Chapter 7

1.7K 175 34
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     *LAYLERH MALEEK*

  *Writting By*
Phatymasardauna

                            *Wattpad*
                   @fatymasardauna

#Fantasy

                   *Chapter 7*

Sauƙe idanunsa da yayi akanta ne yasa duk  tsikar jikinsa mimmiƙewa, take yaji wani sabon yanayi ya ziyarcesa, numfashi ya fesar tare da soma yawo da  idanunsa akanta baya ko ƙiftawa.  
Ɗago ɗara ɗaran kyawawan Idanunta tayi, wanda  hakanne ya bawa  eye balls ɗinta daman sauƙa acikin nasa idanun.    
Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarceta, cikin sauri ta janye idanunta  tare dayin ƙasa da kanta, hakanan taji duk tazama wata iri. Ahankali tasake yin ƙasa da idanunta, tare da kawar da kanta gefe. Cikin yanayin sanyi ta ƙarasa shigowa cikin falon, tare daɗan durƙusawa cikin sassanyar muryarta tace.
"Abbu barka da yamma."       Murmushi Abbu yayi tare da cewa.  "Yauwa Laylerh ya school ɗin?."     ɗan murmushi tayi ahankali ta ce.  "Alhamdulillah."  
Idanunta ta ɗaga tare da ɗan kallon Alhaji Ahmad Rufa'e wanda tun shigowanta fari'ar dake kwance akan fuskarsa ta ƙaru.    Cikin yanayin ta na nutsuwa tace.  
"Ina yini."   
Sake faɗaɗa fari'ar dake kwance akan fuskarsa yayi, murya asake yace.  "Lafiya ƙalau Laylerh ya karatu, ana nan anata fama ko?."  
Kai ta jinjina masa alaman "Eh." still har yanzu fuskarta ɗauke yake da murmushi.
Kallon Abbu Alhaji Ahmad Rufa'e  yayi cikin yanayin jin daɗi yace.  "Masha Allah Alhaji Jaheed Laylerh ta girma, wancan zuwan nawa fa tana ƴar ƙarama da ita, dan in ban manta ba lokacin shekarunta  11 ko."  

Murmushi Abbu yayi, tare da jinjina masa kai, cikin dattako yace.
"Ae kasan girman ƴa mace babu wuya."             
Shiɗin ma Alhaji Ahmad Rufa'e'n murmushi yayi, dan tabbas ko maganan da Abbun ya faɗa haka ne.

Laylerh da duk taji ta kura ɗan muskutawa kaɗan tayi, tare da sakeyin ƙasa da idanunta, hakanan takejin wani iri ajikinta, gashi jikinta na bata cewar ana kallonta.                                

Najeeb ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan lumshe idanunsa, wanda tun shigowarta suke aikin kallonta basa  ko lumshewa, hakanan yaji wani diffrent feeling akan yarinyar, duk da kasancewar tana da ƙananun shekaru, amma ya lura tana da abubuwan burgewa da yawa ajikinta, sosai kuma ya karanci yanayinta, cikin zuciyarsa yake maimaita sunan da yaji Abbu ya ƙirata dashi wato "LAYLERH". 
"Nice name." Ya faɗa batare daya bari sautin muryarsa ta  fito fili ba, saidai laɓɓansa da suka ɗan motsa, baisan meya saba har yanzu ya kasa ɗauke idanunsa akanta.      

Bazata iya jure zaman wajen ba, musamman yanda taji tsikar jikinta na zubawa,  miƙewa tsaye tayi  domin ayanzu ba abun da takeso kaman ganinta aɗakinta, dan ko tantama batayi, kasancewar taji ajikinta cewa ana kallonta.             
Ganin Laylerh'n ta miƙe tsaye ne yasa Abbu cewa.  
"Laylerh baki ga Yayanki Najeeb bane? kigaishe sa mana."     

Jin Maganan da Abbu ya faɗa ne yasa akaro na biyu ta ɗago kyawawan idanunta ta kalleshi, kasancewar tun ɗazu idanunsa akanta yake, shiyasa idanunsu suka faɗa  cikin na juna, saurin sadda kanta ƙasa tayi tare da kama ƴan yatsun hannunta ta shiga murzawa, cikin muryarta dake cracking tace. 
"Ina yini."   
Akaron farko kenan daya  janye idanunsa daga gareta, cikin son samawa kansa nutsuwa yace.  "Lafiya."    
Jin sauƙar muryarsa acikin kunnuwanta ne yasanya ta sake ɗago kai ta kalleshi, wani abu da ta tuna ne yasa ta ɗauke idanunta daga kansa, tare da miƙewa tsaye cikin yanayin nutsuwarta ta nufi ɗakinta, kasancewar ta ɗebo gajiya amakaranta shiyasa takejin kanta nayi mata ciwo kaɗan kaɗan.     

Ta gefen idanunsa yabita da kallo,har  ta shige wani ɗan corridor dake cikin falon, wanda anan cikin corridor ɗin ɗakinta yake,  ganin ya daina ganinta ne  yasa shi ɗauke kansa daga kallon hanyar da tabi.                     

LAYLERH MALEEK Where stories live. Discover now