Chapter 2

23 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀
*IZAYYAH…!*
_(Return)_     
🌀🌀🌀🌀
          NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''       
*MUM SEEYAMA*

©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN🚴🏻‍♀️'''

*SADAUKARWA*
'''NAZIFI YAREEMA'''
_Ina matuƙar gdy a gareka_

*PAGE 2*
*…* Kursum tace "duk da nasan kina matuƙar son Hayat amma bai kamata kina faɗar haka ba, shin zaki iya kashe wanda kike so kenam? inko har haka ne to ya tabbata bakya son sa, matuƙar kina sosan baza ki so wani abu ya samesa ba balle har ke ki iya kashesa, mu dai tsaya a matarsan da kuma tada musu bala'i kala daban-daban. "Haka ne kuma Kursum kin faɗi gaskiya nima raina ne ba ɓaci sosai shiyasa na faɗi haka, amma ija zan iya kashe sa, amma fa karki manta matuƙar na rasa sa to wallahi zan iya kashe shin ma. ta faɗa tana mai ƙara fashewa da kuka, Kursum tace "to naji yanzu dai taso muje mu kwanta dan dare yayi sosai gobe ma ɗaura, miƙewa suka yi suka shiga ɗaki na kusa dasu suka kwanta, tuni Kursum tayi bacci amma Eeshart idanunta biyu tunani take yanzu yana chan da wata bada ita ba, yanzu yana chan yana lailaya wata ita tana nam, dole tasan abunyi,cike da wannam zantukam bacci ɓarawo ya saceta.
*Washe gari*

Tun ƙarfe takwas su Umma suka ɗauki hanya zuwa Kano tayi kuka sosai tunanin ɗiyarta ce fal cikin zuciyarta, duk da tasan akwai ƴan uwanta da suke garin zasu na ɗan leƙa ta cike da kewa suka tafi, Oum kuwa daɗi taji kamar am mata bishara da aljanna dan dama zaman da suke ji tayi duk ta takura amma yanzu da suka tafi sai taji saƙayau, Aziza ta saka su gyara gidan amma fir suka ƙi daga ƙarshe ma sai bar mata gidan suka yi, haka ta tiƙi aikin gidan sosai ta gaji hada ƴar ƙwallarta anam ta tabbatar da Fa'eesha tana ƙoƙari sosai.

        Fa'eesha kwance take a jikin Hayatu sai shagwaɓa take zuba masa, shiko sai riritata yake kamar ƙwai, cike da farin ciki yace "haƙiƙa jiya kin shayar dani kin kuma kai ni duniyar da ban taɓa riskarsa ba, tun a jiya na tanadar ki miki da kyautarki, nam ya ciro kwali dakr gefensa yace "rufe idanunki in kina so kiga wannam kyautar. da sauri ta rufe da tafin hannunta yace "miƙo hannunki. miƙo masa taya nam ya buɗe kwalin waya ya cire mai matuƙar kyau da tsada a hannunta ya saka mata ya ƙara ciro wani Key ya saka mata sannam ya cire damin kuɗi guda uku dubu ɗari uku kenam nam ya ɗaura mata yace "to ki buɗe idon ko, amma kafin nam duk mai kika gani a hannunki karki yarda kice komai balle kice zaki mai do, inko kika yi haka zamu samu tsaɓani dake sosai kinji ko? da to ta amsa masa dan ita ta zaƙu ta buɗe idanunta taga wannam kyauta, nam yace "to maza buɗe, aiko da sauri ta buɗe ta fara bin hannunta da kallo cike da mamaki nam ta wawwaresu, taga kuɗi, taga waya, ga kuma key, duk da yace kar tayi magana amma dole za tayi dan taji key ɗin na miye tare da kuɗin, murmushi tayi sannam tace "Yallaɓai to key ɗin na miye tare da kuɗin? hararar wasa ya mata sannam yace "shi key ɗin na motarki ce gata chan a waje kuɗin kuwa na baki na kashe wane da sayan maƙulashe dan nasan nayi ajiye a jiyan nam,da sauri ta rufe idanunta tace "kai Mijina har kasa naji kunya daga jiya kace har a samu baby?,"to ki tsaya wasa ni kam nasan nayi ajiya ato garama ki fara shirin karɓar baby tun yanzu,"to Allah ya kawo masu albarka,"amin ya Allah haka nake so matar Aljanna ya faɗa yana sake rungumeta, buɗe idonta tayi tace "haƙiƙa duk da kace kar nayi magana amma dole nayi saboda ka faranta min fiye da zato na, Allah ya biyaka da gidan aljanna amma kuma kuɗin… shitttt!!! bana son jin komai ya faɗa tare da ɗora yatsarsa a bakinta alamun tayi shiru, ya ƙara da cewa "Allah ya sunduma mu a aljanna baki ɗaya ya cire yatsan tare da haɗe bakinsu guri ɗaya ya fara mata wani irin hot kiss. taf! taf! taf!!! suka ji ana tafi da sauri suka ɗago ido, Eeshart ce tsaye ita da Kursum Eeshart ce mai tafin, ta iso inda suke tace "yayi dai ango da amarya kuna sha'aninku yasin irin wannam kyauta duk akan ta baka budurcinta ashe biya ake kenam ban sani ba? lalle Yaya Hayatuddeen ashe haka kake kashe mata kuɗi, kuma duk iskanci da kuja gamayi a ɗaki bai isheku ba? ke kuma hada wani maƙalƙalesa talakar banza da hufi wawiya ƙazama, tun da kika aure abunda nake so ti wallahi bake ba zaman lafiya a gidan nam sai kin fita da ƙafarki jaka ka… fauu! fauu! fafauu!!! sautin marin da ya sauƙa a fuskar Eeshart wani irin gigicaccan ƙara tayi ta durƙushe a wajen…
   Afusace Hayatuddeen yace "ke dan ubanki karki ga na barki kuma ki wuce gona da iri wallahi zan tattakaki ne akan Fa'eesha na faɗa miki bana sonki bana sonki bana sonki ko ana so dole ne? ina tambayarki nace ko ana so dole? to tun wuri ki san inda dare ya miki, ko da ina sonki bani da ra'ayi haɗa mata biyu dan haka maza a cikin wanda suke zuwa wajenki ki nemi mijin aure yafi miki alheri ke in banda hauka ba taya zaki tsaya shiririta akan wanda baya sonki? sai kace ba… "dakata Hayatuddeen wulaƙancin ya iska haka a gaban matarka kake cimin zarafi haka to ka sani ku zaka mutu sai ka aureni kuma wannam abun da kamin zanfashe walau akan matarka walau akan ka dan haka ku kwana da shirin ramako, daga haka ta wuce fuuuu kamar kububuwa, Kursum ta mara mata baya, Fa'eesha ne ta durƙushe a wajen tare da wani irin sakin kuka haƙiɗa ta tausayawa Eeshart kuma ta tausayawa kanta sosai take kuka, da sauri Hayatuddeen ya kamota ya haɗata da jikinsa yace "haba *My wife* kukan miye kuma haka? na san akan abunda wacchar mahaukaciyar ta faɗa miji ne ya ɓata miki rai, wallahi ni yafi ɓatamim ma akan ki amma dan Allah kiyi haƙuri nasan ni na ja miki ko… "Wallahi tana sonka tabbas Eeshart tana matuƙar ƙaunarka dan Allah Mijina ka amince da soyayyar Eeshart…"Dakata Fa'eesha wannam wani irin magana kike? kin ko san mai kike cefa? na auri Eeshart fa kika ce? to wallahi ki sani duk randa kika ƙara min wannam zancen ranki in yayi dubu sai ya ɓaci, ke sai kace ba mace ba oh dama dai ba sona kike ba domin mai son ka shi yake kishinka, baki sona shiyasa kike min zancen na Auri Eeshart kin ko san wace Eeshart? Hmm wallahi in da kinsan wace ita baza kice na aureta ba, ta inda yake shiga ba ta nam yake fita ba, Fa'eesha ganin haka yasa ta saki wani irin Kuka dan ta matuƙar tsorata da ganin yana yinsa yadda ya koma, tabbas tana son mijinta amma yau ya tsorata ta dan yadda yake diri ga kuma yadda idanunsa ya chanja launi, da sauri ta rungumoshi tana kuka tace "Mijin wannam ina sonka ina kuma matuƙar ƙaunarka ban san wace Eeshart ba, amma na ga yadda take ƙaunarka ne na kuma tausaya mata amma dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan ƙara ba kar kayi fushi dani mijina. ta ƙarasa tare da shigewa jikinsa ta sake wani sabon kuka,  murmushi yayi wanda ya ƙara baiyanar da kyansa ya kamo ta ya share mata hawaye cike da murmushi yace " *My wife* baki min komai ba illa rashin kishina da kika nuna, wallahi bazan iya fushi da ke ba in nayi fushi dake ai kamar nayi da kai na ne, kar ma kisa damuwa a ranki yanzu dai muje ɗaki ki ƙaramin  domin wani ya taru fa. da sauri ta ɗago tace "mai kuma ya taru? ,"abum mana ke dai taso muje ki gani dan a buƙace nake…
        Eeshart suna fita ta durƙushe a wajen ta saki wani marayan kuka, Kursum ne tace "haba Ƙawata a yau na tabbatar da Hayatuddeen baya sonki baya ƙaunarki hasalima ya tsaneki dan Allah na roƙeƙi ki rabu da Hayatun nam nikam ka samari da dama nam a gidan duniya sai binki suke, sai kin zaɓa kin darje haba Eeshart kefa… "ke dahalla tsaya min kina tunanin na bar hayatu? Uhum wannam abun kina nufin na barsa kenam? ina bazai yiwu ba dole nine ajalin matarsa, nasan muddin ta mutu dole ya so ni kuma ya zauna dani, dan haka dole yanzu muje na siyo sabuwar wuƙa dan a yau Fa'eesha zata bar duniya…

_Wannam shine ƙarshen Free page nasan da yawa kun karanta sa dan haka na bada Free page guda biyu_

'''Tabbas yanzu wasan zai fara, wasa farin girki, duk mai so a tafi dashi domin yaji wannam chakwakiya da takr kunno kawai tofa yayi saurin garzayowa.'''

_Amma ta Hanyar Nuna min Ƙauna da Soyayyarku wajen Siyan *NA YARDA NA MUTU...!* Akan Naira 300 kachal👌🏻Vip 500 ta wannam Account Number, 0134205910 HAFSAT AYUBA UNION BANK, sai ki turo shaidar biya ta wannam Number 08132761212 ko Katin waya na MTN, shima sai ki ɗauko hoton Katin a Turo kai tsaye ta wannam Number 08132761212 ga masu saya na farko zasu samesa a 200 Vip 400 sai kunzo Masoyana._

_Kada fa ku manta Akwai Garaɓasa na mai son siyan Biyu *IZAYYAH (Return)...!*  Shima Dai nawa ne a 400 Vip 500 ne Kachal👌🏻 Shima ta wannam Number Account ɗin da na bada da Number Wayan ta Sama ko Kuma kai Tsaye ku Tuntuɓe ni ta wannam Number domin ƙarin bayani._
08132761212

*HAFSAT A GARKUWA CE*🤙🏻

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 22, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

IZAYYAH (Return)Where stories live. Discover now