45&46

452 8 0
                                    

*KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_

*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_

*WATTPAD*
_Realeshaa_

_Like my page on Facebook_ 👇🏻

https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/

*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

_Wannan page din kyauta ne agareki hazika kuma fasihiyar marubuciya *AUNTY BINTA UMAR ABBALE* Ubangiji Allah yakara daukaka ki fiye da yanda baki zato Alherin Allah ya kaimiki aduk Inda kike Inai miki fatan alkhairi._ 😍😍😍😍

       *PAGE 45&46*🖌️

_______________________________📖Madede cin parlour dattijuwar suka shiga;Wanda akalla shekarunta zasu Iya kaiwa hamsin da biyar, ko sittin.Cike da dattako tanunawa Nadiya wajen zama,tana mebin fuskarta da kallon tausayi ganin yanda fuskar ta tuttuje kamar wacce sukayi kokawa da zakan ya".Zama Nadiya tayi tana matsar kwallar takaici da bakin ciki"Cike da tausayi dattijuwar takalle ta tace"Nadiya barayine suka shiga gidan ku sukayi muku irin wannan danyen aikin haka!?ina mijin naki shi kuma yashiga? ina fatan de basuyu masa illah irin taki ba!?ta karashe cike da jimamin ganin yanda halittar fuskarta tasauya baki daya!.Kuka Nadiya tafashe dashi tace"Wlh Mama hansi ba barayi bane sukayi min wannan abin face kishiya ta,dubi irin wannan abin da tayi min kuma abin bakin ciki agaban mijinmu tayi min, anma sam be dauki mataki akai ba kokuma ya dakatar da ita"karshe ma sakina yayi yakuma Koreni acikin wannan Daren yace inbar masa gidan sa!"Ga mahaifiya ta batada cikakkiyar lafiya,Hawan jini ke damunta,nasan kuma muddin naje mata da wannan bakin labarin, ciwon ta ze Iya tashi karshema yajanyo sanadiyyan ta,shiyasa nazo kitemaka min kamar yanda Allah yatemake ki takarashe cikin wata raunanniyan murya.Cike da jimami,gamida tausayin ta Mama hansi tace taya zantemake ki Nadiya?"Bayan bawata alaka me karfi bace atsakanina da mijinku banda alakar musulunci.Hawaye tashare tace inde mukaje ki kabashi hakuri ze hakura yamayar dani dakina,dan yana ganin kimarki da mutunci ki,amatsayin ki na Dattijuwar arziki wacce duk mutanen unguwar nan suka dauke ki tamkar Uwa.Shiru mama hansi tayi,tana nazarin kalaman ta tasan gaskiya tafada,duk mutanen unguwar nabata kima da mutunci amatsayinta na Babba wacce takama kanta da mutunci ta awajen su.Numfasa wa tayi kafin tamike ahankali tadauki hijab dinta tasanya,suka fice...
"Sun dauki sama da minti goma atsaye awajen suna knocking kofar anma shiru ba abude musu ba"seda Mama hansi tayi magana kafin baba mai gadi yabude mata,yana ganin ta da Nadiya yayi saurin maida kofar zerufe,gudun kar yayi lefi awajen Ubangidan sa"cike da kamala tace"Yi hakuri bashiga zanyi ba sonake kayimin sallama da me gidan.Baba Mai gadi komai bece komai ba yajuya yanufi cikin compound din dan isar da sakon su"Mintuna ka'dan da shigar sa,se gashi yafito Ahmad na biye dashi abayansa.Koda yaga mai kiran tasa seya durkusa har kasa yagaishe ta cike da mutunci dakuma karramawa.Amsa wa tayi fuska asake tare dacewa dan Allah Alh alfarma nazo nema awajenka,ba danni ba sedan girman Allah dakuma darajan manzon tsira Annabi Muhammad(S.A.W).nake rokon ka dakaji kan wannan yarinyar kamaida ita dakinta,duk da kasancewar bansan wani irin lefi tayi maka ba!anma dan Allah kayi hakuri kamai da ita dakinta tarayu akan 'ya'yan ta,yanda zata basu tarbiyan daya dace sannan hankalin iyayenta ya kwanta domin zamanta adakin mijinta shine kwanciyar hankalin su."Shiru Ahmad yayi yakasacewa komai saboda kunya da nauyin matar dayakeji bakaramin kwarjini tayi masa ba"hakika bazeki bin maganar taba,kodan fitowa da tayi awannan Daren,gakuma girman Allah da darajan ma'aikin Allah data hada shida shi yaci, ace yahakura ko dan mutunta maganarta..Cike da jin nauyi yace hakika Mama ina ganin girmanki dakuma kimarki,anma kiyi hakuri bazan Iya maida Nadiya ba harse tayi hankali takuma koyi hakuri da zama da mutane kafin in mayar da ita dakinta!!..Durkushewa Nadiya tayi tare da rike kafafunsa, cikin muryan kuka tace dan Allah Dadyn Rufy kayimin rai, Wallahi bazan sake aikata kwatan kwacin abinda Na aikata abaya, ba natuba nabi Allah da manzo,nakuma bika" idan harka sake kamani da laifi akan Sukainat Wallahi nayadda kayanke min duk hukuncin dakaga yadace akaina;Nayi alkawarin zamu zauna lafiya tamkar yanda ko wasu abokanan zama suke zaman lafiya, sannan zan riketa kamar kanwata koda lefi tayimin zanyi hakuri da ita babu Wanda zeji kan mu,takarashe zancen cikin gunjin kuka... Kafin Ahmad yace"wani Abu Mama hansi tace"dan Allah Ahmad kadubi darajan Allah kakuma dubu yarinyar nan, kayafe mata lefin datayi tunda ta amshi lefinta,ta kuma yi alkawarin bazata sake aikatawa ba.Shiru Ahmad yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace"Shikenan Mama taci albarkacinki nayafe mata nakuma mayar da ita dakin ta, Allah yayafe mana lefin mu baki daya..Cike da murna Mama hansi tashiga yimasa Albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya."seda yarakata Har kofar gidanta kafin yadawo cikin gida ko kallon Inda Nadiya take beyiba yawuce sashen,Sukainat yayi kwanciyar sa lokacin goma da Rabi yagauta...

KISHIYA KO BAIWA???.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora