Chapter one. 🌷🌹

35 2 0
                                    

*BANSAN INDA SUKE BA*
_a halin yanzun_

       *NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA*
*WRITERS ASSOC*

*Marubuciyar👇*
*Nana Jawaheer*
*Gimbiya Hakima*
*Izzah ko mulki*
*Sanadin link*
*A gidan haya*
*Ɓarawo ne*
*Sadaukin  burhaan*
*Sanadin soyayyar shan minti*
*Bayi ma ƴa'ƴane book 1&2*
          _AND KNOW_
*BANSAN INDA SUKE BA*
_a halin yanzu_

*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Am back again my lovely fan's, fatan zaku anshi BANSAN INDA SUKE BA fiye da yanda nike tunani dan kuwa salon nashi daban yake, dan yazo da abubuwa iri² tsaya gaya maku shi zaku ce cika baki ne, amman na barku ku zaku gaya da kanku😘*

*Chapter one🌹*

Wata budurwa ce tsaye idonta cike  da hawaye tana kallon matar da ke kwance rai hannu ga Allah, ana bata magani, bayan Doctor din ya gama duba lafiyarta gami da yi mata allurar da  yake mata kusan kullun,wanda ita har yanzun bataga anfanin yin allurar ba, duk da Allah shike da magani amman har yanzun itadae bata ganin wani cigaba... tashi Doctor yayi tsaye ya mika ma saurayin da ke gefe hannu yana cewa..."congrats Barrister Salim, Alhmdulh jiki ya fara yin sauki cikin ikon Allah."
Shima mike mashi hannu yayi sannan yace, "Masha Allah, Allah dai ya kara bata sauki." Cikin annuri Doctor yace...."Amin ya Allah, ni zan koma hospital abokina ga magungunanta nan Allah ya taimaka." Cikin dauriya Barrister yace....."Amin ya Allah ina godiya."

Bayan tafiyar Doctor,  Barrister Salim ya Kalli Salma cikin nuna alama ta rashin wasa a cikinta yace..."yau dai Salma sai kin gaya man wacece ke, sannan kuma wani matsayin wannnan matar take dashi a wajenki." tsareta da narkarkun idanuwanshi yayi yana jiran yaji abunda Salma zata ce mashi dan ya gaji da zama dasu ba tare da yasan su waye su ba....numfasawa tayi idanuwanta cike da kwalla dan ita yanzun ba wannan ne a gabanta ba, ta lafiyar wannan matar da ke kwance take amman ya zama dolenta yau dae ta gaya mashi wacece ita dan gaskiya Salim yayi hakuri da yayi zaman shekaru dasu yana taimaka masu ba tare da ya matsa mata da jin daga ina suke sannan kuma suwaye su, cewa tayi....."Salim ko baka tambayen ba daman yau nayi shirin na gaya maka wacece *UMMA SALMA MUHAMMAD*, sannan na gaya maka matsayin ta a wajena....

Zagaya Baban parlourn ta kamayi sannan tace...."Ka gyra zama yau zan baka tarihin rayuwarmu nida wannan baiwar Allah." Zama yayi ya maida hankalin shi wajenta ba tare da yace mata komai dan ya ƙagu ta fara, lura da tayi da hakan yasa ta fara magana..

"Mahaifina ya kasance mai kudi ne,na bugawa a jarida, mu biyu ne ya haifa nida yar'uwata Basma, kuma muɗin yan biyu ne, na kasance mai bala'in son ganina a makarantar boarding tun Basma bata da ra'ayin zuwa boarding har na cusa mata shi a zuciyarta koda muka gama primary muka zana science and technical, cikin ikon Allah mu duka biyun muka samu addimission a G.G.Sandamu da ke cikin jahar katsina."

Cikin murna nike tsale ina cema Basma! "Ye! Ye!! Ye!!! Ke basma gobe ne zamu makarantar boarding fa."
da yake ita Basma har yanzun bata ida sa son zuwa boarding a zuciyarta ba cikin tsora tace.
"Ke Salma baki jin tsoro? Naji ance boarding mugunta akeyi sosai, ni shiyasa duk bani jin dadi baki daya."
ta ida maganar cikin damuwa da tsaro dan ita bata son abunda zai bata wahala a rayuwa, ni kuwa cikin garaje nace mata.
"bangane baki jin dadi ba? Ai boarding duk wanda yayi maka ramawa ake, ai shiyasa nace ma Baffah in zai hado mana provision ya hado mana da dorina, kinga duk waida ta bugemu sai mu rama,kuma duk waida ta samu daukar ruwa, sai muce bamu dauka itama sai ta daukar mana namu, sannan mu hada madara da bornvita yanda muke so, ga kuma sardine muce mu ƙoshi, ba kamar nan gida ba sai Momy ta zuba maka two spoon ba."
Na ida maganar cikin Murna da yake mun taso cikin gata da kulawa tun daga kan Momy har Baffah, itama Basma ceman tayi cikin murna tace."hakane Salma, to tashi mu tafi gidan Zaliha mu anso dinkin uniform din mu."

Nida da Basma kenan, lokacin muna da  kshekara goma sha daya dayake mu  *IDENTICAL TWINS NE*baka ganemu, saboda kamarmu ta baci komai namu iri daya ne harta maganar mu iri daya ce,Momy kawai take banbance mu, itama a fuskar take gane  wani abu ya banbantamu amman ba wanda ya ganshi sai ita daya, dan ko Baffah baya ganemu...... Ita Basma tana da san surutu, amman batada fada, ni kuma,mafadiciya ce, amman bana cika san yawan surutu ba, to tanan watarana yan gida suke gane mu, da yake wani abokin Baffan mu Alhaji Mala gidan mu yake zaune shi da iyalinshi....Haka muka dauki hanyar zuwa gidan Zaliha dan anso dinki uniform dinmu.
"Assalama Alaikum.'' Cikin dariya Zaliha ta ansa da..."Amin wa'alaikumus Salam"...."Zaliha ina wuni."?...."Lafiya lau yan biyu kyautar Allah,  to yau sai kun gayaman wacece Salma wacece Basma a cikinku, sanann zan baku dinkin Uniform din ku."
ta ida maganar tana dariya...Karrab nace mata "nice Salma.".... Sai Basma tace.."Aa Zaliha karki yarda nice Salma itace Basma."
nan sai gardama ta kaure tsakanin mu kowa yana cewa nice Salma, haka dai Zaliha tayi hakuri ta bamu dinkin mu ba tare da ta gane Salma da Basma ba, bayan ta bamu muka dawo gida.

"Momy mun dawo."...."to Sannunku da dawowa, kunga yanzun saura ku sawo tsintsiya tunda kun anso dinkin..."cikin shagaɓe nace..."Haba Momy mu gaskiya ba wata tsintsiyar da zamu tafi da ita ni har yanzun banga Baffa ya sawo mana dorina ba, amman ana yi mana maganar wata tsintsiya."
cikin faɗa Momy tace. dan kuwa bata son muje wata boarding dan ba yanda zatayi ne kawai cewa tayi...."To tunda kun matsa ku a dole sai kunje boarding ai dole ku tafi da tsintsiya, tunda naga yau wulakanci kuke ji bari na ba Idi mai-gadi ya sawo man dan ban yarda ku tafi ba tsintsiya ba.".....Bayan Momy ta gama yi mana parking tace mu zo mu zauna tayi mana wa'azin tafiya boarding... Nan ta fara yi mana wa'azi kamar haka..
"Kuna jina ko"?cikin natsuwa muka ce a tare "Eh Momy." kamo hanayenmu tayi ta cigaba da cewa."Yauwa  idan kuka je boarding bance ku yarda wata tasa maku hannu cikin wando ko riga ba, kuna ji ko."? Sake cewa.. "Eh mukayi, amman Momy duk maiyasa hannu cikin wando wata ko riga ai yar iska ce ko."? Basma tayi ma Momy tambayar cewa Momy tayi...."Eh Basma yar iska ce, ai shiyasa nace maku karda ku yarda ko kuna so ace maku yan iska."?...da sauri muka ce..."Aa bamu so."cikin murmushi ta cigaba da cewa..."sannan idan aka yi maku wanki ku tsaya kayan ku su bushe sanann ku kwashe ku linke abunku... "to Momy."
muka amsata sake cewa tayi.
"Sai kuma ku ringa yin sallah kan lokaci da sa dan kwali, karku sake ku zauna ba dan kwali, ko kuna so aljanu su shigeku."?...."Aa mudai bamu so.."Sannan ku ringa yawo da hijab, karku kuskura ku fito ba hijab"to Momy..
"Sai kuma kuyi karatu sosai, duk wanda tayi na daya Baffanku yace shi kadai ya san abunda zai bata, dan haka sai ku dage kuyi karatu karku sake ku chanza position dinku na primary kunji."?
"Eh Momy, nan dai Momy ta kama yi mana wa'azi sai da ta gama yi mana sannan ta barmu muka kwanta dan gobe da safe za'a kaimu school..

Washe gari tun da safe aka shirya mana  komai da komai, harda abinci da miya aka akayi mana sannan muka shiga mota muka dauki hanya G. G. S. S. S. Sandamu...
Government Girls Science Secondary school Sandamu, makaranta yan mata ce take karamar hukumar Sandamu Daura local government Katsina State..
Bayan mun shigo cikin makaranta, motarmu tayi parking a bakin gate, nan Baffah yasa aka shigo mana da kayan mu cikin makarantar, nan muka shiga cikin addmintrastion block.
Nan muka shiga office din vice-principal Salisu Nuhu, nan Baffah ya shiga damu ciki office din, aka fara yi mana registration bayan angama Baffah ya nemi alfarma abarmu a class daya, haka akayi mu duka aka kaimu JSS1C, sannan aka kaimu hostel RED HOUSE, bayan angama yi mana komai Baffah ya dauko kudi dubu goma ya ba vice yace "gasunan in kuna bukatar wani abu sai kuyi  mashi magana."
Nan dai aka gama komai sannan muka ɗauki school bags dinmu aka rakamu class din mu...

Bayan an kaimu class,  muka shiga class muka samu second row first sit muka zauna ba tare da mun tambayi ko da mai waje ba... Bayan mun zauna sai ga wata ta shigo class da alamu fitsari tayo, amman tana dawowa taga mutane cikin sit dinta, cewa tayi....."Lafiya Malamai bangane ba?"tace mana cikin fada, nima ce mata nayi."Ko? cikin sigar raini, sannan na cigaba da cewa....."Karki damu zaki gane nan gaba kadan."
Na cigaba da hidimar gabana cigaba da cewa tayi....."To wallahi baku isa ba, sai kun fitarma a sit, tunda na rigaku zuwa.."
Kallonta nayi nace mata"Dan kin rigamu zuwa shine akace ke daya zaki zauna cikin sit din? sai kace daga gidan ubanki kika zo dashi." na ida maganar ina mata kallon banda lokacin mai lokacin ki...."karka manta Salim daman nace maka ni mafadaciya ce, to sai akayi sa'a na hadu da dai-dai ni dan  itama ceman tayi cikin fushi da masifa dan ga dukan alamu itama ba daga baya ba wajen fada..... "Gidan ubana?  ke har kin isa daga zuwanki ki nemi ki zagar mani uba? ke kin san ni wacece a class din nan."?
Kallonta nayi na watsar sannan nace.......

*Muje zuwa..... 🖤*

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Pls

BANSAN INDA SUKE BA A HALIN YANZUNWhere stories live. Discover now