1

430 35 1
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*MUTANEN K'ARANGIYA GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻😝*

*Lamba ta 18*

Da tsallen jin dad'i ta shiga gidansu sai wasar Baki take yi, Inna ta bita da kallon mamaki wadda ta fita tana kuka yanzu kuma itace ta dawo tana wasar Baki, aiko sai da ta zauna daf da Inna sannan ta kwanta saman cinyarta tana rufe ido da tafukan hannayenta, Inna ta shafo dunbujen tulin gashinta da kullum ba'a wuce yi mata tsoro hudu a saman Kan nata, saboda bala'in jin zafin kitso ne da ita gashi gashin a cikenshi yake da kuma tsawonshi tubarakallah, don ko shartar gashin za'a yi mata idan an kwance sai duk makota sun sheda, saboda kururuwar da zata dinga yi tana kukan wayyo ita zafi, shiyasa kullum kitsonta tsoro hudu ne  don ko shi d'in sai Inna ta ajiye bulala  a gefe sannan ake yinshi tana kuka har da su majina shabe shabe, saboda in ta kawo mata reni kai tsaye ta ke mazgarta da bulalar, shiyasa in dai har ranar kitson ta zagayo to ko Baffah dole ne sai ya siyo mata wani Abu a matsayin cin hanci don kawai a samu ta natsu a yi kitson lami lafiya, amman da ta canye abun sai a koma tarxomar da aka saba kullum.

Tana shafar gashin kan nata tace,. "Yau kuma me ya saka 'yar Baffah farin ciki irin haka??, Ke da kika fita da kuka to me ya sakaki wannan murmushi da kike ta yi?"

Dije ta tashi daga kwancen ta rufe fuskarta tace,. "Inna mun shirya da D'anbirni har ma ya yi man alk'awali zai sakani Makarantar Likitoci in dinga yiwa mutane allura"

Inna ta zaro ido waje tace,.  "Au kin amince zaki aureshin yanzu??"

Dije ta rufe fuskarta alamun jin kunya tare da d'aga kanta, Inna ta bita da wani kallon yaron man kaza tace

"Kina sonshi kenan?"

Dije ta mik'e da sauri zata shige d'aki tace,.  "Ni WALLAHI fa bana sonshi amman zan aureshi saboda ya kaini Makarantar koyon Likitanci"

Har zata shige ta dawo baya tace,. "Kin ga shikenan Ni sai in dinga yiwa mutane allura ba har sai an tafi zuwa birni ba"

Inna ta maka mata harara tace,. "To sai aka ce da ke in har kin aureshi a nan garin zai zauna da ke ko?, to bari kiji garinsu nisa ne dashi ke asali ma sai anyi kwana biyu ana tafiya kafin aje cen d'in, kin ko ga Baffahnki ba zai tab'a bari ki yi auren ba saboda nisan da ke tsakaninmu da su"

Dije ta dawo tare da kumbure fuska tana dire diren kafa tana fad'in,.  "Ni WALLAHI Inna ina son in zama Likita don ALLAH ki ce da Baffah ya barni in aureshi don ALLAH"

Aikuwa caraf sai ga kunnen Baffah da ke shigowa tare da Usman, cike da mamakin abunda ya jiyowa kunnenshi ya k'araso idonshi akanta yace,. 

"Me naji kina fad'a ne???"

Dije ta isa wurinshi da sauri ta rik'o hannunshi tana share yan guntayen kwallar da suka zubo mata tace,.   "Baffah D'anbirni yace dani idan na aureshi zai sakani Makarantar likitoci in zama babbar Likitar Mata don ALLAH ka barni in aureshi WALLAHI ina son zama liktanya Baffah don ALLAH kaji?"

Ta k'are maganar tare da d'aga kanta ta kalleshi cikin marairecewa, Baffah ya k'wace hannunshi da ta rik'e ya tureta gefe ya wuce yana fad'in

"Ke wace irin yarinya ce da kullum shirmenki k'aruwa yake yi? Sai ana murna anga sauyi sai kuma ki k'ara tsunduma ruwa? To bari kiji ni zan ganshi da kaina in sanar dashi cewa ba Zan bashi ke ba, tunda har baiji kunyar zaunar dake ya sharara maki wannan k'arya ba, ke kuma da yake ba wayau ne da ke ba kika amince da zancenshi na yaudara, to WALLAHI na sake jin ma kin tsaya da shi kunyi magana sai kinsan d'anjaki dukiya ne, tunda ke kwakwalwarrki bata hasko komi sai shirme mara tushe bale makama, ke Makarantar ma kin daina zuwa daga yau sai nagani in akwai wanda ya isa yasa ki koma"

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now