chapter 26

281 14 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-2️⃣6️⃣

____________________yaya sadiq bai samu ya isa gidan ba dan koda ya shigo unguwar wasu masallatai har anfara sallah, gayawa Mai achaban da ya daukoshi yayi ya sauke shi dan bai fito da motaba,

Sauke shi yayi yabi jam'i sannan daga baya ya isa gidan, hajara ya iske zaune a falo tana kallo ko kallon gefenta baiyi ba yayi hanyar dakin jidda,

Wani murmushi tayi ta bishi da kallon da ita kadai tasan ma'anarshi a ranta kuwa cewa take zaka sani yau,
Miqewa tayi ta nufi dakinta,

Zama yayi a falon jidda sannan ya ciro waya ya kirata, gayamata yayi yana falonta tazo ta karbi maganinta sannan ya kashe yana cigaba da latsa wayarshi,

Jidda dake kwance har lokacin ta miqe daqyar da dafa bango ta iso falon,
Zaunawa tayi tare da gaisheda shi, ya amsa tare da tambayarta ya jikin,
Miqa Mata ledar maganin yayi ya miqe tsaye yace,
"Toh ni Zan koma auta Allah yabaki lafiya,

"Amin yaya nago...
Sai dai bata kaiga qarasawa ba suka jiyo kamar hayaniya,

Dukan qofar akeyi da qarfi, muryar Yaya deeni sukaji yana cewa ku bude qofar nan nace,

Cike da mamaki suka kalli junansu dan dai qofar a bude take kawae dai bai murd'a handle din bane,

Kallonshi hajara tayi tace,
"Sun bar key din a ciki ne ai da yanzu na bude da wannan na hannuna tun Kan ka qaraso ma,

"Tun yaushe yake gidan ne?
Kana fita zuwa masallaci Yana shigowa,

To shine kuma baki kirani ba,

Nima na dauka ko ya tafine sai da nafito naga qofar arufe har lokacin, shine ma na dauko keys din dake gurina,

Bude qofar sukaji anyi duk da Daman can a bude take dan dai kawae andora shine, shi kuma ya hau Kai ya zauna,

Fitowa yaya Sadiq yayi daga dakin ko kallon gefensu baiyi ba yayi hanyar fita daga falon,

Shan gabanshi yayi tare da cewa"
Me kake yi a dakin jidda?

Kallonshi yake yi cike da mamaki, kafin ya ra6a ta gefenshi zai wuce, fincikoshi yayi da qarfi cikin qaraji yace bazaka amsamin tambayata ba?

Muryar jidda sukaji tana cewa,
Magani ya kawomin, ta fada tare da nuna ledar dake hannunta,

Mayarda kallonshi yayi kanta kafin yace, to ubanme ya sa aka kule qofar Kuma me kuka tsayayi tun fitana har yanzu,

Itama jidda cike da bacin rai da ciwon da ke damunta tace, meye wannan kake yi Yaya?
Me kake nufi da anrufe daki Kuma tun fitar ka?
Magani fa yakawo min Kuma shigowar shi kenan, haba yaya, ta fashe da kuka,

Murmushin takaici Yaya Sadiq yayi yace" zargi na kakeyi Koh deeni? Okay fine" karka fasa kacigaba dayi bakada laifi Nina kawo kaina gidanka dan haka ko abinda yafi wannan kayimin kayi daidai,

"Kar ka nemi rainamin hankali malam ka amsa min tambayarda nayi maka, ubanme ya tsayar da kai bayan kabata maganin,

"Shima ranshi a 6ace yace, abinda kake zargin ya tsayar dani shine ya tsaidani kayi abinda zakayi,

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now