Chapter Eight

874 149 65
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

Zaune suke a conference room wuraren qarfe hudu da rabi na yamma.

Paapa, Hafeez, Hanifa da Unit heads na Comapny din..

Sadiq ne ya shigo yana fadin "sorry for keeping you waiting.. Clients din namu ne sai ahankali"

Hanifa wadda take zaune kusa da Paapa ce da danna mishi harara yayinda sauran heads din suke fadin "it's okay Sir"

Paapa ya nuna mishi kujera wadda take opposite ta Hanifa yace "ai ni na so kawai ayi forfeiting deal din tunda na ga murdaddun mutane ne.. were you able to convince them in the end???"

"Yes Sir.."

"Well done Son.."

"Thank you Sir" ya fada tare da zama kan kujera

Gyaran murya Paapa yayi sannan ya kalli Hanifa yace "toh Baby, tell us why you called for this emergency meeting"

Cike da mamaki na ga Sadiq ya kalli Paapa sannan ya kalli Hanifa wadda itama shi take kallo..

Wai dama ita ta kira meeting din? for what??

Hanifa wadda ta miqe tsaye ce tace "dama ina so in fadi muku cewar Sadiq is not who you all think he is.."

Gaba daya aka ce "what??"

Paapa wanda yake kallon Hanifa cike da mamaki yace "Baby me kike fadi haka??"

Gani nayi Sadiq yana ta shafa kanshi da hannuwan shi biyu non-stop.. da alama baya son inda zancen Hanifa yake zuwa.. He knows cewar whatever it is, it has to do with receipt na Bristol da ta gani a ofis dinshi dazu.

hmmmm...

"Yes Paapa.. Sadiq sata yake yi maka a kamfanin nan"

Tun kafin ta rufe baki kowa ya cika da mamaki yayinda na ji wasu suna fadin "subhanalillah" wasu kuma suna fadin "what??" yayinda saura suke ta qus-qus...

Sadiq dai a wannan karon duqar da kan shi kawai yayi cike da haushi da takaicin abinda Hanifa ta fada..

A ran shi kuwa fadi yake yi "this garl must be very stupid"

Paapa wanda shima ranshi yake a bace ne yace "Ke Hanifa lafiyar ki kuwa??? akan wane dalili zaki tara mu ki ci ma Sadiq fuska?? how can you accuse him of stealing?? shin kin san ko waye Sadiq kuwa??"

"ofcourse na sani Paapa, Abubakar Sadiq Bunza is a thief" ta fiddo copies da tayi na receipt din Bristol ta miqa ma Paapa sannan ta miqa ma Head of Marketting wanda yake zaune a gefen ta shima ya gani sannan yayi passing round.

"Sadiq ya saci kudi har N16.9m daga kamfanin nan ya biya kudin accomodation a Bristol Palace Hotel.. Shin salary dinshi har ya kai ya mallaki irin wannan kudaden?? what is he doing in a luxurious hotel anyway??? aaaah, No wonder ya karbi position din Finance Manager ya hana komai motsi.. sai da authorisation dinshi za'a iya fitar da kudi meanwhile yana kwasan kudi yana kashewa ba tare da an sani ba plus....."

"Shut up Hanifa..." Paapa ya dakatar da ita cikin fada yayinda na ga ta kalle shi cike da tsananin mamaki.

"Kina da hankali zaki zo cikin mutane kiyi ma Sadiq cin mutunci irin wannan?? dama kin fara aiki a kamfanin nan saboda ki sa mishi ido ne? da kika gano all these me ya hana ki zuwa wurina direct ki gaya mun?? do you have to come here and defame him??"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now