Page 14

27 0 0
                                    

❤❤❤❤❤❤❤❤

     *MATAR ABDALLAH*

        ❤❤❤❤❤❤❤❤

_(A Love Story)_

_*Daga Alk'alamin 🌹Shatu🌹*_

                *Wattpad:Shatu70*

~*Wannan littafin sadaukarwa ne ga Jamila Umar (Janafty)san so fisabilillahi*~

_Dedicated to Aysha Alto_

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_

_*70 to 75*_

            """""""""Cikin amincewar ubangiji jikin Kawu Sageer ya na ta samun sauk'i domin ya na samun kulawa yanda ya kamata saboda kud'in da Abdallah yake kashewa gurin ganin ya samu lafiya domin duk wani wanda yake da alak'a da Amrah to ya na da muhimmanci agurin Abdallah shiyasa ya tsaya kai da fata gurin jinyar Kawu Sageer d'in kuma alhmdllh jiki ya samu sauk'i, ganin Abban Salma ya na samun lafiya kullum sauk'i samuwa yake shine ya saka Mama Hindatu barwa Salma kula da Abban nata ita kuma take yawan ta son ranta.

Yau ma kamar kullum Salma ce a asibiti gurin mahafinta ya na daga kwance ita kuma tana kan kujera kallonta yayi yace;  "Salamatu ko zaki kiramin Zainab ne naga yau tun safe shiru babu ita babu Amratu ma ina so nasan wane hali suke ciki dan tabbas akwai abinda yake faruwa tinda d'azu ma sai da yaron nan Abdullahi yazo neman ita Amrah d'in".

'Yar k'aramar wayarta k'irar tecno ta fitar tare da danna kira a number Ummah tana fara ringing ta mik'awa Kawu karb'a yayi dai dai lokacin kuma Ummah ta d'auki kiran.

"Assalamu alaykum".

"Wa alaykumu salam Zainab".

"Na'am yaya ya jikin naka?".

"Jiki alhmdllh nace dai lafiya kuke? naga yau bake babu Amratu saima yaron nan Abdullahi da yazo nemanta".

"To yaya lafiyar dai ita tayi kad'an domin gamu a asibiti Amrah ce tsautsayi ya afkamata a hanyarta na kawo maka abinci safe yanda mai mota ya bigeta, amma kuma babu wani babban rauni sai d'an buguwa da tasamu a k'afofinta kuma yanzu hakama likita ya bamu sallama zamu wuce gida".

MATAR ABDALLAHWhere stories live. Discover now