Chapter 1

84 3 4
                                    

🌀🌀🌀🌀
*IZAYYAH…!*
_(Return)_     
🌀🌀🌀🌀
          NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''       
*MUM SEEYAMA*

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN🚴🏻‍♀️'''

*Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani ikon dawowa a karo na barkatai, ina ƙara godiya a gareka yadda ka bani dama na fara, Allah yasa in kai ƙarshensa lafiya tare damasu Karatu baki ɗaya Ameen ya Allah.*

*PAGE 1*
  *……* Haƙiƙa ita Duniya babu abunda baya faruwa a cikinta walau mai kyau walau maras kyau, Rayuwa in tazo wa mutum a baibai to yayi ƙoƙari ya karɓeta hannu bibiyu baka da tsimi ko dabaran da zaka gyarata, Ina ko ta zoma dai dai ta ka ƙara riƙeta gam ba wai ka barta tana tangal tangal ba, domin watarana zaka nemeta ka rasa.

*……* "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,"Oum mai yake faru dake haka dan Allah ki tashi karki mutu ki barni ba tare da anyi Aurena ba wallahi bazan samu farin ciki ba matuƙar bakya duniya dan Allah ki tashi ki gani Oum nice fa Azizarki, ta faɗa tana mai ƙara fashewa da kuma,  Hajiya Kaka ce ta shigo tace "Ke Aziza wai mai yake faruwa ne kike ta rusar Ku… yawun bakinta ne ya ƙafe ta kasa ƙarasa maganar ganin Oum kwance tamkar gawa da sauri ta ƙarasa tace "Aziza mai ya sameta haka?,"Wallahi magana kawai na faɗa mata sai kuma wani abu da ta kalla a waya shikenam ta faɗi ban san miye damuwarta ba ta faɗa tana sake fashewa da kuka, Kaka ne tace "Ba kuka za kiyi ba maza kawo min ruwa mai sanyi kika, da sauri taje ta ɗauko mata, Kaka tsiyaya mata tayi a jiki sai da ta jiƙata sharƙaf sannam taja dogon numfashi a hankali Oum ta fara buɗe idanunta ta sauƙesu akan Aziza wacce idanunta yayi matuƙar kumbura ga kuma ja da yayi, Kaka ne tace "Sanni Bara'atu ke ko mai ya tada miki da hankali har kika yi irin wannam dogon sumar? Kaka ta faɗa da alamar tambaya, murmushin yaƙe Oum tayi tace "Um…Um… Um dama na ɗan shiga firgici ne na rabuwa da Fa'eesha sai yanxu naji matuƙar kewarta na zuwarmin, ta faɗa cike da ƙinƙina, Kaka ta miƙe tace "Ayya ai sai haƙuri Aure ai ba mutuwa bace gashi kuna kusa Ummanta ne ya dace da haka ma bake ba saboda basa kusa amma ke ko da yaushe za ki iya zuwa ki ganta, "Eh kuma haka ne kam ta faɗa tana gallaea Kaka harara, Kaka ko tuni tayi hanyar fita dan tasan ƙarya kawai ta gulla mata, tana fita ta nufi ɗakin da aka ware musu nam ta sanarwa da su Umma da abunda ke faruwa murmushi Umma tayi dan tasan wannam tatsuniya ce kawai ta zuba amma akwai dalilinta nayin haka, Allah dai ya tseratar mata da ɗiyarta tunda tayi Aurenta a gidan mutunci, haka suka kwanta cikin shiri da gobe zasu tafi tunda an gama komai, Oum ko miƙewa tayi ta nufi ɗakinta cike da baƙin cikin irin dukiyar da Mijin Fa'eesha ya tara sa kuma irin tsaruwar gidanta, da ƙudirin hanata zaman lafiya a gidan tayi bacci, dan ta saka a ranta sai ta cireta ta kai ɗiyarta guda ɗaya a maimakonta…
           Tunda su Eeshart suka tafi Fa'eesha take cikin tashin hankali dan tayi matuƙar tsorata da Lamarin shi kansa Hayatuddeen ya firgita san Yarinyar ta matuƙar ƙuresa, cikin nutsuwa ya koma hannun Fa'eesha da jikinta yayi matuƙar sanyi yace "Karki damu babu abun da zata iya zan yiwa tufkar hanci, "Kamar ya za kayiwa tufkar hanci kana jin abun da ta faɗa a gabanka amma baka iya cewa komai ba, tukunna ma wacece ita wannam ɗin miye alaƙanka da ita? ta faɗa cikin ɓacin rai da kuma alamar tambaya, murmushin yaƙe yayi yace "Uhum labarin da tsayi amma bari na faɗa miki gajeran ciki ita ɗin Ƴar uwatace kuma ta jima tana sona amma ni sam bana da ra'ayinta shiyasa take ta wannam haukan, ajiyar zuciya ta sauƙe jin shi baya ra'ayinta hakan ya sanyaya maya zuciya sosai, nam ya lakaci kumatun ta yace "wato da kishin ne ya motsa kika haɗe min rai?  to ai ni naki ne ke kaɗai daga ke kuma ba ƙari, rufe fuskarta tayi alamar jin kunya, nam ya ɗagata chak suka nufi toilet ya cire mata kaya duka wanka ya mata siɗak ita dai duk kunya ta isheta dan sam bata bari sun haɗa ido ba har ya saka ta tayi Alwala ya fito da ita kayan bacci ya saka mata masu matuƙar kyau da taushi, ya shafeta da mai tare da turare masu matuƙar daɗi da ƙamshi, toilet ɗin ya koma shima yayi wankan sannam ya ɗauro Alwala yana fitowa ya sanya mata hijabi ya jasu sallah, Bayan sun idar ne ya jawo leda ya je kitchen ya ɗauko Cup da filet ya zuba musu kaza tare da Milk nam ya jawota jikinsa ya mata tambayo kamar dai yadda Addini ya tanadar komai ta amsa masa yadda ya dace ya kuma riƙe kanta ya mata Addu'a nam ya cire mata hijabi ya mannata da jikinsa tare da shafe jikinta a haka ya fara bata naman ba musu ta karɓa ta fara ci a hankali hat sai da ta ƙushi ya fara Milk ɗin tasha sosai, ƙara rungumeta yayi ya fara cin nasa shima sai da ya ƙoshi sannam ya tattara komai yakai kitchen ya dawo in da ya barta haka ya sameta…
      Yana zuwa ya ɗagata tare da saka ta a gado rage musu hasken ɗakin yayi ya saka musu mai duhu, rungumarta yayi ya kai bakinsa sai tin kunnenta yace "Alhamdulillah yau dai na ɗaura kin zama mallaki ne, sauran aikim ko ya rage nawa, karki manta fa ina son Love, murmushi tayi tare da rufe idanunta da tafin hannunta wata kunya taji ta rufeta tabbas mijinta ɗan son Soyayya ne dan haka doke ta cire kunya sannam tadage tana faran ta masa rai insha Allah zanyi haka, "Aiko kamar kin sani inko kika minhaka to tabbas kin gama mim komai wallahi, cike da mamaki tace "kamar ya? "Kamar yadda kika ji mana,"kana nufin duk abun da na faɗa kaji?,"ƙwarai kuwa,"Wayyoo ni!!! taya kaji abun da ke zuciyata?,"Ji nayi kina ta magana ashe wai da zuciyarki kike magana, ashe nine zuciyar taki kinga ko ai dole naji, murmushi tayi tace "haka ne… bata ida rufe baki ba taji hannunsa akan Boobs ɗinta, sai da taji wani yar haka ya fara chakwarkwa ɗata, sai dai muce ango da amarya sai da safe asha amarci lafiya.
                  Eeshart suna fita daga part ɗin Fa'eesha ɗayan Part ɗin suka shiga suna shiga suka zauna Eeshart tana fashewa da wani uban kuka da sauri Kursum tace "Haba Eeshart karki bada mata mana, nasan iya abunda kika musu yanxu bazai bari su samu masalaha ba yanxu haka ƙila faɗa suke daga ƙarshe kuma ya saketa kinga sai kuma zancen aurenku dan Allah ki dai na kuka tunda har yanxu da sauran tuggun da zamu musu in har sun tsallake wannam baza su iya tsallake na gaba ba dan haka ki kwantar da hankalinki, "Haba Kursum taya zaki ce na kwantar da hankali na bayan gashi chan da wata macen wadda ba ni ba, ban san mai Fa'eesha ta fini dashi ba wanda ya ƙini ita ya sota ban san miye dalilinsa na ƙi na ba haƙiƙa ko kisa ne sai nayi domin na samu ya Hayatu sai dai duk abunda zai faru ya faru matuƙar zai Aureni wallahi akwai bala'i sosai…

'''Uhum to ya kuka ji wannam ɗin sharhin ku shi zai sa na gane hakam.''' *INA ZUWA*🚴🏻‍♀️🚴🏻‍♀️

_Amma ta Hanyar Nuna min Ƙauna da Soyayyarku wajen Siyan *IZAYYAH (Return)...!* Akan Naira 200 kachal👌🏻Vip 400 ta wannam Account Number, 0134205910 HAFSAT AYUBA UNION BANK, sai ki turo shaidar biya ta wannam Number 08132761212 ko Katin waya na MTN, shima sai ki ɗauko hoton Katin a Turo kai tsaye ta wannam Number 08132761212 ga masu saya na farko zasu samesa a 200 Vip 400 sai kunzo Masoyana._

_Kada fa ku manta Akwai Garaɓasa na mai son siyan Biyu *NA YARDA NA MUTU...!*  Shima Dai nawa ne a 400 Vip 500 ne Kachal👌🏻in kuma ɗaya kake so 300  Shima ta wannam Number Account ɗin da na bada da Number Wayan ta Sama ko Kuma kai Tsaye ku Tuntuɓe ni ta wannam Number domin ƙarin bayani._
08132761212

*HAFSAT A GARKUWA CE*🤙🏻

IZAYYAH (Return)Where stories live. Discover now