💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~TRUE LIFE STORY~
Free Page 8
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma , getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
"Kuka take sosai tana tunanin rayuwarta data gabata , isa izza da jiji da kai ko yar sarauta iyakarta kenan , dayawa mutane ada can baya sun sha faɗa mata cewar da gidan sarauta aka haife ta ba'a san abinda zatayi ba,ita kanta tasan gidan sarauta ne yafi dacewa daita saboda karfin mulkin dake tattare daita, taja numfashi a hankali ta sauke tana ciza gefen labenta na kasa sai ga wasu sababbin hawaye masu zafi sun gangaro mata ."
"har ga Allah bata marmarin sake yi masa rashin mutunci saboda ta horo iya horowa akanshi , tana tsoron sake faruwar wani abu saɓanin zaman lafiya , shiyasa da zasu zo kasar aunty ummi bata so ta biyosa ba , taso ya barta a kasarta ne ta cigaba da rayuwarta a gaban iyayenta domin tasan zasu taimaka mata ,dan bazasu yarda wani mummunar abu ya sameta ba, duk lalacewar itace din rayuwarsu ce amman ta nace lallai sai ta biyosa wanda ita a tunaninta kasancewarsu guri daya zai sa ta janyo hankalinsa gareta a she bata sani ba cikin ukuba ta jefe kanta ta karasa maganar cikin wani sabon kuka ."
wani kullin tashin hankali ta dinga ji a cikin zuciyarta ,a ranta tace "Aliyu baya qaunata sai wasu hawayen sharrrrrrr tamkar an bude famfo , tana jin motsin saukowarsa amman taki fitowa daga bayi dan tasan idan ta fito ma wani sabon bakinciki zai kusan mata , kuma tasan wannan fitowar da yayi gidan nawal zashi dan ya kuntata mata , sai data tabbatar da ya bar gidan gabadaya sannan ta mike ta isa bakin fomfo ,ta kusan minti biyar a jikin famfo tana wanke fuskarta , addur kariya da zaman lafiya a tsakaninsu tayi yafi sau babu adadi sannan ta fito parlour ,ta cigaba da sheshekar kuka, ranta na wani irin quna ta zauna hawaye na sake bin kuncinta ,da zarar ta runtse idanunta babu abinda take gani sai kyakkyawar miskilalliyar fuskarsa mai nuni da babu wani abu da ke damunsa . "
tana cikin wannan halin taji motsin buɗe kofar falo da sauri ta bude idanunta ta soma ƙoƙarin goge hawayenta da hanzari safiyya ta karaso cikin filin falon tana tambayarta "lafiya me kike ma kuka kisna "?wani matsanancin kuka ne ya sake kufce mata haka yasa hankalin safiyya sake tashi "wai meke faruwa ne kisna ki faɗa min me ya faru kike kuka "?
cikin dasashiyar muryarta da bata fitowa sosai tace "ba abinda ya sameni juyin duniya safiyya tayi da kisna domin jin abinda ke faruwa amman taki faɗa mata dan haka Safiyya ta bige da rarrashi har ta samu tayi shiru "kin ma ci abinci kuwa ta d'aga mata kai ba dan ta sakawa cikin komai ba , ruwa safiyya ta tsiyaya mata a glass cup ta mika mata ,ta amsa ta sha kadan sai lokacin taji zuciyarta ta ɗan yi mata sanyi ,cikin natsuwa safiyya tace "ki ƙara hakuri kisna duk da kina boye min abinda ke damunki amman zuciyata na faɗa min kina cikin damuwa mai tsanani wanda kusan ina ganin hakan a zahiri ,dan duk sanda zan zo gidan nan sai na iskeki cikin tashin hankali da damuwa ".
"abinda nake son dake Ki ƙara hakuri kowace mace da kika gani yanzu hakuri take a gidanta ,ba wai wani dadi take ji ba, kowani ma'aurata da irin tasu matsalar , idan kikaji matsalar wata zakice naki ba komai bane, sannan idan kina
lura zaki ga kowace mace a gidan aurenta tana da katuwar matsala , idan aka tara miki matan duniya babu mace guda daya da za'a cire wacce bata da matsala a rayuwar aurenta, haka idan aka tara mazan duniya kowane dana shi matsalar , abinda ya kamata muyi shine hakuri ,ki karfafa zuciyarki ki daina wannan kuka babu abinda Aliyu yake so a rayuwarsa kamar ya ganki cikin damuwa da tashin hankali , mai yasa bazaki d'aurewa zuciyarki ki fita lamarinsa ba , duk abinda kika san hakinsa ne ki sauke masa kiyi lamuran gabanki , wallahi muddin yaga kin fita hanyarsa kin sharesa zai dawo hankalinsa dan yaga kina yawon damuwa idan ya bata miki ."

YOU ARE READING
CUTAR KAI
Romance"Ka sake ni ko dole sai nayi rayuwa da kai?" Me zanyi da kai a rayuwata ? " wallahi Dady ya gama cutata tunda ya rasa Wanda zai hadani aure dashi sai kai , bari na Tina Maka idan ka Manta matsayinka... Kai din fa bakowa bane face yaron babana me...