MY BESTIE'S HUSBAND

1.9K 104 14
                                    

*_My Bestie's Husband_*



*_Ummuh Hairan_*


*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_Dedicated to Real Smasher_*
_Ina gdy da kulawarki gareni Allah ya qara ilimi me amfani😍_


*_19-20_*

____________________________
____________________________

Tunda suka dawo gidan mutanen gdan suka hadu a kanta suna aikin rarrashinta yin duniya taqiyin Shiru Koda tayi niyyar yin shirun idan ta tuna da furucin aminiyar tata ta Kuma tuna da cewa yanzu fah da ita da aminiyarta duka sunan matan mutum daya suke amsawa sai taji sabon kuka ya qwace Mata qarshen qarshema zazzabi ne ya rufeta ba qaramin artabu sukayi da Abba ba sannan ta daina furta zata kashe kanta yajata yakaita daki kamar wata qaramar beby ya kwantar da ita ya rinqa bubbuga bayanta har bacci ya dauketa sannan ya tashi ya fita.
Dakinsa ya shiga ya Kira wayar Dad ya daga suka gaisa yace “Haba Sabo meyesa kayimin haka don Allah banji dadiba wlh duk da na matsu naga Rafi'ah ta fitar da miji Amma ai ba irin wannan matsuwar da zaa kasa duba alaqa ba yanzu ga abinda wannan auren ya janyo daga ita har Ni'imah babu me hayyaci ita tanata kukan bataso saita kashe kanta kota kashe Ja'afar ita Kuma Ni'imah tana zargin da sahalewarta akayi wannan auren Sabo wannan bayyananniyar cin amanace fa da kowa zai shaida...."

Katseshi yayi da cewa “meyesa zaka tsuke tunaninka ka rinqa tunani irin na Mata Alh Nuhu Ni dama na dade da fahimtar hakan zata faru Ja'afar yanason Rafi'ah tunkan ya auri Ni'imah da an qara jinkiri baayi gaggawar hada aurensa da Ni'imah ba qila da Rafi'ah zaigani ya zaba to Amma Allah ya hukunta dukkansu matansa ne saboda haka muyi Shiru kawai mu karbi abinda Allah ya zartar Ni'imah ai ba ita tayi kantaba naji duk haukan da taje tayi muku wlh akan lamarin nan zan iya cin mutuncinta indai bata nutsu ta fahimci abinda ke gabanta ba bandama shirme irin nasu na Mata da yaje ya dauko Mata bare ta girgijeta ai gara ya auri aminiyartata babu wani cin amana a auren sunnah dukkansu matansa ne haka Allahu ya tsara to mubi kawai muyi Shiru"
Sosai Alh Sabo ya rinqa tausar Abba da kafa masa hujjoji hardai ya rusuna ya karbi abin tare dayi musu fatan alkhairi Amma yana Jinjina yanda zaman zai kasance shi tausayin ma Ja'afar din yakeyi har gara Ni'imah qila ta tausu ta dadi Amma Rafi'ah tanada wuyar sha'ani akan abinda ta yarda aranta ba daidai bane"

Bangaren angon Ja'afar kuwa da Ni'imah tunda yaje gida ya haye samansa yanada dan qaramin clinic a cikin bangarensa ya fara dressing din hannunsa ya yanku sosai amma baiji haushi ba saima murmushi da yayi yace “zan saitaki ne Rafi'ah wahalar dama zamowarki tawa tunda kin zama ai asiri ya rufu" yana wanke ciwon yana cije lebe har ya gama ya koma ya kwanta yanajin zugin hydrogen din ya jima a kwance sannan yaji alamun shigowarta saman ta hau ta kalli qofar a rufe ganin hakan yasata fara dukan qofar da dukkannin qarfinta tana cewa.
“Tunaninku zakuci amanata ku hutane qarya kake Ja'afar Wakil tabbas baka fara shiga damuwa ba wlh ka zubar da farin cikinka tunda kaci amanata macuci mayaudari maci Amana azzalumi, Ashe dama abinda yasa kullum bakada Hira saita Rafi'ah kenan Ashe da gaskene saqon da aka taba turomin cewa kullum sai anganka a makarantarsu ka dauketa ni Ina tunanin saboda nine macuci Ashe kanka kake ginawa to wlh dole ayi dayan biyu dole ka saki daya cikinmu domin baa fada daya sarki biyu Ja'afar ka budemin ka fadamin laifin da nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...."

Yanajinta yayi Mata banza tayi bugun duniya yaqi budewa zagin duniya tayi masa ya shareta saboda dama ya shiryawa zuwan wannan lkcn baizaci ma haukan nata zai tsaya iyanan ba a yanda ko a Hira take nuna masa ita zata iyayin komai akan kishiya, yanajinta ta gaji ta zube a gurin taci gaba da kukanta tana cewa “Allah dama mafarki nakeyi na bude idona naga ba gaske bane Allah ka mayarmin dashi tunani na shaidan Allah bazan daukaba wlh kasan bazan daukaba bazan iya zama da Bestie na matsayin kishiya ba Allah ka kashe wannan azzalumin Ja'afar na huta Allah ka hada hardani  nikam na shiga ukuna Allah...."
Maganganu takeyi kamar zararriya yanajinta yaqi budewa saboda shi kansa zuciyarsa a cunkushe take bada damuwar Ni'imah ba aa damuwar halin da Rafi'ah take ciki shine yake addabarsa gashi Kiran duniya yayi taqi dagawa ya tura Mata saqo taqi replying dabara ce ta fado masa ya Kira number Ammi don dama tun ranar data kirashi tayi masa warning yayi saving ring biyu ta daga da sallamarta ya amsa tare da cewa “Ammi barka da Rana" jin muryarsa yasata hadiyar wani takaici Amma dake dattijuwa ce saita dake tace “lfy Ja'afar ya gdan"
Shiru tadan ratsa kafin ya ja numfashi yace “inata Kiran wayarta taqi dagawa Ammi Allah yasadai lfy?" Iska ta furzar tace “yo wanne lfy Ja'afar dama kanasonta da lfy ne ai da sauqi ma da bata hadiyi zuciya ba tanacan tana fama da zazzabi" miqewa yayi zaune yace “ya Salam bari nazo na dubata" yana fadin haka ya kashe wayar ya tashi shi kansa idan zaa dubashi din so yake bai Saba da tashin hankali ba shi tashin hankali fitar dashi a hayyaci yakeyi.


MY BESTIE'S HUSBANDWhere stories live. Discover now