Chapter 48

314 16 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
♠♣♠♣♠♣
♠♣♠ ♣
♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
♣♠♣♠♣♠
♣♠♣♠
♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Story*
*and*
*Written*
*By👇*

*Asmy Jafar*
*(Ummu Abdulhakim)*

&

*Zainab Mukhtar*
*(Ummu Maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

🅿️-4️⃣8️⃣

_________Kwance Jidda take akan doguwar kujera tana game awayarta sai faman karkacewa take yi tana cewa "good" wani lokacin kuma tace "kash" tare da ɓata fuska.
Mama ce tsaye a kanta tana magana sai dai hankalin Jiddar kwata-kwata ba ya kanta, fisge wayar mama tayi sannan fa hankalin Jidda ya dawo kanta, Shagwa6e fuska tayi tana cewa "mama shikenan kinsa anyi min game, ta ƙara ɓata fuska cike da zallar shagwa6a, murmushi kawai Mama tayi tare da cewa" to ba gashi yanzu kin ji niba, amma ina ta magana bakya ji kin tattara hankalin ki gaba ɗaya a waya. Miƙewa zaune Jidda tayi tace "Laaa dama magana kikeyi mama? Yi haƙuri dan Allah kinji mamana Allah ban jiba ne, dariya Mama tayi tace "ai ba zakiji ba kina aikin la dar ne zaki wani jiyo ni? Dariya sukayi dukan su sannan Mama tace "sai ki tashi kije yamma sai daɗa yi take, kafin Ummanki ta yanko min samma ci,"

Dariya Jidda tayi sannan tace "ina jiran mamata ne fa, tace akwai sa ƙon da zata bani idan ta dawo.

Mama tace "to sarkin gardama ki tashi kije nace, gobe ai kin dawo ki karɓi sa ƙon nasan zata ajiye miki ko yaushe ne.
Ɓa ta fuska Jidda tayi tace"to in kuma wanda la la ce ne fa Mama? Ni dai kiyi haƙuri in karɓa nasan in sha Allah yanzu haka tana kan hanyar da wowa, kinji Mamana! Ta faɗa cikin sakarcin da ta iya.

Duk da haka Mama bata yarda ba sai da ta ko ra ta, aiko ta miƙe tana diddira ƙafa fu a ƙasa tana Shagwa6a har da cewa "ita gobe ba inda za ta, kuma daga yau bazata sake da wowa gidan ba sai ƙarshen wata.

Dariya kawai Mama tayi tace" ina nan zaune zaki ka wo kanki da kanki za mu haɗe da ke ne. Daga haka tayiwa Mamar sallama ta wuce.

Zaune ta iske Yaya Deeni a falon Umma ya tanƙwashe ƙafa fu yana cin abinci, za ro ido tayi dan tuna gargaɗin da yayi mata na duk inda za taje ta fara sanar mai koda gidan su ne, duk da kasancewar gidajen a haɗe suke amma ya gindaya mata sharaɗin kar ta sake taje ba da izninshi ba.

Kallonta yayi ganin irin kallon da take mishi tana zazza re ida nu yace " eh ai dole ki za ro ido waje tunda kinsan baki ta ki gaskiya ba, okay fine! Sai ki shigo ki karɓi hukuncin ki na ƙetare magana ta da kikayi.

Narke fuska tayi tare da fa ra yimai ma giya tana haɗe hannunta duka biyu guri ɗaya, duk ta marairai ce. Dariya ta bashi amma yayi kokarin ganin ya danne dariyar dan kar taga damar shi, yace " oyah zo ki kai kayan nan kitchen ki da wo ki karɓi hukuncin ki.

Nesa dashi ta gurfa na tana jan gwuiwa kaɗan-kaɗan tare da miƙa hannun ta a hankali ta janyo plate ɗin gaban shi, da sauri ta miƙe tana ja baya ganin tayi nasarar ɗauke plate ɗin ba tare da ya ka ma taba, hanyar kitchen ɗin ta dosa tana hamdala a ranta, can ƙasan ruhin ta kuwa ta gama ayyana dagaa ajiye plate ɗin guduwa za tayi ta ƙofar kitchen ɗin, kuma kai tsaye ɗakin umma zata wuce kar ya ritsata a ɗa kinsu. Ƙa ra ɗaga ƙafa tayi tana sauri ta shige kitchen ɗin, sai dai tana ajiye wa har zata gudu taji an cabko ta, ta buɗe baki da zummar za tayi ihu ya toshe bakin tare da jan hannun ta suka fita ta ƙofar.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now