72

556 39 6
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*ALHAMDULILLAH!!!! ALHMDLLH!!! ALHMDLLH!! GIDAN AURE shine sunan book ɗina da zanyi a gaba, wadda take buƙata zata biya kuɗinta 300 kacal ta hanyar transfer ta wannan account ɗin HADIZA D AUTA 1230094555 access Bank, idan kuma kati ne zaki turo aritel ko mtn na ɗari uku to za'a turo ta wannan numbar 09032685442*

*Ƴargata Maman Sultan Ubangiji ya baki lafiya yasa kaffara, Mrs Naseer ina miƙo gaisuwata zuwa gareki akan namijin ƙoƙarinki ga book ɗina, my Ambash ALLAH ya saukeki lafiya mu zo mu ci rangyem, Asma'u Umar  ki yi haƙuri na goge laifina🤗*

*Lamba 72 last page*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Baffah yana murmushin jin daɗi ya ce "Ameen Dijengalata amman fa ko haka aka tsaya Alhamdulillahi, don ba abunda za mu ce wa ALLAH sai godiya ALLAH ya sawa aurenmki albarka ya baku zaman lafiya ke da Mijinki da abokiyar zamanki duka, kuma ya baki ƴaƴa nagari masu albarka waɗanda zasu yi maki fiye da abunda kinka yi muna na alkhairi"

Dije sai "Ameen Ameen" take faɗi zuciyarta cike da jin daɗin samun iyaye nagari, sai da suka ɗan taɓa fira sannan ta dawo falon Inna suna cin abincin ana ci gaba da fira cikin raha da barkwanci.

Kwanansu Zee ɗaya direba ya kwashesu suka suka koma suka bar su Inna da kewarsu tare da jinjina lamarin Ubangiji, ganin yanda dukansu daga Zee har ita Fiddon sun saki jiki da su kamar cewa daman cen ƴan'uwan juna ne.

Bayan su Inna sun dawo daga rakiyarsu ne Hansai ta goye Sayyid ta yi ɓangarenta, Dije ta faɗa kujera tace

"Wash ALLAHna WALLAHI Inna gaba ɗaya jikina ciyo yake yi"

Inna ta zauna tana ƴar dariya ta ce "sai kin yi haƙuri kam don yanzu jikinki yake haɗewa daga ɗaukar ciki da haifuwar da kika yi, wani zubin ma har zazzaɓi wasu su ke yi a wannan lokacin"

Dije ta dafe goshinta ta ce "ai kam dai nima ina jin abinda nike ji a jikina"

Inna ta kalleta da kyau sannan ta ce

"Naji daɗin yanda yarinyar nan ta sauko kuka fahimci juna ga shi yanzu zamanku gwanin burgewa"

Dije ta yunƙura ta ta shi zaune sannan ta kalli Inna ta ce "kin dai gani Inna ga shi yanzu kamar ba'a yi ba ashe da kirkinta sharrin sheɗan ne da kuma mugun kishin Abban Sayyid da take yi"

Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce "duk macen duniya dole zata yi kishin mijinta, ke ba mijinta kawai ba duk abunda kake so a rayuwa dole ka yi kishin ganin wani ya raɓeshi, sai dai na wani ya fi wani don kowa da kalar dauriyarshi, shiyasa kika ji na ce da ke duk runtsi ki sa ya dawo da ita a matsayin matarshi, saboda ko da ta fita dole ne ya auri wata, kuma ita zata iya shigowa gidan da shirinta ƙarshe ma ta janye maki Mijin ya koma gareta a barki da cizon yatsa, amman in ita ce sanadiyyar wannan abun da ta aikata zai dakushe mata karsashi akan ko ma aikata wani mummunan abu saboda ganin igiya ɗaya ce ta rage a tsakaninsu, saɓanin wacce zai auro ba ita, don ba lalle bane ba ace ku fahimci juna, bale kuma ta barki ki ji daɗin zama gidan aurenki ko zama da  Mijinki lafiya, don wata mace sharrinta ko sheɗan ya sarawa bala'in da ke tattare da ita, amman yanzu kin ga komi ya zama tarihi kuna zaman lafiyarku Masha Allah, wanda  hakan da kuke shi zai ƙara farantawa mijinku rai ya ji daɗin kyautata maku"

Dije ta cire tagumin da ta yi ta ce "Lalle Inna na yarda da aka ce abunda babba ya hango yaro ko da ya hau sama bazai iya hangowa, kuma naji daɗin biyayyar da na yi wajen sakashi dawo da ita, yanzu ga shi abun Ni ma ya zamo mani alkhairi don baki ga yanda ta ke son Sayyid ba, bata bari ya zauna hannuna matukar ba abincinshi zai sha ba, kuma ina bashi take sake karɓeshi su tafi, shi kanshi Abbanshi sanadin wannan halin kirkin da take yi ne yasa ya sake mata sosai suna ɗasawa, sai dai wani lokacin ina jin ba daɗi idan naga yana kulata Inna, Amman idan na tuno da cewa itama fa Matarshi ce kamar Ni sai in baiwa zuciyata haƙuri don bana son ta fahimci ina jin zafinta"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 21, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now