
     _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
          👇🏻
_09013718241_

_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_
           👇🏻
_09013718241_

_Mutane suna complain din yayi tsada 1k wai wayema yace ku biya 1k ne VIP nace 1k course banson hayaniya Very Important people's, sune zasu biya 1k ba kowa ba idan bakida hali ki shiga single 300 shima normal ne,_

*Episode 10*

Murmushi governor Waziri yayi yace “matsalarki kenan daukan abu da zafi kin dai san halin yaron nan ba juyuwa yakeyi ta dadi ba namijin duniya ne saboda haka ki bisa a sannu ni kaina tsoron hatsabibancin Taheer nakeyi"
Bata iya jurewa kalaman governor Waziri saboda haka ta fice daga bangaren nasa ta koma bantarenta ta rinqa kaiwa da komowa tabbas dole ne ta shiga tsakanin Taheer da Habeey, wannan abin kunya ne abin maqiya suyi musu dariya.
Sake daukar wayarta tayi ta kirashi video call amma yaqi dagawa course yasan halin Mom dinsa yanzu saita gigita masa duniyarsa.


Qwafa tayi ta ajiye wayar ta kira bangaren kula da tafiye tafiye tace tanaso maza a shirya mata tafiyar gaggawa zuwa Dubai.
First lady zatayi tafiya babu bata lkc sukace “angama ranki ya dade" bangaren yayanta Mata ta shiga “Kubrah ke Kubrah Ina Bushirah ku shirya jibi zamu tafi Dubai duk abinda Son yakeyi a qasar nan saiya bari ya biyomu"
Kallonta Bushirah tayi tace “amma Mom kinsan halin Yaya bayason ana shigar masa rayuwa ko?" Daquwa ta watsa mata tace “dake dashi din zan hada inci ubanku na shiga rayuwar tasa nace na shiga ya fitar dani"


Qasa tayi da kanta tana qunquni Mom ta cafketa tace “zan dagargazaki makira kitifaffiya almura" kuka ta farayi tana buga qafa tace “kuma kawai daga na fada miki gaskiya naga yace akwai wacce yakeso, to a qyaleshi mana ya kawota ai komai lkc ne amma kunbi kun dameshi da aure aure bayan ga Ya Mahfuz nan shima yana sharholiyarsa ko mgnr auren ma bayayi, ni na rasa meye yasa kika sawa rayuwar Yaya Taheer ido haka Mom shifa namiji ba kamar mace bane yanada burukansa da muradans..."
Ficewa Mom tayi saboda ta lura duka halayyar yayan nata sunyi hannun riga da nata Mahfuz Taheer da Bushirah sunsha kwana da tunaninta, dama dama Kubrah ita wannan yar I don't care ce.

_________________Cikin kwanaki biyun nan sosai Habeey ta karbi gashin azaba a gurin Taheer duk da rashin lfyr da taketa fama da ita amma yaqi saurara mata.
Saida yaga tana neman tafiya garin da babu hanyar dawowa sannan ya daga mata qafa ya Kira mata likita ya sanya mata drip ya bata magunguna tare da injection's sosai Taheer yaji yanajin haushin kansa daya kasa fahimtar yanayin quncin da zuciyar masoyiyar tasa take ciki.
Ya shiga tashin hankali lkcn da likitan yake mata hoton qirjinta yake zayyana masa abubuwan da suke damunta, baisan sanda wasu hawayen tausayinta suka zubo masa ba.


Koda suka koma gda tattalinta ya rinqayi ko Motsin kirki bai barinta tayi, shine yakeyi mata alluran daqyar bayan ansha daga saboda shikam Allah ya dora masa jaraba akan Habeey ko yaya jikinta zai hadu da nasa sai yaji yanason kasancewa da ita.
Bacci ne ya zame mata abin yinta ko yaushe tana bacci, duk da Bushirah ta sanar dashi zuwan Hajiya bai wani damu ba illa dai shiryawa zuwan nata da yayi yasan dan qaramin yaqi zasuyi da ita.
Ranar da zasu taho Habeey a kwance ta yini ciwon baya yana damunta ko abinci bata iyaci sai yayi mata dabara yake bata take samu tanaci tana hadiya kamar me hadiyar qwaya, kawai yau tunda ya tashi yakejin wata masifaffiyar jaraba na damunsa tun yana control din kansa har ya gaza ya riqo Habibah jikinsa na rawa yace.



DUBAIWhere stories live. Discover now