sadikgg

Assalama Alaikum Warahamatullah Wabarakatuh. 
          	
          	Mutanena da ke wannan dandali na wattpad, ina farincikin sanar da ku cewa, na fara sakin sabon littafina mai suna TA ZAMA HAJA!
          	
          	Ku kasance da ni tare da yi mini sharhi da fatan alkhairi daga farko har zuwa karshen labarin. 
          	
          	Na gode sosai. 
          	
          	Sadik Abubakar. 

sadikgg

Assalama Alaikum Warahamatullah Wabarakatuh. 
          
          Mutanena da ke wannan dandali na wattpad, ina farincikin sanar da ku cewa, na fara sakin sabon littafina mai suna TA ZAMA HAJA!
          
          Ku kasance da ni tare da yi mini sharhi da fatan alkhairi daga farko har zuwa karshen labarin. 
          
          Na gode sosai. 
          
          Sadik Abubakar. 

sadikgg

Assalama alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuh. 
          
          'Yan uwana abokan arziki maza da matan alkairi sannunku da hutawa, sannunku da jumirin karance-karancen littattafai musamman na "Adabin Hausa".
          
          Ina mai farin cikin sanar daku cewa zan fara sakin sabon littafina, bayan dan gajeren hutun da na tafi sakammakon kammala rubuta labarin *MATAKIN NASARA*.
          
          Insha Allahu zan fara sakin sabon labarin da na yiwa lakabi da *ƘUDA BAKA HARAM* a ranar *17, GA watan Rajab 1442H,* wanda ya dace da *1, ga watan Maris, 2021M.*
          
          *ƘUDA BAKA HARAM* Kirkirarren labari ne na wani ma'aikacin damara mai halin dan akuya da kuma salahar matarsa, wacce Allah ya sanya jarabawarta ta kasance zama da wannan kaddararren miji. 
          
          Akwai dimbin darussan da zamu karu dasu a cikin wannan labari, fatana Allah yasa abin da zan fada ya amfanar dani, ya amfanar daku. Kuskuren da zan yi ina rokon Allah ya yafe min, ya yafe muku kuma da kuka karanta. 
          
          Kofata a bude take wajen karbar gyara, shawara, ko kuma korafi.
          
          Ga email dina : insado26@gmail.com

sadikgg

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ 
            ━━━━༺۵༻━━━━
          
          Ƙagaggen labari ne na wasu tagwayen 'yan mata da suka tashi cikin ƙunci da talauci, tun daga ƙuruciyarsu har zuwa lokacin da suka girma. 
          
          A wani lokaci sun kasance riƙe da akalar ciyar da kansu tare da iyayensu, sakammakon cutar tsinkewar laka (spinal cord) da ta samu mahaifinsu.
          
          Yara ne kyawawa ƙananu ɗanyu sharaf amma sun gamu da aikin bauta, aikin kamfanin barkono ko citta, da wannan aiki suke samun abin sakawa a bakin salati. 
          
          Bayan duhu sai haske, inji Hausawa, daga ƙarshe rayuwarsu ta sauya bayan matakin haƙuri da addu'a da suka lazimta, kowacce tayi babban kamu na auren ɗan millionaire. 
          
          Akwai ɗimbin saƙonni masu muhimmanci da me karatu zai ƙaru dasu cikin wannan labari.
          
          
          Ku kasance da wannan gida domin jin wannan muhimmin labari daga farkonsa har ƙarshensa. Ƙarfe 8:00pm zuwa 10:00pm na dare, daga ranar *14th ga September, 2020* zan fara posting. 
          
          
                          *Sɑdik ɑbubukɑr*
          
          Wɑttpɑd @sɑdikgg 
          
          Nagode.