chapter 33

450 73 12
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

33🧝🏻‍♀️
Kallon shi yayi cikin rashin fahimta yace "aure kuma zayd? A irin wannan lokacin?.......Wani abu ne ma yasa kaji kana sha'awar yin aure bayan kasan matsalar da kake tattare dashi"

Gyara zama yayi ya fuskanto shi yanda zai fahimce shi sosai in a serious tone yace
"Yaya nifa ɗan adam ne kuma ajizi, bani da lafiyar ruhi amman ina da lafiyar jiki dole watarana nima naji ina buƙatar yin aure, shekaru na 28 fah dan Allah ka duba lamarin nan a san yanda za'a yi"

Murmushin takaici sulaiman yayi yana girgiza kai, ya rasa me yasa zayyad ya girma amman kuma bayi da tunani kullum shi kenan ayi ta maimaita mishi magana ɗaya kaman karatu?

"Remains only 2 years, shekaru biyu kacal suka rage mana da sun cika bama sai da izini na ba zaka auri ko mata 4 ne kake so a lokaci ɗaya, kayi haƙuri na shekaru masu yawa na 2 yrs sai ya gagare ka? zuwa lokacin kaima kana da naka abin da zaka riƙe su dashi na gashin kanka ba sai ka roƙa an baka ba kuma babu wani tsoro ko fargaba a tare da kai bayan wannan lokacin idan Allah yaso ma zaka iya samun lafiya ka warke tangaras, domin duk inda ya kamata mu shiga mu fita zamu je a nima maka lafiya ba tare da damuwan rasa komai ba, ka haƙura ka ajiye wannan batun Please"

"Amman yaya ba zata iya jira na har zuwa lokacin ba..."

"Then just let her goo!! Let...her..go!" Binshi kawai yake yi da ido ya lura bai san girman abinda yake shirin saka shi aikatawa bane, saudat tayi tsiron da ba za'a ce ya cire ta cikin zuciya na kuma ya iya aikata hakan ba,

Ya tashi daga zaunen da yake ya ɗauki babban rigan shi a hannu ya zuba wayoyin shi a aljihu yana son tafiya don bayi son su ja maganar kada ranshi ya ɓaci daga ƙarshe cus so much is already going in his mind,

"I believe ko a wuni ɗaya kayi deciding auren wata macen bayan ita za'a iya kammalawa kafin dare a kaita ɗakin ka tunda kuɗi ne yake yin aure just let her be ko ita waye kuwa koda Sulthana ce ka rabu da ita zaka samu wacce ta fita"

"Ba Sulthana nake son aura ba..."

"Koma waye kace ta jira idan ba zata iya ba ta ƙara gaba, kada kabi na mata zasu saka ka rasa komi naka ba tare da ka shirya ba, ni zan wuce gidan umma na gaida su"
Da faɗan haka ya fice abunshi ya bar zayyad cikin jimami, bayi da wani zaɓin da ya wuce yabi umarnin babban yaya a yanzu idan ba haka ba kuma saɓa mishi zai iya jawo babban ɓaraka a tsakanin su kuma ba zai taɓa bari hakan ta faru ba,

Shima ɗaukan nashi babban rigan yayi yana gani ana setting dining don cin abinci yayi shigewar sa ɗaki dan bayi jin zai iya saka ma cikin sa wani abu,

Cire rigan jamphan shi kawai yayi ya ɗauki waya ya kira saudat.....

  *****
"Kai aunty Aisha ta daina fah, arba'in ɗinsu da saura ina zata je a......." magana ta ne ya katse saboda ruri da waya na ya ɗauka na bishi da kallo tare da ɗauka ina duba mai kiran sunan zayyad na gani kasa picking nayi na barshi ya yanke a take wani kiran ya sake shigowa,

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now