💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗Page 3
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number +234 803 238 4602 alert domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
...A matukar firgice ta farka daga nannauyen baccinta tana zaro idanuwa dafe da gefen fuskarta inda taji saukar mari "are you mad what are you doing ? " yayi maganar a fusace yana zaro mata kyawawan idanunshi , take jikinta ya ɗauki rawa "uban wa yace kiyi changeover ?"
"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta shiga furtawa a zuciyarta tana maimaitawa kafin a hankali ta yunkura ta mike tsaye tana duban inda yake tsaye kikam hannunsa rike da yar saman suit d'insa, Kana kallonta zaka gane irin tashin hankalin da take ciki a lokacin, dan gabadaya fuskarta cike take da matsanancin tsoronsa , babu abinda take ganewa a tun sanda ta buɗe idanunta akanshi baya ga fuskarsa da kayan dake sanye ajikinsa .."
Take Jikinta ya sake ɗaukar rawa sakamakon irin kallon iskan da yake jifanta dashi , yayinda zuciyarta ke dokawa da matsanancin karfin gaske , da sauri ta durkushe a gabansa tare da haɗe hannuwanta duka "dan girman Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure , karka dakeni nayi maka alkawarin bazan sake ba "..
ya zuba mata kyawawan idanunshi kawai yana kallonta "kayi hakuri nasan cutar da kai na sakaka cikin damuwa nasan wannan kadai zai ......."
"Shiiiii........" ya d'aura yatsansa ɗaya akan lip's d'insa " karki sake na sake jin sound d'inki anan "kin jawowa kanki dan babu ruwana da wani banzar hakurinki dan sai jikinki ya gaya miki ya ajiye rigar hannunsa a kan kujera ya soma ƙoƙarin sunce belt din jikinsa " shegiya har da wani cewa kar dakeki gaki yar gwal ko ?" zaki yadda zanyi dake gobe idan nace ga yadda nake son tsarin gidana haka zaki bi ,tana ganin ya kusan gama sunce belt din kugunsa ta kwasa aguje ta haye sama tana ihu dan tasan mai kwatarta a hannunsa sai Allah bayanta ya biyo taku uku yayi ya samu nasarar hard'e kafarta ɗaya ta fadi akan step , yasa kafarsa ya take mata kafafu ya shiga zuba mata belt tana ihun Kiran sunan iyayenta "wayyo Allah na shiga uku wallahi bazan sake ba ! bazan sake ba!! kayi hakuri bazan sake ba karka kasheni dan girman Allah ka maidani gida wallahi na hakura da aurenka jin haka yasa ya sake daddagewa ya lafta mata belt a tsakiyar bayanta wani gigitaccen qara ta saki tana dafe gadon bayanta tare da furta wallahi zan bi umarninka bazan sake ba "...."kima sake an faɗa miki wannan aliyu irin wanda kika sani ,wanda kika raina , wannan Aliyu ya wuce da tunanin dakikiya sakariya irinki , yana magana yana lafta mata belt tana ihu tana tarewa da hannunta sai daya lilis sannan ya barta yana haki " Useless girl Kawai , idan kika sake min irin wannan ganganci zaki ga aikin ganganci dan daidai sisin kwabo bazan raga miki .."

YOU ARE READING
CUTAR KAI
Romance"Ka sake ni ko dole sai nayi rayuwa da kai?" Me zanyi da kai a rayuwata ? " wallahi Dady ya gama cutata tunda ya rasa Wanda zai hadani aure dashi sai kai , bari na Tina Maka idan ka Manta matsayinka... Kai din fa bakowa bane face yaron babana me...