🅿️➡️1️⃣6️⃣

25 2 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

  🌐 *ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
      
*_MALLAKIN_*
*MRS NOOUR(PHEEYMARRH)*

WATTPAD *@ MRS NOOUR*
Email@ pheeeymarrh@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

_All is dedicated to u my dear dedeey ƴaruwa rabin jiki,dukda baki karanta novel☹_
*Ummu Maryam(Mrs Abubakar)*
Allah ya tsone idanun makiya akan ki🥰

🅿➡1️⃣6️⃣

kyaututtuka  masu daraja da yawan gaske ta same su wurin manyan mutane ƙawayen Mammi waɗanda suka zo,cikin kwanciyar hankali aka gama komai gab da magrib,sannan aka maida ita gidan ta wanda yake tamkar gida ɗaya ne a haɗe sai dai irin  katangar nan wacce kana iya hango mutum ba mai tsayi bace ita ta raba  tsakanin gidan,wanda dama tun tuni daddyn ya gina ya ƙebewa ƴaƴan shi domin zuwan wannan lokaci na auren su.

Sallah sukayi,sanna aka sake kimtsa mata gidan duk da babu datti gidan,bayan kammala cin abincin du wanda dama daga Hajjo sai Ni'ima suka rage,hajjo ta sanya ta tayi wanka lafiyayye da wasu irin turaruka wanda mai gyaran jikin ta bayar tayi amfani da shi in an kawo ta.

Duk da yadda take jin tsananin faɗuwar gaba hakan bai hanata tsayawa ta yi wanka na musamman ta wanke ta goge jikinta tas da mayuka wanka masu matuƙar kamshi da sanya santsi da laushin fata,sannan ta sake yin wanka dana turaruka,wanda tun kafin ta fito daga bathroom ɗin wani irin sanyayan ƙamshi mai jan hankali da sanyaya zuciya ya cika gidan,sai da ta ɗan jira ruwan ya ɗan tsane a jikinta kafin ta ɗauro towel iya ƙasan gwiwa ta yafa mayafin ta akan ta sannan ta fito.

Shafa tayi da wani mai shima wanda duka yana cikin kayan gyaranta,ba ta tsaya kwalliya sai powder kawai ta sanya da man baki mai ƙyalli ta ɗan zirara kwalli suma Ni'ima ce ta matsa mata.Atampar da suka za6ar mata ta sanya ta pink color mai ratsin baki-baki da light yellow, ɗinkin riga da zani,rigar ta kai iya gwiwa wato three quater,dinkin yasha aiki a jiki na surfani wanda aka yiwa ado sa stones masu matuƙar ƙyalle da kyau,sarka da warwaro haɗe da ɗan kunne farare masu sauƙin kwalliya ta sanya wanda suka ƙara haska ta.

guɗa sosai hajjo ta saki cikin farin ciki,sannan tace"alhamdullih Allah ya tsone idanun makiya akan ki".

"Kai hajjo kin manta dare ne kike wannan guɗar"Ni'ima ta faɗa tana sake fesge jikin ƴar uwar ta da turare, itama cikin tsannin farin ciki ganin irin kyauwun da ƴar uwar ta tayi wanda ko mai hassadar mai hassada dole ya faɗi kyauwun ta ko a zucci ne.matsawa Ni'ima tayi kusa da Anisha sukayi hoto na,sanna kowacce ta sanya gyalen ta domin tafiya gida,hakan ya ƙara tada hankalin Anisha saboda dama chan ganin su ne ya sanya take dauriya.

Har bakin kofar fita daga parlor ta rakasu duk da hanatan da Hajjo tayi,da ƙyar suka lalla6a ta ta saki hannu Ni'ima da alƙawarin dawowa gobe da safe da tayi mata,babu yadda ta iya haka ta hakura ta rufe kofar shigan ta koma bakin window ta tsaya tana kallo har driver ya ja motar suka fita daga gidan aka rufe gate ɗin,juyawa tayi jiki a sanyaye ta komawa sama ta shiga ɗakin ta a matuƙar tsorace ta zauna a kan gado a takure,ba kajin ƙarar komai sai na ac da injina masu aiki na gidan saboda unguwar ta masu hannu da shuni ne ko da rana ne sai a yanka a babbake basu sani ba balle da daddare,adduoe tayi ta kwanta a tsorace tana kallon agogo goma har da minti ɗaya.rufe idanu tayi tunani iri iri.

Anya batayi gangancin barin Na'ima ta tafi ba ,taya zata iya kwana gidan nan ita ɗaya,wani irin aiki ne wanna da zai iya sanya Abeer ya barta a yau data tare a gidan shi,bayan duk irin tarin buri da tanadi dayayiwa wannan ranar?,wayar ta ta lalubo a gefen pillow da ta datayi matashi da shi,number Abeer ta soma kira karo na ba adadi,har lokacin a kashe take,ajiye ta tayi a gefe tana rufe idanu cikin tsoro,tana fatan ta iya samun bacci ko da na awa ɗaya ne.

Kamar yadda suka shirya shirin su haka Hajiya karima ta tabbatar ma Mammi da komai zai tafi yadda suka so nan da ɗan lokaci ƙadan,sosai Mammi tayi farin ciki duk da dai zuciyar ta takasa nutsuwa da daina bugawa cikin rashin kwanciyar hankali,kallo ɗaya wanda ya san ta zai yi mata ya gane bata cikin nutsuwa,kuɗaɗe masu yawa ta ɗibo ta zuba a jaka ta miƙawa hajiya karima sukayi sallama ta tafi ta bar mammi da fargaba biyu ,ta nasara ko akasin hakan.

Yayinda hajiya karima ta tafi da murnar abu biyu na ganin burin ta ya kusa cika da na shirin su da ƴar ta.

Kwance yake bisa ɗaya daga cikin kujerun parlor yayi matashi da duka hannuwan shi a ƙasan ƙeyar shi,gaba ɗaya pillows ɗin kan kujerar ya yi watsi dasu a ƙasa,knocking ɗin da ake sannu a hankali shi ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa,ƙaramin tsaki yayi ba tare da ya ko motsa ba haka kuma bai buɗe idanun shi ba.

Jin shirun yayi yawa ya sanya Sahla yanke shawarar shiga Ciki kamar yadda mommyn nata ta umarce ta don sun kwana da sanin cewa ba lallai ya sauraresu cikin sauƙi ba,dai dai ta muryar ta tayi haɗeda jan ƴar matsattsun kayan dake jikin ta ta gyara zaman su,sannan ta shiga bakin ta ɗauke da sallama.

Sosai ranshi ya 6aci da jin muryar mace duk da bai san wacece ba,kawai dai baya buƙatar kowa kusa dashi ,sannan baya son damuwa kai ko kwakkwaran motsi baya son ji daga ko ina.

Sallama ta ske yi cikin rgae murya da siranta ta,rintse idanun shi ya sake yi saboda yadda yake jin muryar ta cika mashi dodon kunne tamkar kanshi zai tsage,hannun shi ɗaya ya cire ya dafe goshin shi da shi cikin bacin rai.

Barka da hutawa,da fatan ban shiga lokacin hutawar ba ko?sahla ta faɗa cikin sigar  jan hankali,tana kurawa hallitar shi idanu,sanya yake da wando light blue dai dai gwiwa da ƙaramar rigar marar hannu mai sharar shara itama light blue,ji take tamkar ta kwanta a jikin shi ta rungume shi ko ta rage abun da take ji game da shi.

Kusan minti biyu shiru baice komai ba domin kamshin turaren nata yana shigar shi soai yana kuma tasiri wurin fuzgar shi kamar yadda suka shirya hakan,wanna dalilin ne kawai ya hana shi cin mutuncin ta,

Zama tayi daga ɗaya daga cikin kujerun ɗakin dake gefen shi tana kallon inda yake"Haba ya Azhar tamkar baka gani niba,ko kallo na kasa samu a wurinka balle jin muryar ba,ko bakayi murna da zuwa na ba?.

*MRS NOOUR CE*🥰

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 08, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƘARSHEN ALEWA ƘASAWhere stories live. Discover now