80-85

1.2K 76 0
                                    

(AUREN HADI)
:

:

Har sallah azahar Ummi na bacci sai da Salman ya dawo daga masallaci ya tasheta tayi sallah, tana kammalawa ta fito falo tana wata irin tafiya kamar mai koyo, tana zuwa ta zauna kasa kusan kafafun Salman, saukowa yayi ya zauna kusa da ita yana fadin "aljannata ya jikin naki?"

Kallonshi tayi da mamaki tace "aljannarka kuma, yanzu kenan na tashi daga aljana na koma aljannarka?"

Gira ya daga mata yace "in dai har Ubangiji yana bamu aljanna a duniyar nan, to ni kece aljannata."

Hada kanta tayi da gwiwa tana murmushi, yana ganin haka ya fara yi mata cakulkuli yana fadin "tunda ba zaki yi magana ba sai mu sake komawa ciki."

Ummi kam dariya take tana bille bille duk ta hayeshi, saida yaga hawaye sun fara fitowa a idonta tsabar dariya sannan ya daina, ba tare data tashi daga jikinshi ba, ta gyara kwanciyarta ta yanda suke kallon juna tace "nifa yunwa nake ji."

Wani kallon so yayi mata yace "na sani dama dole zaki ji yunwa, amma kiyi hakuri na kira Mama na fada mata kuma yanzu zata aiko maki da abinci."

Cikin haushi ta kalleshi tace "yanzu fadawa Mama kayi?"

"A'a, na dai fad'a mata cewa  baki iya girki bah saboda haka  tasa dake a cikin  nasu."

Kallonshi tayi tace "yaya Salman na dauka ae fita kayi, saboda duk kasa hankalina ya kasa kwanciya."

Cike da mamaki yace "me yasa?"

"To ai naga kayi kwalliya ne dayawa, kuma naga ko a aurenmu ba kayi irinta ba."

Dariya yayi yana kallon fuskarta yace "kwalliya fa,to kenan kwalliyarce ta d'aga maki hankali?"

"Yaya Salman ina jin baka duba madubi ba bane shi yasa, kai kyakyawane kuma yau naga kafi kullum kyau, kaga dole hankalina ya tashi dan ban san da suwa zaka hadu ba."

"Wai mata kike nufi?"

Turo baki tayi tace "Eh mana."

Gashinta ya  fara shafawa yana fadin "da a jiya kika fada haka kafin dare, to da saina yarda, amma yanzu ni Salman na Ummi ne ita kadai babu k'ari."

Murmushi tayi sosai hakan yasa ya saka dan yatsarshi a kurmin kumatunta yana kallonta, cewa tayi "amma fa yaya Salman kai kace zaka kara aure."

"Eh, a da kenan, amma banda yanzu da Ummi ta zama ta Salman suka hadu suka zama manyan yara."

Dariya tayi tace "ni dama babbar yarinya ce."

"Da gaske, to shikenan zamu gani."

Cikin shagwaba tace "yaya Salman da gaske ba zaka kara aure ba?"

Murmushi yayi yace "ba zan kara bah  in dai kina tare dani."

Tashi tayi zaune ta tara mashi tafin hannunta tace "ka rantse ba zaka kara ba."

Fashewa yayi da dariya ya janyota jikinshi ya hade  kanta da kirjinshi yace "Allah ya shirya min ke."

Tashi tayi daga jikinshi tace "yaya Salman wallahi da gaske nake, in san samuna ne na zauna da kai ni kadai, wallahi ba zan juri ganinka da wata mace ba."

Tsaida dariyar sa yayi ya sauke ajiyar zuciya, tabbas ya fahimci da gaske take kuma ga dukkan alama Ummi zata iya yin komai dan taga ta sameshi ita kadai.

Ganin baiyi magana yasa Ummi tace "yaya Salman dan Allah kamin alk'awarin zama dani ni kadai, idan kamin haka ni kuma zan zama kamar baiwa a gareka, ba zan taba gajiyawa da hidimarka ba insha Allah."

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now