*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Free book_*
*_5-6_*
_Kullum saina fada wannan book din Free ne comment kawai nake buqata OUM HAIRAN PALACE 1 Bakwa comments wlh daga wannan page din idan baa gyaraba zan daina yimuku post kwake gani a moqota Ina gdy OUM HAIRAN PALACE 2 inayinku Allah yabar qauna kuci gaba da zuba comments nikuma zanci gaba dayi muku typing._
Kallonsa takeyi cikin tsananin ta'ajibi tace "me hakan yake nufi?" Bude idanunsa yayi da suka kada sukayi red ya motsa dan qaramin bakinsa tare da qanqantar da qananun idanunsa yace "like feels...." Gabanta yabada wani ras ta cije lebe tare da bude motar ta fita shima ya fito yana gyara hularsa ya bude but din har tayi masa nisa ya Kira wasu samari da suke qoqarin giftashi ya nemi alfarmarsu suka daukar Masa kayan suka bita jin alamun ana bintane yasata tsayawa ta juyo kawai sai ta ganshi sauke da kaya niqi² ta dan bata fuska tace "meyesa kake haka bana buqatar qarin komai Mr Ja'afar Wakil Ina da komai enough...." Saukar hannunsa a bakinta ne yasata daga qwayar idonta ta zubashu cikin nasa shima nata idon yake kallo ya qara yalwata murmushinsa dimple dinsa ya lotsa farar fatarsa ta fulanin azare da ta hadu da hutu sai glowing takeyi yace "duk abinda nayi niyya baa dakatar dani Ja'afar Wakil baison sorry please baison...."
Shiru yayi yanaci gaba da kallon qwayar idonta ta sauke numfashi qamshin turaren hannunsa yana ratsa hancinta ta sanya hannunta ta dauke nashi inda matasan suka ajiye Mata kayan a daidai qafarta ya zaro kudi me auki ya Basu sukayi godiya suka tafi jan hannunta yayi yayi kissing nashi ya juya da sauri yabar gurin ya barta da sanyayyiyar gwiwa mamakin lamarin mijin aminiyar tata takeyi gabadayansa ta kasa gane inda ya dosa tun ranar dinner take tuhumar kanta me wasu abubuwan da ya rinqayi suke nufi amma ta kasa ganewa,
Tabe baki tayi ta debi kayan ta shiga ciki zama tayi a bakin gadonta ta fara bude kayan daidai lkcn da Nina wata abokiyar karatunta ta shigo ta zauna a kusa da ita tace "kay Hajiya ta kina wanke garori fah wannan hadadden guy din fah Ina kika samoshi?" Tsuke fuska tayi tace "ke banson iskancinki fah mijin Bestie nane wlh" zaro ido Nina tayi tace.
"What wanne irin mijin aminiyarki me ya kawoshi gurinki?" Yarfa hannu tayi tare da tabe baki tace "nims bansani ba wlh nayi tunanin daurin aure yazo ko wani Abu amma na tambayeshi yace takanas danni yazo"Jinjina Kai Nina tayi tace "na dade Ina kallonku fah ni wlh na dauka saurayinki ne Amma gsky akwai alamun tambaya a cikin kallonsa gareki Kuma fah shi namiji bayada tunani wani lkcn lissafinsu na abinda yayi musune basa lissafin meye zaiyi daidai da tunanin dan' adam nifa na hango wani Abu a qwayar idonsa Pretty anya bazaki dakatar dashi ba"
Numfashi taja ta sauke tace "ni kaina yasani a compus inata tunanin abubuwa mabambamta Amma idan na tuna wayeshi kuma na tuna alaqar dake tsakanina da matarsa da irin soyayyar da sukayi ta one month before aurensu sai na qaryata zuciyata nakan dauki abubuwansa a matsayin son farantawa bestie na tunda yasan cewa bata da farin cikin da ya wucce taganni cikin farin ciki wannan dalilin yasa nake qaryata mind dina Nina Ja'afar Wakil bazai aikata abinda zuqatanmu suke fadi mana ba kawai dai shidin haka yake meson damuwa da damuwar wani" a kusan tare suka sauke numfashi Nina tace "Uhm to! Da wannan don wannan Amma dai gsky kiyi takatsantsan Rafi'ah ni na hango abinda ke baki hango ba" da wannan suka fara duba kayan tayi murmushi tace "gashi kuwa ya iya siyayyar Mata bari na Kira Bestie na nasata tayi masa gdy" saurin dakatar da ita Nina tayi tace "idan kikayi haka zaki iyafa sosa zuciyarta kinsan ita batada qashi" harara ta galla Mata tace "ashema ba Bestie din nawa bace ai bazataji ko ta kawo komai ba kuma bari kiji"Wayarta ta fito da ita ta latsa number Ni'imah bugu biyu ta daga tace "My Bestie yanzu sweet yake cemin yazo ya kawo miki ziyarar bazata" ajiyar zuciya ta sauke tace "eh wlh yanzu bai dade da tafiya ba kawai sai naga Kira unexpected na daga yace nazo na sameshi a two park Ina zuwa naganshi naji dadi sosai sai naji kamar ke nagani"
Murmushi tayi tace "inanan inata fama da tunaninki sai yanzu na samu nutsuwa gashi zamu wucce Abuja baki dawo ba" jikinta ne yayi sanyi taja numfashi tace "kiyi hqr Bestie kina Raina banzaci zan dade hakaba a school so kinsan karatun namu sai a hankali Amma nayi Miki alqawarin indai na dawo hutun section zanzo har Abujan nayi Miki sati guda" wani ihu Ni'imah tayi tace "amma dakin burgeni kinsan me?" Girgiza Kai tayi tace "aa saikin fada" dariya tayi tace "sweet ya dameni da mgnrki kullum sai ya tambayeni wai bakida tsayayyen saurayine da bazakiyi aure ba idan nace masa bakya kula samarin ne sai yacemin Wai to ko bakida lfyne nace masa qalau kike ya Kuma cemin Kuma idan kika samu mijin zakiyi sure Niko nace masa to ko yana cikine wannan tambaya haka"

أنت تقرأ
MY BESTIE'S HUSBAND
عاطفيةMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...