BAKAR FURA EPISODE 31- 32

320 35 5
                                    

*🕳️BA'KAR FURA🕳️*
    _A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_

   PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

                    episode 30- 31

   Dagowa yayi cike da kwarin guiwa yace Baffah matar aure ce ita, wannan yariyar tana da aurenta, matar abokinace daga Cameroon suke, ita da Mijinta, tafiya ce takamashi zuwa garin dabesan Ina zai sauka ba, gshi anan din ma batasan kowa ba, asalima bata hausa, shine ya nemi da in kawota gidan mu ta zauna nawani lokaci kafin ya dawo, cikin baccin rai ya sake cewa inda nemanta nake ai bazan kawota gidanmu ba, Kuma cikin kannaina Baffah, nadauka cewar Ina da damar da zankawo wadda naso.

    Ajiyan zuciya Baffah yayi, cike da gamsuwa yace, " nafahimta Haydar, kana da damar shigo da duk wadda kaso kuwa domin gidan mahaifin kane, saidai inaga ba laifi bane  dan naga kamar zaka karkace natuhume ka, Kuma bayani yana da dadi, dole ne hankalina ya tashi ace yau na samu labarin ka sauki mace bana miji ba, batare da wani bayani ba, ya dace ace da abokin ka ya kawo matarsa ka kawoshi mugaisa, sannan ka sanar Mana cewa zaibar matarsa anan, kamar yadda kai bayani yanzun, dan haka nan gaba ka gyara wannan kuskure ne.

        Kansa akasa ya amsa da toh yayin da Baffah yace wane sunan yariyar??

      Muryan Aliyu adakushe yace, " Sunanta Humaira"

        Allah sarki, toh Allah ya dawo da mijin nata lafiya.

        Dakai ya amsa sannan ya mike yayi sallama ya wuce Office.

                     Ajiyan zuciya yaketa saukewa ajijjere, wani na korar wani, yayin da yake bakin cikin turkeshin da Baffah yayi tabbas yasan Momy ce ta zogoshi dan haka yaji abun nakara bata masa rai, kenan dan iska suka maidani, irin wannan tunanin yaita yi yayin da yakejin ransa na dada baci.

      
                       *******

     Aisha zaune kusa da Islam, waige kawai Aysha take yau bataga Aliyu ba, hankalinta ne ya fara tashi sai raba ido take, tun safe take sarai da ganin sa, gashi yanzun har sha daya, cikin ranta ta fara tunanin gida Mama Umma acen bangaren Kuma ga Daddy ta duk tabarosu ta tahonan da kudin data dade tana tarawa gashi yanzun har yanzun bataga Aliyu ba, wata zuciyar ce tace mata yanzun idan  be dawo ba fah Yaya zakiyi, ki koma gida?, hawaye taji ya zubo mata sharrr, Hannu tasa ta share sannan tace duk acikin ranta, idan kin samu kudin motar Ina zakibi kihau motar? kinsan hanyar tashan ? Me zakicewa masu mutar?, yin wannan tunanin hawaye ya fara ziraro mata babu kaukautawa, Meenat ce ta kula tabajin kukanta kasa kasa waigawa tayi ta kalleta cikin mamaki tace da Islam kuka take🤔

      Juyowa Islam tayi ta kalleta tare da tafata tana fadin kiyi hakuri baiwar Allah.

   Meenat kuwa fadi take menene?

      Islam ce tace ai kinsan baji take ba French Zaki mata.

           Akace miki wani iyawa nayi?, ni bansan yadda zan lallasheta ba.

        Islam ce ta saki bayan ta koma bakin gado ta zauna tana fadin, mudai mun shiga uku, ya hadamu da aiki ya wuce aiki abun sa, ni wlh abun nan haushi yake bani, ace kaita mgn da mutum besan me kake cewa ba.

         Ayaha ko shashekar kuka take taree da Kiran sunan Aliyu, sunan kawai suke iya fahimta.

   Meenat ce tace niman ya Haydar fa take bakijin tana cewa Aliyu ba, Islam kice mata yaje aiki anjima zai dawo.

       Cike da fada Islam tace ke meya hana kice mata, gaki kusa da ita.

       Ai bajina take ba, Meenat ta bata amsa.

BAKAR FURAWhere stories live. Discover now