Abu Bilal

67 6 2
                                    


                                 <4>

Washe gari tunda sassafe Bilal ya fita bai zarce ko ina ba sai gidan ogan su, a yanda yana zuwa ogan nasu ya fito cikin shiri zaka san cewar dama sun shirya tafiyan tsakanin su, cikin girmamawa Bilal ya gaisheshi a matsayin shi na oganshi Kuma ban gyare daya abokin Daddyn shi, amsa mashi yayi cikin kulawa sannan ya tada motar suka cilla bisa titi, a kallah sunyi kusan tafiyar awa biyu kafin su Isa inda zasuje, kofar wani gida Naga sun tsaya horn Bilal ya sannan jim kadan sai ga mai gadin gidan ya bude gidan ya leko, ganin katowar jeep gashi glasses dinta duk sunsha tin, yasa yaki isa gurun motar yadai yi tsaye yana kallon motai, ganin haka yasa Bilal fitowa ya nufi inda mai gadin take tsaye, ganin wanda ya fito daga motar da kayan sojoji yasa Mai gadin sakin ajiyar zuciya da Ida karasa fitowa, hannu Bilal ya mika mashi suka gaisa kafin yace yai masu iso ga mai gidan "kace Major general Ali ne"  jiki na bari mai gadi ya juya da sauri ya wangale masu gate din gidan ganin haka yasa Bilal komawa cikin motar ya tada ya dannan kan motar ciki, parking lot din gidan yai Mata masauki, da gudu bayan mai gadi ya kunle gate din ya nufi ciki, bakin kofa suka kusa cikin karo da mai gidan nashi, cikin girmamawa yake gaishe a matsayin shi na Mai aiki a karkashin shi dukda cewa a girme ya girme shi sosai saboda tsoho ne mai gadin, cikin girmamawa shima ya amsa mashi fuskar shi dauke da far'ah yace " baba jiya na manta bance maka zanyi baki ba ko, wallahi na shafa'a ne shiyasa a bude Mamu falon bakin can, bari inje in iso dasu" cikin girmamawa baba mai gadi yace " toh ranka ya dade"

Wurin motar su ya nufa, cikin dan sauri sauri, kafin ya karaso Bilal ya zagaya ya bude ma major Ali kofa, fitowa yayi fuskar shi dauke da murmushi ya nufin mutumen da shima murmushi ke a fuskar shi suka rungume juna, irin alamun tsofin abokan da suka dade basu hadu ba, gaisawa sukai cikin barkwanci. Da alama abokan irin tun abotar yarinta ce, daga yanda suke jan junan su, bayan sun gama gaisawa major Ali ya maida kallon shi kan Bilal da yake tsaye yana jiran su gama gaisawa shima ya gaishe da mutumen.

"Yawwa Alhaji Hamza wannan shine Bilal da mukai magana akan shi jiya" cikin girmamawa Bilal ya gaishe da Alhaji Hamza daidai lokacin kuma baba mai gadi ya iso wurin "an bude falon ranka ya dade"  "ok toh nagode baba" Alhaji Hamza ya amsa, sannan ya kalli abokin nashi yace "toh bismillah mu karasa ciki sai muji dadin tattaunawa da kyau" Yana gaba suna binshi a baya har suka Isa falon, wanda ke dauke da kujeru na alfarma, daidai misali falon ya kayatu gaskiya, basu dade da zama ba aka kawo masu kayan breakfast kala kala, major Ali ne kadai ya dan hada tea, shiko Bilal ba abunda ya taba ma.

Bayan sun dan natsu sun huta, major Ali ya gyara zama ya fuskaci Alhaji Hamza dake zaune kusa dashi ya fara mashi bayanin halin da ake ciki, kam babu abunda ya boye mashi har plan din da Bilal din ya kawo shawarar suyi, shiru Alhaji Hamza yayi na dan wani lokaci kafin ya gyara zaman ya fuskaci major Ali dake jiran jin amsar shi. Nisawa yayi ya sauke nannauyan numfashi sannan yace "naji duk abunda kace Alhaji Ali saidai wannan abu babban abu ne, musamman ma idan sukai saurin gano cewa kudin da aka kai fasu fake ne, zamu iya rashi shi Alhaji mustapha din da wanda aka aika ya kai masu kudin, kunsan fa sai sun fara duba kudin kafin su saki mutun, sannan maganar bomb dinnan gaskiya nidai Ina tsoron musamman yanayin ka'idojin kasar mu ba kowane soja ake bari yana amfani da bomb ba dukda nasan kunfi Ni sanin komai ta wannan bangaren, Amma dai ina jin tsoron hakan" Alhaji Ali ya gyada kai alamar ya fahimci abunda take nufi "nasan da hakan Alhaji Hamza Amma inshaAllahu muna da yakinin babu abunda zai faru inshaAllahu plan dinmu zai tafi a yanda muka tsara, munai fatan mu shine ka taimaka Mamu da fake kudin nan, dan gaskiya bama son mu basu kudin gaske, sanin kudin suna iya konewa hakanan a banza, shiyasa na yanke shawarar zuwa wurin ka da kaina, dan already ma har mun fara magana da kidnappers din, so muke mu hada komai kafin lokacin da zamu gama negotiation da su" nisawa Alhaji Hamza yayi yana nazarin komai kafin yai making decision dinshi, cikin amincin Allah ya amince da batun su, Nan sukaci gaba da tattaunawa yanda zasu gudanar da komai ba tare da su kidnappers din sun gano komai ba da fatan Allah yai masu shagora.

Sai bayan sallahn azahar suka baro gidan Alhaji Hamza, awa biyu daidai ta kawo su garin gombe daga bauchi. Saida Bilal ya fara aje major Ali a gida kafin ya wuce gida shima, daidai bakin gate ya danna horn ba'a dau lokaci ba mai gadi ya wangale gate din, ya danna kan motar ciki ganin wasu motacin daban bana su uncles dinshi ba yasa shi tuna yau fa rumah tace mashi zasuzo, dafe kai yayi na dan lokacin kafin ya bude motar ya fito, mean falon gidan ya nufa, daidai bakin kofa ya dan tsaya na wasu yan second ne kafin ya murda kofar ya shiga bakin shi dauke da sallah,  gaba ki daya falon juyowa sukai suna kallon shi tare da amsa sallamar da yayi, Ida karasowa yayi tsakiyar falon ya dan rusana ya gaida mahaifin rumah da mahaifiyar ta, cikin jimami suka amsa mashi sannan sukai mashi jajen abunda ya faru, juyawa yayi ban garen rumah dake gaisheshi yayi ya amsa mata cikin kulawa, itama din jajen tayi mashi sannan, yabi mutanen falon da gaisuwa, sannan ya mike ya haura sama dan ya samu ya dan watsa ruwa.

Bai dawo kasan ba Saida Aunty rahila taje ta sanar mashi su rahila zasu wuce,  amsa Mata yayi, tashi yai ya ida kimtsawa, sannan ya nufi downstairs, tunda ya fara saukowa take kallon shi, jin kamar ana kallon shi yasa dago kai, karaf idanuwan su suka shiga cikin na juna, yanda ta wani narke mashi ga kwalli cike da idon ta yasa shi sakan mata murmushi, wanda ko ba'a fada ba da ka kalli fuskar ta zaka san murmushi ba karamin tasiri yayi a zuciyar ta ba.

Karasa saukowa yayi ya isa tsakiyar falon ya zauna daga kasa shima. Cikin jimami da tausayi suka kara jajanta mashi da yi addu'ar Allah ya kubuto da Daddy lafiya. Ameen duk suka amsa dashi. Sannan sukai masu sallama, har bakin mota suka rako su, Saida suka ga fitar su sannan suka dawo gida.

Abu BilalWhere stories live. Discover now