AKAN Y'ATAH

49 0 0
                                    


                           

Da asuba bayan ya gama sallah yana bude wayarsa ya ci karo da miss calls na Kamal, yana kiransa kusan sau biyar a na shiddan ya dauka, abinda ya fara ji ya sashi salati ba shiri, ya dade da wayar sagale a kunnensa sai da yaji muryar Kamal "Kai sam aikin lkitanci bai dace da kai ba, tausayinka yayi yawa Bilal..." Cikin rauni murya yace "Dole ne Kamal na shaku da Mama sosai..." Kamal ya sauke ajiyar zuciya
"Tabbas hakane, addu'armu Mama ke bukata Allah ya jikanta yasa iyakar wahalar kenan" cikin dakiya Bilal yace "Ameen thumma ameen, gani nan zuwa yanzu jana'iza"


********

DUBAI (UAE)

5 days later


A zamansu Dubai banda siyayyar shagon Sanayah ba inda basuje yawon shakatawa ba, kayan shagon Sanayah kuwa ba abinda Ummu bata siya ba, tun daga kansu gold, diamond, abayas, bags, gowns, english wears, costumes da cosmetics, shoes, a bangaren kayan maza ma ta siya riguna da wanduna as in jeans, takalma, covered shoes, wrist watch kala kala etc...
Ranar da zasu bar Dubai Sanayah murna kamar me zataje Korea, duniya tana son Korea sheyasa batada aiki sai kallon Korean series.
Tun asubar farko ta farka dama ta riga kowa shiryawa tare da fito da akwatunanta living room. Karfe 7 da rabi suka shirya gaba daya sam Mummy batayi mamakin ganin Sanayah living room ba don dama tasan a rina.
Karfe kusan tara ta wuce suka daga sai Korea.


********

SOUTH KOREA

SEOUL, INCHEON INTERNATIONAL AIRPORT

6pm suka sauka airport din, Nan suka samu driver ya kaisu masaukin su, a gajiye suke saboda doguwar tafiyar da sukayi, a wata babbar hotel suka sauka dakunan kamar apartment suke, Nan kowa ya nufi bedroom din, Saida kowa yai wanka ya kimtsa sannan suka fito daidai lokacin da aka Danna ball din d'akin , sanayaah ta bude,  room service ne da abinci tana turowa saman wani Dan table, hanya sanah ta Bata ta shigo ta jere masu abincin a wani madaidaicin dinning table bayan ta gaida su mama ta wuce ta fita, nisawa Mama tayi sannan Tace "Ummu kin tabbata da abincin Nan dai ko? Kar a kawo Mana Naman alade ko na Kare mu Kama ci bamu sani ba?" ta ida managar tana Kai duban ka ga mummy, murmushi mummy tayi "Mama Sai da nayi binciken sosai kafin in Kama Mana hotel dinnan, saboda gudun haka ne ma na zabi wannan hotel din, in kin lura ai ba kamar sauran hotel take ba apartment ne lafiya lau Kinga harda kitchen saboda mu rinka girka abincin mu da kanmu wannan ma Dan duk mun gaji shiyasa nayi Mana order shi kafin mu fita muyo sayayyar abubuwan da zamu bukata" cikin gamsuwa mama ta kada kai, murmushi mummy tayi ta maida hankalin ta ga abinci taliya ce kamar yanda ta bukata Sai fruit Nan kowa ya zauna ya cika cikin shi, sannan suka tashi sukayi isha'i, sannan kowa ya Kama hanyar dakin shi Dan samu su kwanta su huta Dan ba karamar gajiya sukayi ba.

Tunda Sanayah tayi sallah asuba Bata koma bacci ba, tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar Riga ta material Mai kalar red da ratsin Ash kayan sun bala'in amsar farar fatar ta, wata hula ta daura a kanta Mai kyau wacce ta shiga da kayan sannan da dauko takalmi high heels Ash da irin side bags din Nan itama Ash ta rataya, wani katon Google ta Sa Wanda ya kusa rufe fuskar ta shima Ash Sai veil dinta medium irin material din ba karamin haduwa tayi ba karfe 8 ta fito daga d'akin ta, balcony ta nufa ta Dade tana kallon garin, ba karamin burge ta yayi ba gaskiya garin ya hadu fiye da tunanin ta, tana a tsaye taji mummy na Kiran ta, ciki ta nufa da sauri tana ansawa, tsaye mummy tayi tana Kare Mata kallo da mamaki "wai har kin tashi kin shirya?" Ta tambayeta fuskar ta kunshe da mamaki, Dan batayi zaton ta tashi da wuri haka ba gashi alamu sun nuna har wanka tayi ta shirya.
"Mummy tunda na tashi fa da asuba ai ban koma ba fa" 

Murmushi mummy tayi tana girgiza kai, ta ayyana a ranta Bari ta Dan jata taga ya zatayi "toh wannan uwar kwalliyan da kikayi tunda safe fa? kamar zakije wani wuri ta micece?". Cikin katsewar hanzari sanah ta kalli mummy da fuskar jimami tana zancen zuci "kardai mummy Tace yau baza mu fita ba sai gobe?" dake fa nake kika kafa man Ido kamar baki taba ganina ba." mummy ce ta katse Mata tunanin zucin da takeyi, cikin sanyin jiki sanayaah ta Kai kallon ta ga mama da fitowar ta kenan tana tambaya mummy ya akayi?, Tace "a'a sanah ce naga taci uban gayu kamar wacce zata je gasar sarauniyar kyau shine nake tambayar ta ko wani wurin zataje?" Kuma Naga dai ba sanin gari tayi ba balle...." ta ida maganar ta kunshe dariyar da tazo Mata ganin yanda sanayah tayi zuru tana kallon ta kamar marar gaskiya, murmushi Mama tayi da ta fahimce Ummu so take kawai ta gara diyar tata, girgiza kai tayi ta canza maganar da "Ummu yunwa fa nakeji Dan ita ta fito Dani ma, inba haka ba da ba abunda zai fiddo ni yau saidai inyi sallah in koma in kwanta Dan ba karamin gajiya nayi ba" ta karashe zancen tana kallon sanah ta wutsiyar Ido da tun dazu ta kasa magana Sai fuskar ta da ta canza yanayi na damuya.

AKAN Y'ATAH. COMPLETEDWhere stories live. Discover now