Abu Bilal

123 8 3
                                    


                     <27>

Ranar da su yadikko suka baro kauyen, Baffa idi ya dira dashi da tawwagar shi, kai tsaye gidan Abbu suka nufa dan tunanin su, su yadikko na nan amma ga mamakin su sai suka iske kangon gidan kawai, gidan mai gari suka juya suka nufa dansu a tunanin su baza su wuce cikin garin agadaz ba, hardai kauyen su ya dikko sunje basu sami labarin su ba nan fa hankalin baffa idi yayi mugun tashi, gashi dama yanda sukai da yan bindigar idan sun kashe kanen nashi zasu biya su idan sun kwaso dukiyar shi, dama dai baffa idi baida komai sai yar buga buga, kamar wasa duk kauyen da yake tunanin zai same su yaje basu nan, da ya gaji da billayi ya kara dawowa kauyen su Abbu kai tsaye gidan mai gari ya nufa, mai gari na zaune tare da dattijen cikin garin ana ta fira sai ga mutun ya fado masu, baffa dake ta mazurai kamar wanda yaima sarki karya yace "kai haladu wurin ka nazo ka dan bani minti biyu" kallon shi mai gari yayi sannan yayi murmushi ya mike suka koma gefe, cikin isa baffa ke magana "dama dukiyar dan uwa na da ya mutu ya bari nazo ka bani" kallon shi mai gari yayi na yan second sannan ya girgiza kai yana murmushi yace "toh malan idi shi dan uwan naka da Allah yaima rasuwa baida itali ne? Injin da uwar shi a raye da yaran shi biyu, ko ance maka duk sun mutu ne? Toh bari kaji in fadi maka katmrka sake zuwa man nan tambayar dukiyar marayu in kana so kaji inda dukiyar take kaje wurin sarkin agadaz dan shi yayi masu rabon gado bani ba" mai gari na fadin haka ya juya ya koma mazaunin shi, yana mamakin karfi hali irin nasu baffa, duk kauyen su kowa yasan da sa hannun yan uwan Abbu wurin kisan shi da wasu da suka rasa rayuwan su suma a wancen lokacin amma ji wai yazo neman dukiyar da baida gado ciki, da su yadikko na nan haka zai masu fin karfi ya kwace dukiyar, gaskiya  Abbu ba karamar dubara yayi ba da yace subar kasar niger kwata kwata,  hannu yasa ya share hawayen da suka zobo mashi saboda tuno Abbu da yayi mutun mai kirki, mutumen arziki "Allah yaji kanka malan Ibrahim" ya furta a fili gaba ki daya wurin suka amsa da "Ameen " lokaci daya kowa jikin shi yayi sanyi, saboda shidai Abbu baida abokin fada a garin kowa nashi ne.

Haka baffa idi ya gama tsayuwar shi cikin tashin hankali sannan yaja kafafun shi yabar wurin kai tsaye kauyen su ya nufa yana tafiya yana share zufa.

Su Daddy sun sauka Germany lafiya, taxi ya tarar masu suka wuce gida, daidai kofar gidan su mai taxi din ya tsaya ya fiddo masu kayan su daga cikin booth, shidai Ayaan hankalin shi ba a kwance yake ba dukda dama yasan dole nan din zasu fara sauka, kwaso kayan yayi yabi bayan Daddy cikin sanyin jiki, doorbell din Daddy ya danna jim kadan wata mata tazo ta bude da ganin ta mai masu aiki ce gaishe da Daddy tayi cikin far'ah tana bashi hanya, sjima din amsawa yayi fuskar shi dauke da murmushi, ita ta kama ma Ayaan suka shigo da kayan, sannan ta wuce sama dan sanar ma mummy.

Nigeria

Sosai Abeer ta dage wurin koyon turanci da girki, gashi yanzu ta kuma islamyar Saturday da Sunday kwata kwata bata da lokacin kanta, har tausai take ba bilal wani lokacin. Rayuwar Abeer da Bilal  gwanin ban sha'awa dan sosai yake nuna ma Abeer so, itama kuma dunda kunyar da take hana ta yin wasu abubuwan wani lokacin amma tana kokarin taga ta faranta ma mijin nata, musamman ma da tasan fa nan gaba akwai wacce zata shigo gidan, duk wata hanya da zata bi ta mallake zucitar Bilal ta riga ta gama binta, ita kanta tasan ba so kadan Bilal din ke mata ba, ga wata natsuwa irin ta matan da suka dauki aure da mahimmanci na shigar ta, ko shigar ta tayi daban da ta sauran yan uwan ta matan aure masu irin shekarun ta, ko kawaye Abeer bata dasu saboda ita mutun ce dama marar son shiga jama'a, hakan ba karamin yima Bilal din yayi ba dama shi baison kwashe kwashen kawayen nan marar sa kan gado.

Haka rayuwa taita tafiya, har akai ma Bilal transfer daga wurin aiki zuwa Abuja sosai yan uwan shi suka taya shi murna, su mummy dai saidai sukai magana ta waya. Ayaan dake school shima ya kira dan uwan nashi ya taya shi murna sosai. Bayan komai ya lafa Bilal ya fara shirin komawa Abuja saidai bada Abeer zai tafi ba tukun sai ta gama jarabar ta sannan zasu koma gaba daya.

Abeer ce a d'akin Bilal  tana ta hada mashi kayanshi cikin damuwa, duk yana lura da ita tun safe take haka ya kuma san tafiyar da zaiyi ce ke damun ta, shi kanshi dandai jarabawar da zasu fara soon da ba abunda zaisa yabar matar shi, amma kuma in ya tuna wani abu sai yaji wani irin sanyi na ratsa mashi zuciya, ko ba komai dai ya kusa samun abunda kullin yake mafarkin samu, dukda dai daurewa yake, sannan kuma yana son cika alkawarin da ya daukar ma kanshi gaskiya da tuni labari yasha banban, ai kila da yanzu Abeer din kanta ta kusa haihuwa, wata yar karamar dariya ya saki yana rayawa a ranshi randa zaiga Abeer dauke da ciki "rigima kenan" ya fadi a fili yana kallon Abeer din da ta dago tana kallon shi tun lokacin da yayi dariya, bata fuska tayi ta turo baki tana hararar shi kasa kasa, cikin shagwabe  tace "wallahi hammah gulma ta kake a zuciyar ka ko?" Tayi maganar tana kallon shi, dariya yayi ya daga hannuwa sama yace " Ni kuma? Yaushe? Nidai karkiyi mani shirri wife, babu gulmar kin da nake" ya fadi yana zama kusa da ita, jawo ta yayi ta fadi jikin shi, yana dariya kasa kasa dagowa tayi tana kallon shi, shidin ma kallon ta yake, daga mata gira yayi alamun kallon fa? Sunnar da kanta tayi cikin kirjin shi tana dariya, haka dai suka shiririce harsai kusan shabiyun dare sannan suka kwanta manne da juna.

Washe gari Bilal ya wuce abuja cike da kyewar matar shi, ita kanta Abeer din duk ta zama wata iri saukin ta daya ma gidan Hajjo ta dawo da zama.

Lokaci yana ta tafiya har ya kama saura sati daya su Abeer su fara waec, sosai take karatu ba na wasa ba, dan musamman Bilal ya samu mata malamar da zata rinka yi mata lesson har gida kuma cikin ikon Allah tana ganewa da yake kwanyar na ja. A bangaran Bilal  kowa tunda yaga sun kusa fara exams ya dage wurin gyara masu inda zasu zauna wani tsohon gidan Daddy ne dake Abuja da yake da can sunyi zaman garin, gida ne mai kyau saidai kawai tsufan da yayi amma baida wata makusa gaskiya, kuma a cikin asokoro gidan yake shiyasa Bilal yace bazai nemi wani gidan ba tunda  dai ga wani.

Kwance take a dakin da hajjo ta ware mata waya ce kare a kunnen ta, babu abunda take sai murmushi da gani dai firan na mata dadi, magana taje kasa kasa duk min kwafkwafin mutun bazaiji mi take cewa ba, haka yadikko ta shigo ta iske ta, sallama naga tayi ta aje wayar gefe, tana sauraren yadikko fake ce mata zasu tafi gaisuwa can kasan layi ita da hajjo....

Cikin yardar Allah su Abeer  suka fara exams babu kama hannun yaro a kalla sunyi wata daya suna waec, ranar da zasu gama kar kuso kuga bakin Abeer dan murna gashi kuma da sun gama waec da wata daya zasu fara neco shiyasa Bilal yace suna gama waec zaizo ya dauke ta in sun kusa fara neco ya maido ta tayi dan ya gaji rmda rashin ta kusa dashi.

Ita ko Abeer murna biyu take na farko zata ga mijin ta na biyu kuma zataje abuja saboda ita dai tana bala'in son garin yayi mata sosai, gashi  Bilal yace mata wannan karon hutu zai dauka na musamman saboda ita, saboda tunda ya koma abujan baizo gida ba. Shine dalilin da yasa ta kagu su gama. Hmmmm su Abeer  kenan🤭

Karfe 3:30 suka fito daga paper karshe duk wanda ka kalla zakaga tsantsar farin ciki da gajiya a fuskar shi, tafiya take a hankali har ta fito bakin gate din makarantar, tunda ta fito take ta kalle kalle ganin ko driven ta yazo, can dan nesa da ita ta haggo shi tsaye jikin mota ya rungume hannu yana kallon ta ta cikin bakin glass din dake manne a fuskar shi, wani sihirtaccen murmushi kawai yake fita a fuskar shi, Abeer hannu tasa ta murtsike idanuwan ta dan ta tambatar da abunda idon ta ya gano mata. ganin haka yasa shi bude hannuwan shi alamun ta taho gare shi, hakan ya tabbatar  ma Abeer da gaske dai hamman ta ne, watsar da papers din hannun ta tayi ta nufeshi da gudu, tana zuwa ta fada cikin kirjin shi, shi kuma yai mata kyakkyawar rungume tare da sakin ajiyar zuciya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 17, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Abu BilalWhere stories live. Discover now