*🕳️BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_*Na*
_Fadeela Lamido_PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
https://youtu.be/ebcYnNjGbOI
episode 32- 33
Ganin yayi sama da ita fara fadin, " Ya Aliyu sauke ni wasane nake maka.Cikin falon ya nufa da ita yana cikuikuye da hijjabinta, Aysha ko dariya take cikin wuntsula kafarta take rokon sa ya sauke ta tare da magiya.
Bisa kujere dake falon ya sauketa, sannan ya zame yasa guiyoyin sa akasa har yanzun yana rike da ita, hadiye murmushim sa yayi kina nufin har yanzun din dai abakin nake?
A'a Ya Aliyu yanzun kam kadan washe.
Nadan washe?, Aliyu ya tambaya yana tsare Aisha da idon sa.
Eh Mana ka Kara haske kadan.
Jimmmmm, yayi zuwa cen ya lumshe ido lokaci daya ya bude su tare da fadin, " toh naji ni baki ne, ahaka Kuma aka kanni ake Sona.
Murmushi Aysha tayi waye keson naka?
Mikewa yayi ya zauna daf da ita yana fadin wadda ya tsargu.
Hannunta ta mika ahankali ta Kara da hannun sa yayin da yai saurin janye nashi, dariya Aysha tayi Yaya nifa wasa nake maka fari ne Kai tasss.
Bawani, kinsan me??
A'a
Tsoro nake karmuyi aure mu dinga haihuwar bakaken yara.
Dariya Aysha ta Kuma sawa, yayin da Aliyu ya daure kamar ba shine yai mgnr ba, cikin kallon idon sa tace toh meye?, Yaya Aliyu kaifa ba baki bane, Kaine kake bani dariya da nafahimci baka son ace maka baki, bakin ka me kyau ne, kana da fari hasken fatane baka dashi Kuma kamafi kyau ahakan.
Lumshe ido yayi na kaiki?
Kama fini Yaya fa.
Haba?
Allah.
Ninasan duk wayoni kike min, nasan ke zarah ce acikin taurari, kina da kyau Aysha, tun kina karamar ki, yanzun ko da kika girma kin Kara kyau sosai, ni yanzun ma burina in ga na mallake ki, Aisha tunda naganki akaro na biyun nan naji na matsu inyi aure, kallon cikin idonta yayi sannan yace, ko kema kinajin irin wannan abun?
Cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa nidai kawai nasan namatsu ingan ka Kuma dana ganka naji dadi.
Ki ganni kawai shikenan?, Auren fah?
Cikin kukan shagwaba ta juya baya tare da fadin, " ni kabar wannan mgnr"
Shiru yayi idon sa akan nata tsayon lokaci sannan yace, " kina nufin baki damu da auren ba koko dai kinajin kunyata ne?
Yaya ni abar wannan mgnr.
Baza abarta ba, sai nayi, baki son muyi aure?
Ni intani a zauna ahaka.
Bangane azauna ahaka ba?, gaya min me kike nufi?, baki son aure?
Ni Yaya kabar mgnr nan muyi hirak kawai.
Ke!!, Karki Raina min hankali, an gama hiran sure nake so ni.
Toh ya Aliyu ai auren lokaci ne.

YOU ARE READING
BAKAR FURA
Romance✍🏻✍🏻BAKAR FURA lbr ne da yafaru da gaske, wanda yake dauke da Soyayya me kayatarwa, ga tarin Nishadi, ban al'ajabi tare da ban tausayi, gameda fadakarwa, wadan da abun ya faru dasu muna nan muna cigaba da rayuwa tare dasu cikin wannan duniyar tamu...